A Dinga Sara Ana Duban Bakin GatariDOLE rayuwa sai an yi hakuri da kaddara mai kyawu da maras kyawu, sannan za a samu lafiya, domin hassada da kushe ba sa haifar da alheri ga masu yi. Haka kuma wulakanci da tunanin dauwama kan wani tafarki shi ma ba abu ne da ya kamata mutum ya dauka ya dora a kansa ba, ba don komai ba sai don rauni da dan'adam yake da shi, na cewar idan kai ne yau, to gobe fa dole ta kasance waninka ne ba kai din ba.
Duk da yake mun san harkar shirin fim gasa ce, amma ya dace a dinga sara ana duban bakin gatari don gudun cabewarta. Kira tare da tsokaci nake yi game da irin halin da muka tsinci kanmu a wannan lokaci na canjin yanayi na sana'armu ta finafinan Hausa. Dole a hada da hakuri a cikinta.
Jama'a da dama suna yawan kuka da surutai kan wulakancin da wadansu jarumai da kamfanoni suke yi don sun samu dama da daukaka. To a nan ina so na ja hankali tare da ba da shawara ta hanyar tuno da baya. Duk da cewa masu Karin magana sun ce "kowa ya tuna bara, to bai ji dadin bana ba," amma ni na san wani tuna-bayan bai zama lallai a ce rashin jin dadin bana ne ke kawo shi ba. Dalili kuwa, mutum ya wahala a shekarun baya shekarun gaba za su zo masa da kyawu sosai. To ashe don ya tuna baya, ba wahala ce ta sa shi ba. Amma dai duk da haka dan'adam ajizi ne, duk lokacin da yake cikin dadi ba kasafai yake baza tunaninsa ba. Amma da zarar ya fuskanci wata 'yar matsala yanzu zai kara, tare da kawo abubuwa iri-iri a cikin zuciyarsa da zarge-zarge.
Ni a nawa hangen bai dace ga mutumin da Allah ya bai wa wata daukaka ya zama mai wulakanci ba. Domin yau da gobe sai Allah. Daukakar nan dai Allah ne mai dora ta a kan bayinsa, lokacin kuma da ya so dauke ta daga kan wanda ya dora ba sai ya shawarci wani ba. Domin an yi haka ya fi sau shurin masaki. Kai da kake ganin wani ne ko kike ganin wata ce, mutum yana ji yana gani ya zama dan kallo, rayuwar ba ta yi da shi. To ka ga a nan babu babban mai cin ribar rayuwa illa mutumin da ya samu daukaka ya zauna da jama'a lafiya. Domin ko babu komai ranar da rayuwa ta juya maka baya, wadanda ka kyautata wa ta hanyar zaman lafiya za ka mutunta, sabanin ka zama mai dagawa da cin zarafin jama'a yayin da ka sami wata 'yar dama da ba kai ne ka bai wa kanka ba.
Idan muka yi dan nazari kan yadda wannan sana'a tamu ta faro, ai ba ma sai an ce da maci dambu ya sha ruwa ba. Da a baya, kafin mu kawo wannan lokacin, ai kamfanonin da ake magana da jarumansu wadanne ne? Iyan-Tama ne da Gidan Dabino da Sarauniya da Tumbin Giwa. A jarumai kuma Mandawari ne da Ado Ahmad da Hamisu Iyan-Tama da Adamu Kwabon Masoyi a maza; a mata kuma su Hindatu Bashir ne da Hawwa Ali Dodo da Fati 'Ki Yarda Da Ni' da A'isha Bashir. A mawaka maza kuma su Dandirimi Satatima ne da Sani Yusuf Ayagi da Sammani Sani Gwale da Hamisu Bature, yayin da a zabiyoyi su Rabi Mustapha ne da Bilkisu Abdullahi da Fati B. Mohammed Kofar Mata.
Don haka shawarar da zan bai wa wadanda Allah ya haskaka yanzu ake yi da su, su yi taka-tsantsan da halin da suka tsinci kansu don su rabu da kowa lafiya. Domin yadda da babu su wadansu ne, to su ma za a wayi gari wadansu ne ba su ba. Don haka idan an kawo wa mutum ziyara, ya karbi bakon hannu biyu-biyu har su rabu lafiya. Idan kuma bangaren cinikayya ne, a yi kokari a rabu da abokin ciniki salin-alin ba tare da rai ya baci ba, kowa na ganin darajar kowa.
Yanzu ga misali: ina Tijjani Ibraheem? Ina Aminu Hassan Yakasai? Ina Bashir Mudi Yakasai? Ina Yakubu Ibrahim? Ina Nasiru Ishak Gwale? Ina su Auwalu Marshal? Ina Balarabe Sango? Ina su Bala Anas? Ina su Mu'azzam Bos? Ina su Salisu Magashi? Ina su Adamu Kyaftin? Ina su Idi Cana? Ina su Kasko? Kai, ta babban mahaukaci - ina Dan'azimi Baba? Duk mun yi fedin, wadansu ma cikin wadannan da na lissafa sun mutu! Yanzu a irin na da din na daga baya-baya, ban da irin su Sani Danja babu wanda ya rage ake yi da shi sosai. A irin iyaye kuma idan ka dauke Husaini Sule Koki da Kabiru Nakwango da Kabiru Maikaba da Amina Garba, ina ragowar suke? Kuma yawancinsu suna nan da ransu, kuma suna yin harkar, amma kamar babu su!
Don haka ina kara kira ga wadanda yanzu harkar take yi da su, su kula da kyau, kada su yi mutuwar kwando, ko mutuwar yadin shadda.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin