Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 39   Maris 2003
GASKIYA DAYA CE
TARE DA DAN'AZUMI BABA CHEDIYAR 'YANGURASA


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
FADI SONKA
Wasiku
NEMAN MAFITA
DUNIYAR FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
FADI SONKAr sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da tunanin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: Wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, ta da jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Lokacin magana ya zo

A CIKIN 'yan watannin nan an sha yi min wata tambaya wadda na dade ban ba da amsarta ba. Tambayar ita ce: Dan'azimi Baba, shin me ya sa ba ka son fitowa cikin mujallu ka yi magana kamar yadda takwarorinka suke yi? Gaskiya ne, duk wanda ya yi mani wannan tambaya hakika na amince da cewa lallai shi mai lura ne da abin dake kaiwa da komowa a wannan kwarya tamu ta harkar fim, kuma na gode da jin haka.

Wato hakika a da ba ni da wannan buri, kuma ba ya cikin tsarina, in yi magana a bayyane kan harkar fim. Kuma ba don komai ba, sai don hangen yadda harkokin shirya finafinai suke tafiya cikin rashin tsari gare mu baki daya. Domin a yau idan ka kula da yadda harkar shirya finafinan Hausa take tafiya, za ka ga kullum tsalle ake yi a guri daya a dire a guri daya, an rasa wani bangare da zai kawo canji. To bisa wannan dalili ne ya sa nake ganin yin magana a gurbin da ba za ta yi amfani ba bata lokaci ne kawai. Domin idan ka kula da kyau za ka ga tun zubin da muka yi wa harkar fim din Hausa ita ce dai babu canji walau a shirya fim din ko sayar da shi ko yanayin aikin ko labarin. Saboda mafiya yawan jama'ar da suka shigo harkar fim daga bayanmu, ba burinsu ne su bunkasa harkar ba, sun shigo ta ne da sigogi iri daban-daban: wasu don neman kudi, wasu don neman suna su sami damar cutar jama'a, wasu kuma sun shigo ne kawai don gurbata harkar ta hanyar lalata saboda ganin harkar ta cudanya ce maza da mata.

Sannan harkar ta zama babu babba ba yaro, sai abin da kowa ya ga dama yake yi saboda takamar wani abu da bai dace a ce wannan ya zama madogara ba. Abin kuwa shi ne: A yau komai dadewarka a cikin wannan sana'a idan ba kudi gare ka ko ka yi wani fim ya yi tashe ko ba ka da kunya ba, to ba ka isa ka ce a saurare ka ba komai tsufanka a ciki. Kuma kowane irin ci-gaba ka kawo mata a baya idan harkar ta dan juya maka baya babu mai sauraronka sai kalilan daga ciki.

Sannan gaba dayammu ba mu san idan dan'uwanmu ya yi fim karayar arziki ta zo masa a dalilin wannan fim mu tausaya masa ba, sai ya zama kuma saniyar ware-duk inda aka zauna idan ya shige sai a dingi yi da shi. Irin yin hakan hauka ne kawai, domin kowa bai san yadda za ta kasance masa ba, tunda yana cikin harkar. Da ma kuma haka ita ce babbar annobar sana'ar shirya fim a ko'ina a duniya: sai ka gama shirya fim dinka, kai kana ganin ka yi matukar kokari sai ya fito kasuwa ta ki karbarsa. To madadin a taimaka maka, a'a, burin wadansu ya cika; sun ga bayanka a cikin harkar; sai kuma a sa wa wani ido.

Ba zan manta ba, irin makamanciyar haka ce ta sa ni na ci gaba da zazzage wa abokan sana'armu dimbin basirorin da Allah ya ba ni ta hanyar rubuta masu labarai da aiwatar masu da shi a aikace. Wato ina nufin dillalanmu 'yan kasuwa irin su Nasiru Haruna Dararrafe da Ibrahim Hassan Adamu da A. Musa na Malam Kato da Idris Danzariya da Lauwali Dansokoto da Isma'ila I.U.I. da Danlami. Domin lokacin da na yi finafinaina Kyan Alkawari da Kwai A Baka na sami matsala ta rashin tafiyarsu a kasuwa, su 'yan kasuwar nan ne suka hada kai ban sani ba suka dinga yi mini alhairi na kudi ba kadan ba har na shige wannan karni ba tare da wani dan'uwana shugaban shiri ya sani ba. Domin sau da yawa idan na je karbar dubu uku kudin kwalin fim dina, sai na ga kwalin ba su sayar ba, amma da na juya zan tafi sai wani ya kira ni a cikinsu ya yi mini kyautar dubu biyu ko daya! To gaskiya faruwar irin wadannan abubuwa ne ya sa na ja bakina na yi shiru na daina nuna kaina, sai dai shawarwari kawai na cikin gida wadanda idan kungiyata ta 'Kano Filmmakers' ta kira ni na ba ta. To wadannan dalilai su ne suka sa aka ga ba na cewa komai a kafofin yada labarai, domin ni dai duk abin da zan ce ba zan yi son rai ba, gaskiya zan fada.

Amma ina kira baki dayan duk wani bangare da ya shafi harkar fim, na gwamnati da na wadanda ba gwamnati ba, ya zama dole mu hada kanmu don neman albarkar da ke cikin wannan sana'a tamu ta shirya fim. Mu zama uwa daya uba daya, mu gudu tare mu tsira tare. Duk abin da ya shafi mai shirya fim ya shafi mai sayarwa. Duk abin da ya shafi mai sayarwa ya shafi mai shiryawa, ya shafi hukumar da muke karkashinsu, tunda raguwarmu raguwarsu ce, samunmu shi ne nasu.

Abu na biyu kuma shi ne, rashin samun wata karbabbiyar kafar yada labaran harkar finafinai mai inganci da kowa da kowa zai yi na'am da ita. Wato kamar mujallun da muke da su, za a ga babu wata kyakkyawar fahimtar juna da za a hadu mu da su don gina wani abu mai kwari a cikin labaran wanda za ta zama abar farin ciki ga kowa da kowa. Amma ga bisa dukkan alamu ina ganin yanzu mun sami zakaran gwajin dafi gurin isar da sakonni a ko'ina cikin Nijeriya da sauran kasashe makwafta baki daya, ko in ce ko'ina a fadin duniya; ita ce jagorar mujallun Hausa, wato mujallar Fim. Idan Allah ya so za a dinga jina da ganina a cikinta a kai a kai. Ina fatan ni da ku za mu karu da abin da zan rika bayyanawa a wannan shafin nawa, amin. Na gode.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin