Jim kadan da kammala daurin auren Balaraba, mahaifinta MALAM MUHAMMADU KAURA ya tattauna da wakilinmu inda ya bayyana farin cikinsa kan al'amarin aurenta, kuma ya sa mata albarka. Ga wani bangare na hirar:
Fim: Baba, ya za ka bayyana irin farin cikinka a kan wannan daurin aure da aka yi yau?
MALAM MUHAMMADU KAURA: Tirkashi! To ni ya ma zan bayyana shi? Illa godiya ga jama'ar Annabi da suka zo suka taru a nan, na gode masu. Allah Ubangiji kuma yai ma kowa albarka. Allah kuma ya saka ma kowa da albarka.
Akwai wani sako daga gare ka zuwa ga Ango da Amarya?
MALAM MUHAMMADU: Sako daya ne tare da addu'a: Allah Ubangiji ya sa su zauna lafiya. Shi kuma Ango da sauran danginsa (su yi ta) hakuri. Duk abin da ya faru, in mai rai ya yi hakuri sai ya ga karshensa. Saboda mutane sun tako har gidana su yi min sallama su zage ni a kan Balaraba. Amma yau ga shi Allah ya kawo ta yi aure yadda duk diya ke yi. Ni alhamdu lillahi.
Daga cikin 'ya'yanka, akwai wadda ta yi aure har aka tara jama'a kamar wannan?
MALAM MUHAMMADU: A'a, ko alama! Wannan shi ne na taba ganin taron jama'a sun zo saboda ni. Wannan shi ne na farko, kuma gaba Allah ya bar wa kansa sani.
A cikin 'ya'yanka Balaraba ce mafi kusa da kai. To kuma ga shi Allah ya sa an daura mata aure za ta tafi. Akwai wata damuwa a cikin zuciyarka?
MALAM MUHAMMADU: A'a, ba damuwa sai farin ciki tunda yake da ma abin da Allah ya ce kenan - yau na fita hakkinta tunda na aurar da ita. Kuma Allah ya yi mata albarka!
Wane sako gare ka ga mutanen da suka halarci wannan daurin Auren?
MALAM MUHAMMADU: Sakona sai dai in sake maimaitawa. Sakona gare su (shi ne), godiya, da rokon Allah ya maida kowa gidansu lafiya, kuma inai masu godiya.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin