Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 35   Nuwamba 2002
SABUWAR FUSKA


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
FADI SONKA
Wasiku
NEMAN MAFITA
DUNIYAR FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
FADI SONKAr sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da tunanin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: Wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, ta da jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Grace Titus, matar Gagarabadau
Tana so mata 'yan fim su kame kansu, su kuma furodusoshi su rage kwadayi

Daga WAKILINMU a Kaduna

WADANDA suka kalli fim din Gagarabadau ba za su rasa lura da wata yarinya da ta fito a matsayin matar Gagarabadau din ba, wato da sunan Amina. Idan kun tuna, ita ce matar da Gagarabadau (Aliyu Abdullahi Gora II) yake matukar so, amma ya ki ya gaya mata sana'arsa; kullum sai dai ya kawo mata kyauta mai tsada, bayan kuwa babu wanda ya san inda yake samo kudin. Lokacin da 'yansanda suka ritsa da Gagarabadau a gidansa har suka yi harbe-harbe sa'ilin da ya nemi ya tsere shi da matarsa, 'yansandan sun kashe Amina a daidai lokacin da take kan tsani za ta haura kan katanga. Sakamakon haka ne Gagarabadau ya sha alwashin yin ramuwar gayya a kan dukkan 'yansanda.

To, Amina dai ba wata ba ce illa Grace Titus, wadda take aiki a shagon sayar da kaset na furodusa Yakubu Lere, wato 'Lerawa Films,' da ke Badarawa, Kaduna. Grace 'yar kabilar Ibo ce, haifaffiyar layin 'Kinkino Close' cikin garin Kaduna.

An haife ta a ranar 10 ga Oktoba, 1977. Ta yi karatun firamare a 'L.E.A. Malali,' Kaduna. Ta fara karatun sakandare a GDSS Barnawa, amma ta karasa a GDSS Tafawa-Balewa duk cikin Kaduna.

Ana iya cewa Grace kadai ce Inyamira a fagen shirin fim na Kaduna. Ya aka yi haka ta faru? "To, ba abin da zan iya cewa," inji ta, amma ta kara da cewa, "Ikon Allah ne kawai da kuma zama cikin Hausawa. Da ma an ce zama da madaukin kanwa shi ke sa farin kai." Mai karatu, kada ka yi mamaki don ka ji Grace tana watso karin magana, domin kuwa Grace 'Bahaushiyar-Inyamira ce.' Duk wanda ya gan ta, idan ba gaya masa aka yi ba da wuya ya ce ita ba Bahaushiya ba ce. Zama da madaukin kanwa ya sa mata farin kai kenan.

A cewarta, ta shigo harkar fim ne saboda sha'awa kawai. "Domin a duk lokacin da na zauna ina kallon finafinan Hausa sai abin ya dinga burge ni. Ba ma kamar lokacin da Fati Mohammed take tashe. Daga nan kawai na yanke shawarar tsunduma cikin harkar fim."

Grace ta lura da cewa akwai bambance-bambance tsakanin al'adun Hausawa da na Ibo, to amma ta ce na Hausawa suna burge ta kuma tana jin dadinsu. A cewarta ma, za ta iya auren Bahaushe, ko da kuwa dan fim ne. Hausawa, a ganinta, "suna son zama da mutane. Shi ya sa nake son rayuwarsu. Ba su kyamar mutane." To, ina masu son su taya?

Duk da yake ga ta tsundum a tsakanin masu shirya finafinai, musamman da yake kamfaninsu na Lerawa ma ya shirya finafinai, Grace ba ta fito a finafinai da yawa ba. Daga Gagarabadau, sai Adali 2, Kaddara, Arziki, da kuma Ibro Soja. "Amma na fi son Gagarabadau; ya fi kwanta mani a rai daga cikin finafinaina," inji ta. A kan dalilin da ya sa su 'yan fim mata na Kaduna ba su cika yin tashe kamar takwarorinsu na Kano ba, 'yar wasan ta ce, "Gaskiya wani lokaci furodusoshin ne da yawa ba su da kawaici game da mata, mu kuma da ma 'yan matan Kaduna da yawa muna da aikin yi, ba da fim muka dogara ba ballantana mutum ya ce dole sai ya yi abin da furodusa ke so ko da ba mai kyau ba ne don kawai a sa shi a fim." Idan ba ka gane ba, a nan kwai ne fa Grace ta fasa. Tana nufin cewa yawancin furodusoshi suna neman matan da suke sanyawa a fim ne, amma idan yarinya tana da sana'ar yi ba za ta bari tilas sai an neme ta kafin a sa ta a fim ba.

Daga cikin finafinan da Grace ta fito cikinsu, Grace ta fi shan wahala a Gagarabadau. "Domin akwai wani sin da muka yi, kafin a samu abin da ake so na sha wuya. Sai ga shi kuma duk a cikin abin da na yi a fim din na fi son wannan wurin - wato inda 'yansanda suka harbo ni da bindiga na fado matacciya."

Grace ta yi aiki da daraktoci kamar haka: Ishaq Sidi Ishaq (Adali), Hafizu Bello (Gagarabadau) da Saminu Mohammed Mahmud (Arziki). A cikinsu, ta fi jin dadin aiki da Ishaq "saboda ko kuskure ka yi a lokacin shirin fim ba ya fushi; cikin kwanciyar hankali zai nuna maka yadda za ka yi."

Mujallar Fim ta tambayi Grace ta ba takwarorinta 'yan wasa mata shawara. Sai ta amsa: "Shawarar da zan ba su ita ce, don Allah su rika kama kansu, musamman a yayin da ake daukar shirin fim. Da yawa wasu marasa kunya ke zubar mana da mutunci. Allah ya sa su gyara halayensu. Kuma ina ba furodusoshi shawara cewa su guji sanya yarinya a fim ba tare da sun bincike ta ba, sun kuma samu izini daga iyayenta."

To, Allah ya sa sun ji.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin