ABOKAN nan na kut da kut, mawaki Yakubu Muhammad da jarumi Sani Musa Danja suna daga cikin tarin 'yan fim da suka tafi sauke farali a bana. Su biyun a jirgin yawo suka tafi, maimakon bin rububin alhazan Nijeriya, wanda hakan ya nuna cewa lallai rayuwa tana kai wa wadannan matasan a yanzu. Mamallakan na kamfanin shirya finafinai na 'Two Effects' da ke Tal'udu, Kano, suna daga cikin 'yan fim da kasuwarsu take da budi a yau, kuma suna da matukar farin jini a wurin jama'a. Tafiyarsu Makka ta tabbatar masu da cewaa suna da masoya ba a Nijeriya ba har ma a waje.
Da farko dai sai da suka yada zango na tsawon awa biyu a kasar Sudan kafin su suke cirawa sama sai Jidda.
An yi wata 'yar dirama da su a wurin bincikar kaya a filin jirgin sama na Jidda. Da jaka daya suka tafi mai dauke da kayansu su biyu. A cikin jakar akwai yaji, wasu finafinai da kuma mujallar Fim fitowa ta 26 wadda ta ba da labarin bikin bai wa makada da mawakan fim kyaututtukan da mujallar ta shirya. A wata hira da aka yi da Yakubu kwanan nan jim kadaan da dawowarsu daga aikin hajjin, mawakin ya kadabaki ya ce, "Ai da jami'an tsaro suka ga finafinan da yaji sai suka ce ai ba ta sabuwa, tilas sai sun gani kuma an yi masu binciken filla-filla." Ya kara da cewa, "Amma ko da muka nuna masu hotunanmu inda ake ba mu kyauta a cikin mujallar Fim muka ce masu mu 'yan wasan fim ne, sai suka yi ta cewa, 'Tamsiliyya! Tamsiliyya!', wato 'yan dirama! 'Yan dirama!" Shi kuma Sani Danja ya ce haka suka yi ta wasa da raha da su.
Da yake kaya iri daya suka sanya tamkar tagwaye, kamar yadda suka saba, an kara yin wata diramar da su a filin jirgin. Da ma Yakubu ne ya ba jami'an jakarsu. Amma da Sani ya riga shi fita sai ya karba. Shi kuma Yakubu da ya karaso sai ya ce, "Ku ba ni jakata." Naani jami'i ya ce tare da damuwa, "Ba ka karbi abinka ba!" Aka yi ta dariya.
Wadannan sababbin mahajjata tun farkon hirarmu da su sai da suka yi godiya ga dimbin masu kallon finafinan Hausa wadanda kuma suka je aikin hajji daga kasashe daban-daban, musamman Gambiya, Sudan, da Saliyo. Sau da dama, inji Sani, an yi ta kwala masa sunan 'Abba,' wato sunan da ya fito da shi a cikin Tsumagiya, shi kuma yana cewa, "Na'am!"
Wani abin sha'awa da alhazan suka fada kuma shi ne yadda Larabawa suka rika sha'awarsu ganin cewa sukan yi shiga iri daya. "Wannan ya sa har wasu Larabawa kan rugo da gudu su dauki hoto da mu." A Madina, wani wanda ya ce masu asalin iyayensa 'yan Nijeriya ne, ya kwaso matarsa da 'ya'yansa ya kaimasu ziyara. Haka ma a birnin Makka Hausawa sun karbe su hannu biyu-biyu.
A hirarsu da Fim kan tafiyarsu Saudiyya, Yakubuda Sani sun nuna rashin jin dadinsu kan rashin zuwan 'yan fim daurin auren abokiyar aikinsu Rabi Mustapha, wadda aka yi bikinta ba su nan. Suka ce ko ba komai dai ai an ci moriyar Rabi sosai, bai kamata a yi mata butulci ba.
Ana yada karairayi game da 'yan fim a Saudiyya
IBRAHIM Mu'azzam, mai kamfanin 'Zinariya Films' da ke Kano, kuma dan wasa, yana daga cikin 'yan harkar fim da suka sauke farali a bana. Shi dai Alhaji Ibrahim, ba boyayye ba ne wurin masu shirya fim,domin an lura cewa a yawancin tarurrukan da ake yi a harkar, shi ake gayyata ya zama mai gabatarwa (M.C.) saboda iya bakinsa da kuma sanayyar da ya yi wa mutanen da ke cikin sana'ar. Hasali ma dai shi ne ya yi gabatarwa lokacin bikin karrama fasihai wanda mujallar Fim ta shirya kwanan baya.
Wannan ne zuwansa Makka na farko. A tattaunawar da suka yi da wannan mujallar, Ibrahim Mu'azzam ya nuna godiya ga Allah da ya ba shi ikon zuwa. Ya ce, "Aikin Makka kira ne, ba kudi ba ne."
Mu'azzam ya ce duk da cewa bai dade yana fitowa cikin finafinai ba, ya ci karo da jama'a da yawa wadanda suka nuna masa sani kuma suka rika ina-naka-sa-ina-naka-aje da shi. Babban abin da ya fi ba shi mamaki shi ne irin labaran da ya rika ji game da 'yan fim a Saudiyya. "Wallahi, wani labarin sai ma ka rasa ta inda ya tashi daga Kano ya dira Saudiyya," inji shi. Wannan ne ya sa ya kara tabbatar da cewa babu labari mai yawo a duniya kamar na dan fim.
Ya yi bayani kan labaran da ya ji a can har ya ce ya zama kamar wani kundin bincike don neman ilimin 'yan fim. "Gaskiya na sha tambayoyi, kuma mafi yawan labaran da ake kai masu duk na karya ne. Shi ya sa nake yaba mujallar Fim don ko ba komai za ta raba gardama," inji shi.
Mu'azzam ya tuna da wata tawagar mutane shida a karkashin jagorancin wani mai suna Yusuf da suka same shi. Wadannan mutane sun nuna masa sha'awarsu ta shirya wani fim wanda ya jibinci shari'a. Shi ko ya ba su shawarari masu muhimmanci sosai.
Babbar wahala ko kuma matsalar da ya ce ya fuskanta a Saudiyya ita ce rashin wata hanyar isar da sako tare da abokan zamansa a can, wadanda akasarinsu mutane Rasha ne. "Ni da su muna sha'awarar hira amma ban iya Rashanci ba, su kuma ba su iya Turanci ba balle uwa-uba Hausa. Amma da na iya Rashanci, to da sai sun sha tambayar kwakkwafi!"
Shi dai Ibrahim bai dade da shirya wani fim ba mai suna Ja'iba.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin