MUSA Alhassan, wanda aka fi sani da Kalla, yana daya daga cikin tsofaffin 'yan wasan kwaikwayo a Kaduna, musamman wasan dabe da kuma talbijin, ya yi fice kwarai a bangaren dirama a garin na Gwamna, musamman lokacin da shirin Sawun Keke ke tashe a talbijin. A harkar fim da ake ciki kuma, ya fi yin fice ne a fim din nan mai suna Gagarabadau, inda ya fito a matsayin karen motar Moda. Haka kuma ya fito da sunan Tukur Sabalikita a cikin shirin Daren Farko. Dukkan wadannan finafinai, kamfanin 'Northern Star Films' da ke Kaduna, mallakar wannan mujallar, shi ne ya shirya su.
Dan shekara 31 da haihuwa, an haife shi a garin Kubaraci da ke cikin Karamar Hukumar Madobi a Jihar Kano. Ya yi karatun firamare dinsa a 'L.E.A. Badarawa,' ya kuma yi na sakandare a G.S.S. Kurmin Mashi, Kaduna, bayan nan kuma ya karanta kwas a fannin 'Land and Survey' har ya samu satifiket.
Shin bayan Kalla ya kammala karatun akwai wani aiki da ya kama kafin ya tsunduma cikin harkar wasan kwaikwayo? Sai ya amsa, "Gaskiya tsakani da Allah ba wani aiki da na fara yi. Da ma ina dan yin wasan dabe tun daga makaranta. To da na gama karatuna sai na fada wata kungiyar wasan kwaikwayo mai suna 'Haske Dramatic Club' da ke Unguwar Dosa, Kaduna. Ina cikin wannan kungiya ne, wata rana sai K.S.T.V. suka nemi mu zo mu rika yi masu wani wasa mai taken 'Mai Dokar Barci'. To shugaban kungiyar furodusoshin Jihar Kaduna na yanzu, Alh. Ashiru Sani Bazanga, da ya ga wasanmu, sai ya zo shi ma ya dauke mu ya ce yana so mu rika yi masu wasan kwaikwayo shi ma. Ka ji ta yadda na fara shiga talbijin."
Duk da kasancewar Kalla tsohon dan wasa ne, amma yawancin 'yan kallo, musamman wadanda ke wajen Kaduna ba su san shi ba, saboda rashin ganinsa a wasannin bidiyo. Za mu iya danganta wannan da rashin samun dama daga furodusoshi, amma kwanan nan, duk mai kallon finafinan Hausa zai iya nuna maka Kalla ko a cikin dubu, musamman saboda fitowarsa a wasu manyan finafinan 2002. A gaskiya, kwarewarsa ta jawo masa ci-gaba a fagen shirin fim, sai ma abin da ya yi gaba.
To abin tambaya a nan shi ne, a wane fim din ya fara fitowa? Sai ya ce, " A lokacin da ake yayin finafinan Hausa, ban san kowa ba a industiri, sai kwatsam wani abokina mai suna Habibu Soja, wanda a yanzu haka shi ma furodusa ne, ya gayyace ni zuwa inda ake daukar shirin wani fim mai suna Daula. A wannan rana ce na fara sanin Ishaq Sidi Ishaq. Aka sanya ni a wannan fim kuma na yi. Wannan shi ne fim na farko da na fara yi."
Ya zuwa yanzu Kalla ya yi finafinai da dama. Da wakilinmu ya tuntube shi a kan haka, Kalla cewa ya yi "E, to ba shakka na yi finafinai da dama, amma ba duka zan iya tunowa ba. Farko dai akwai fim din Daula, Kaddara, Jini Daya, C.I.D, Illah, Abdulmalik, Ibro Soja, Arziki, Maina, Gagarabadu, Daren Farko da kuma Zuri'a."
Da muka nemi jin ta bakinsa game da fim din da ya fi kwanta masa a rai, musamman saboda irin rawar da ya taka a fim din, sai ya kada baki ya ce, " To a gaskiya fisabilillahi, wallahi ba kamar Daren Farko, gaskiya. Saboda shi labarin fim din ya sha bamban da sauran finafinan da na yi. Sannan kuma rawar da na taka a fim din, ni kaina na ba kaina mamaki, domin ba a taba ba ni dama irin wannan ba. Haduwata kuma da manyan 'yan wasa kamar su Iyan-Tama, Ahmed S. Nuhu, Maryam Mashahama, Ashiru Bazanga, da dai sauransu, ya kara mani kwarin gwiwa. Daga gare shi kuma sai Gagarabadau wanda daga gare shi ne 'yan kallo suka fara gane ni."
Ra'ayin dan wasan game da wasan kwaikwayo shi ne "Ni kam game da wasan kwaikwayo sai baba-ta-gani."
Dan wasan yana da mata daya da 'ya'ya uku duk mata. Bugu da kari, a yanzu shi ma'aikaci ne a kamfanin mujallar Fim.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin