Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 29   Mayu 2002
BUKUKUWA


BABBAN SHAFI
Mu Leka Mu Gani
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 1
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 2
Rayuwarmu
Mu Leka Hollywood
Malam Zurke
Mutanen Boye
Bukukuwa
Sauran Labarai
Ra'ayi Ba Gaba ne
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Akwai:
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


Musa Liman Jalingo tare da abokan ango

Musa Jalingo ya je gida ya darje
Daga ABDULKARIM AL-BASHIR, a Jalingo

JUMMA'A, 8 ga Maris, 2002, rana ce ta tarihi a garin Jalingo, hedikwatar Jihar Taraba. Ta zama ranar tarihi ne sabili da wasu muhimman abubuwa biyu da suka wakana a cikinta. Daya na farin ciki, kana dayan kuwa na bakin ciki ne.

A cikin daren wannan ranar ne dai wasu 'yan fashi da makami suka kai wani mummunan hari da ya yi sanadiyyar rasuwar wani hamshakin dan kasuwa da ke da manyan shaguna a babbar kasuwar Jalingo. Bayan sun kashe shi, sai suka yi awon gaba da wasu makudan kudade da ba a san adadinsu ba.

Haka kuma a dai wannan ranar ce, dubban masoya finafinan Hausa daga sassa daban-daban na kasar nan suka cika garin don nuna kaunarsu ga shahararren furodusan fim din Izaya, Malam Musa Liman Jalingo, bisa aurensa da Malama Rashida Ahmad.

Mutane sun fara taruwa ne tun daga karfe 2 bayan an taso daga masallaci ana ta musabaha da raha da juna. Har ila yau taro ne da ya tara ya kuma kunshi tsofaffin abokai da aminai, musamman wadanda suka dade ba su ga juna ba, kuma tun kafin wannan lokaci waliyyin amaryar, Malam Mijinyawa, ya gama kimtsawa domin amsar waliyyan ango su Alhaji Lawal.

Ba da jimawa ba sai ga wasu motoci dauke da dattijai abokai da 'yan'uwa da iyayen ango wadanda suka zo don shaida daurin auren. Kafin ka ce kwabo sai ga wata tawagar ta masu saida kasa-kasan bidiyo, karkashin jagorancin Alhaji Rabi'u. Haka su ma 'yan kungiyar masu kallon finafinan Hausa ta jihar, karkashin shugabancin Malam Kawu, ba su bari an ba su labari ba.

Nan take kuma, ba tare da bata wani dogon lokacin ba, aka shiga gabatar da abin da ya tara jama'a. Tirkashi! Ana shiga raba goro da abin da ya sauwaka, sai aka ga kura ta tarnako, tana mai maraba da kuma albishir da isowar tawagar ango da abokansa, ciki kuwa har da wadanda suka nuna masa so da kauna, suka yi takakkiya daga Kano don halarta bikin.

Sun hada da Abdulkadir Muhammad Tarauni, Nasir Sabo da ake wa lakabi da 'Black', da fitaccen dan wasan nan Alhassan Kwalle (Bakin Wake), kana da fitacciyar jaruma Hajiya Rukkayya Umar Santa ('Dawayya').

Wasu ababen tarihi da za a dade ana sharhi a kansu sun faru a wannan biki, domin wasu manyan 'yan kasuwa da jami'an gwamnati da kuma wasu 'yan jarida, ciki har da mujallar Fim, ba a bar su a baya ba, don su ma sun sa albarka ga bikin, haka kuma an kayatar da taron daurin auren da dauke-dauken hotuna, inda kowa ke kokarin daukar hoto da ango da bakin Kanawan.

An daura auren da misalin karfe 2.30 na rana. Kowa na hamdala da sam-barka, kuma aka bayyana adadin sadakin da ango ya ba da na N10,000.

Ana shafa fatihar karshe, sai aka dunguma zuwa babban filin wasa na jihar da ake kira dandalin 'Afolahan' ko kuma 'Afolahan Square" domin bai wa idanu abinci na ganin gala da aka shirya.

To, a wajen wasan galar ne mutanen Taraba suka nuna takaici na rashin halartar furodusoshi ko wani wakilinsu, haka kuma duk cikin abokan sana'ar angon da kuma daraktoci ba wanda ya halarta sai Alasan Kwalle. Hakan ya harzuka wasu masu kallon su 'Bakin Wake' da Rukayya Dawayya suna ihu da jifa da cewa: "Furodusoshi sun ba mu kunya, sun nuna mana son kai!" da wasu kalaman da Fim ba za ta iya rubutawa ba. Kai, a takaice, da kyar jami'an tsaro suka samu suka fitar da wadannan shararrun 'yan wasan daga dandalin.

Kuma muna gab da fita dandalin wasan ne, sai wasu tawagar kungiyar masu kallon finafinan Hausa da kuma wasu masu sayar da kasa-kasai suka rItsa wakilin mujallar Fim domin ya isar da sakonsu ga furodusoshin Kano da daraktoci, cewa su mutanen Taraba an ba su kunya da mamaki na rashin ganin ko da furodusa ko darakta guda da ya zo bikin, suka yi barazanar cewa, "Za mu dau mataki, don kowa da ranarsa!"

Har ila yau sun yi mamakin rashin ganin babbabn aminin angon, wato darakta Ishaq Sidi Ishaq. Duk da cewa angon ya karyata zargin da ake yi na cewa a yanzu ba su tare, jama'a na ganin cewa "biri ya yi kama da mutum."

Wani abu da ya burge jama'a a taron galar shi ne yadda wasu gungun matasa suka shirya wani kwarya-kwaryan jerin-gwano na nuna kaunarsu ga jaruma Abida Mohammed duk kuwa da cewa ba ta halarci bikin ba. Matasan dai suna dauke da kwalaye da ke da wasu rubuce-rubuce kamar haka: "Abida ke muke so!" "Allah ya ja zamaninki Abida!" da sauransu. Haka kumaa ranar da suka iso ne wani mashayin giya da ya gama dauke-wuta, ya zo ya gwarawa motar abokin ango, Abdukadir Muhammad Tarauni, kirar Honda Prelude, amma cikin ikon Allah ba wanda ya ji rauni.

Da dare ya yi sai abokan arzuka suka yi jerin-gwano cikin motoci da kuma babura zuwa dauko amarya, Rashida Ahmad, wadda ba ta dade da kammala karamar sakandare ba. Kashegari ranar Asabar da yamma abokai da 'yan'uwa suka raka ango zuwa gida domin neman tubarrakin iyayensa kamar yadda yake a al'adar Fulani.

Lokacin da harkoki suka dan lafa, wakilinmu ya samu zantawa ango Musa Liman Jalingo. Ya ce, "Da farko ina gode wa Allah (SWT) da ya cika min burina da ya nuna min wannan rana da na auri Rashida, kuma ina gode wa duk wadanda suka nuna min kauna suka zo domin taya ni murna, na kusa da kuma wadanda suka zo daga nesa, kai, har da wadanda suke da niyya, amma Allah bai nufa ba. Allah ya saka da alheri, kuma Allah ya bar zumunci, amin."

Musa ya ki ya nuna wani takaici ko damuwa na rashin zuwan wasu abokan sana'arsa daga Kano, maimakon haka sai ya daga kai ya ce, "Allah ne bai nufa za su zo ba, domin na gayyace su kusan wata guda da ya wuce. Don haka ina bai wa jama'a hakuri." Dangane da batun da ake yi a Taraba na cewa akwai soyayya a tsakaninsa da 'yar wasa Aina'u Ade, Musa ya karyata zancen, ya ce mutunci ce kawai tsakaninsu.

Da Fim ta tambaye shi dalilinsa na auren Rashida, wadda take ba 'yar wasa ba, sai angon ya kada baki ya ce, "Ka san mu a al'adunmu ta Fulani, akasari mukan bi shawarar iyaye ne muddin bai saba wa addini ba, don kuma kiyaye tsari na dangantaka da mutunci. Kuma ai matar mutum kabarinsa, to komi nufi ne na Allah (SWT) kuma shi (Allah) ne ya nufa a gida zan yi aure. Kuma ina fatan alheri ga sauran 'yan wasa mata."

Su ma dai da suke tofa albarkacin bakinsu, iyayen ango kamar su Hajiya Salamatu, Hajiya A'isha, babarsa da kuma wadanda suka zo taya shi murna daga Kano, duk sun nuna godiyarsu ga Allah (T) da ya nufa za a yi wannan auren, kuma suka yi fatan alheri ga amarya da ango, kana suka yi masu nasiha dangane da zaman aure da hakuri da juna.

Ita ma 'Yafandonsa,' watau kanwar gyatumar ango cikin harshen Fulatanci, ta yi jawabi kamar haka: "Ina gode wa Allah (SWT) da ya nufe mu da taruwa airin wannan bigire don taya dan mu Musa murnar aurensa da 'yar mu Rashida. Bayan haka kuma a takaice ina mai yi mana nasiha gaba daya da mu ji tsoron Allah, mu tuna da manufar zuwanmu nan duniya na mu bauta wa Allah (T) kuma aure na daya daga cikin nau'o'i na ibada…" Kanwar babar tasa, kasancewarta malama kuma irin sufayen matan nan, ta yi nasiha dangane da rayuwa, zaman aure da kuma rayuwa gobe kiyama da ya ratsa zukatan jama'ar da ta taru a wannan bikin.

Ita ma dai Rashida Ahmad, wakilinmu bai kyale ta ba, don ya ji ta bakinta duk kuwa da irin abin nan da Fulani kan yi na 'Fulaku,' watau jin-kunya. Kyakkyawar amaryar, wadda da ganinta ka san cewa karama ce sosai, cikin kunya da tunani, ta mika godiyarta ga Allah da ya kaddamar da wannan biki nasu, kuma ta nuna farin cikinta ga duk wadanda suka zo bikin, da fatan kowa zai koma gidansa lafiya. Rashida, duk kuwa da cewa danya take, sai da ta dan nuna halinsu na mata. Da wakilinmu ya tsokane ta da batun ko za ta so a yi mata kishiya, habawa! nan take ta harzuka, ta ce, "Ina! Ba zai sabu ba. Ni da angona Musa mutu-ka-raba, kuma zan rufe kofa!" Nan take duk wadanda suke wajen hirar suka dauki shewa.

Shi dai Musa Liman Jalingo, furodusa ne da ya dade a Kano. Zuwa yanzu ya yi finafinai da dama da suka hada da Komi Nisan Jifa, Kowa Ya Ki Ji, Ruwan Zuma, Maci Fariya, Izaya, da kuma Tsaro. Ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba zai fitar da wani sabon fim kan tarihi da al'adun Fulani da ke dauke da soyayya.

An dai yi biki lafiya kuma an tashi lafiya. Tuni kuma amarya ta tare a gidan mijinta. Allah Ya ba da zaman lafiya, ciki da kuma goyo!

Allah ya sa, amin.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin