Abida ta auri rabin ranta Hamza
Abida da Hamza washegarin ranar da ta zama Jarumar Jarumai mata
|
YA zuwa lokacin da kuke karanta wannan shafin, an daura auren Abida Mohammed, fitacciyar ''yar wasa wadda ta ci lambar Jarumar Jarumai Mata ta 2001, da furodusan da ta dade tana soyayya da shi, wato Hamza Mohammed Danzaki. An daura auren a unguwar Fagge a Kano a safiyar ranar 2 ga Yuni, 2002.
Kwanaki kadan kafin a sa Abida a lalle, wakilinmu ya ci karo da ita a ofishin angon nata da ke 'Home Alone Production' a Sabon Titi. Sun zauna zaman jiran Hamza domin ta samu izinin yin hira da mujallar Fim, amma har dare ya yi nisa bai bayyana ba. (Da ma muna da masaniyar shi ma Hamza ya hana Abida yin hira da mujalla a kan batun auren). Lokacin da suke zaune masoyan amaryar sun yi ta zuwa suna taya ta murna, har wata mata ta aiko mata da sadakar Alkur'ani mai tsarki wanda Abidar ta karba cike da murna.
Kadan daga cikin shirye-shiryen da Abida ta yi tare da kawayenta sun hada da yin walimar kawaye kwana biyu kafin a daura auren. An shirya yin wannan a wurin shakatawar manyan sojoji da ke kan titin filin jirgin sama na MalamAminu Kano. An kuma shirya yin yinin biki a ran 1 ga Yuni.
An dade ana zancen auren Abida da furodusan na fim din Nadama, Ajizi da kuma Zahiri. Wasu na cewa yaudararta kawai yake yi, wasu na cewa a'a ita ce take yaudararsa. Watanni kadan da suka wuce Hamza ya saki matarsa ta fari A'ishatu Mohammed, wadda suka haihu daya da ita, wanda hakan ya kasance share fili ga Abida Mohammed. Ita dai A'ishatu, tuni ta shiga harkar fim ita ma, har ta shirya fim da kudinta mai suna Tababa, wanda Mohammed Garba Kabara ya ba da umarni.?
Dan'azumi Dafe-Dafe ya yi amarya tare da karrama 'yan fim
Daga ALIYU A. GORA II a Kaduna
Alh. Dan'azumi Usman tre da amaryarsa Hajiya Rabi
|
BAYAN an dade ana artabu da dauki-ba-dadi da fitaccen dan wasa kuma furodusa Dan'azumi Usman (Dafe-Dafe) a kan dangantakarsa da Hajiya Rabi, sakamakon saka ta a fim dinsa mai suna An Yanka... da ya yi, da yake Allah shi ke maganin komai, ya kaddara aure a tsakaninsu, wanda aka daura a ranar Jumma'a, 24 ga Mayu 2002.
An daura auren a kofar gidan iyayen amarya da ke layin Hausawa a Tudun Wada, Kaduna, da misalin karfe 3 na rana a kan sadaki N6,000. 'Yan fim da dama sun halarci bikin daga sassaa daban-daban na kasar nan. Sun hada da Ashiru sani Bazanga, Auwalu Marshal, Adamu Kwabon Masoyi, Magaji Sulaiman, Nata'ala Aliyu, Ali Abdullahi, SaminuMoh'd Mahmud, Galin Money, Husaina Tsigai, Cinnaka, Dan Wanzam, Rabi'u Rikadawa (Dila), ds.
Lokacin da Rabi ta fito a shirin An Yanka..., mijinta ya yi karar Dafe-Dafe a Abuja a kan ikirarin ya sa matar aure a fim ba tare da sanin mijinta ba. Abin ikon Allah, sai ga shi watanni kadan bayan waccan rigima Dan'azumi ya aure matar, wadda aka ce yana kauna kamar me.
A hirarta da mujallar Fim, amaryar ta bayyana farin ciki game da wannan aure, inda ta ce ba ta taba samun kanta cikin farin ciki kamar irin na wannan ranar ba. A cewarta, ko banza wannan aure ya zame mata na huce haushi.
Shi ma angon ya yi wa Allah godiya da ya nuna masa wannan rana ta auren shi da Hajiya Rabi. Ya kuma yi godiya ga jama'ar da suka samu halartar bikin, tare da yin addu'ar Allah ya maida kowa gida lafiya.
Haka kuma Alh. Dan'azumi ya yi amfani da bikin auren ya karrama wasu fitattun 'yan wasa sababbi da tsofaffi, furodusoshi, da kuma wasu kafafen watsa labarai, ciki har da mujallar Fim. Wasu da aka karrama din sun hada da gidan Rediyon Tarayya na Kaduna da na Jihar Kaduna, N.T.A. Kaduna, DITV, KSMC, Abdullahi MaiKano Usman, Abdu Haro Mashi, Hamisu Iyan-Tama, Yakubu Lere, Usman Baba Pategi, Kasimu Yero, Mustapha Moh'd (Danhaki), Umar Bawa Dukku, Na'ta'ala Aliyu, Ashiru Sani Bazanga, Adamu Bello (Ability), Balaraba Ramat, Saminu M. Mahmud, Ishaq Sidi Ishaq, Adamu Kwabon Masoyi, Sambo Idris Sambo Hakimin Funtuwa, Dan Iyan Zazzau Yusuf Ladan, Rashida Bello, da sauransu.
An yi bikin ne a gidan wasan kwaikwayo da raya al'adun gargajiya na Marhaba da ke lamba BB 1, Ibrahim Taiwo Road, Tudun Wada, Kaduna. An kuma yi lafiya, an tashi lafiya, kowa na cewa, "Allah maimaita mana."
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin