Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 29   Mayu 2002
Mu Leka Hollywood


BABBAN SHAFI
Mu Leka Mu Gani
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 1
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 2
Rayuwarmu
Mu Leka Hollywood
Malam Zurke
Mutanen Boye
Bukukuwa
Sauran Labarai
Ra'ayi Ba Gaba ne
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Akwai:
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


Malam Muhammad Kaura, Mahaifin Balaraba ...a ranar auren
Oscars: Bakar fata sun lashe sun sude
Daga IRO MAMMAN

JARUMIN fim din Training Day, wato shahararren dan wasan nan Denzel Washington, shi ne ya ci kyautar Jarumin Jarumai Maza a gasar finafinai ta duniya mafi shahara, wato Oscars, ta bana. Sau uku ana zabensa a mataki na kusa da na karshe, amma sai a bana ne ya samu sa'a ya doke manyan jarumai irin su Rusell Crowe, Sean Penn da Will Smith.

Haka kuma jaruma Halle Berry ce ta lashe gasar a ajin Jarumar Jarumai Mata saboda wasan da ta yi cikin shirin Monster's Ball. A da, an zaci cewa Dame Judi Dench ko Nicole Kidman ce za ta cinye zaben.

Mai ba da umarnin nan Ron Howard shi ya doke 'yan maza a matsayin Daraktan Daraktocin Duniya, tare da fim dinsa A Beautiful Mind, fim din da har ila yau shi aka zaba a matsayin Gwarzon Fim na bana.

An rarraba kyaututtuka a bangarori daban-daban ga wasu zakarun. A karshe an ba da kyaututtuka na musamman ga wasu mutum uku da aka ga lallai sun taimaka wajen habakar shirin fim na Amerika, su ne Sidney Poitier da Robert Redford da Arthur Miller.

An yi bikin bayyana zakarun gasar ne a dandalin 'Kodak Theatre' da ke cikin unguwar 'yan fim ta Amerika, wato Hollywood, a birnin Los Anjalis.

Wani abin juyayi a bikin shi ne yadda bakaken fata suka yi zarra a gasar bana, abin da ba a saba gani ba. Su ne Denzel Washington da ita Halle Berry. Jawaban da suka yi sun nuna yadda akan maida bakake gugar yasa a gasar Oscars; duk da fasahar iya wasa da bakake suke da ita, ba a cika ba su manyan kyaututtuka ba. Misali, rabon da a ba mace bakar fata matsayin Jarumar Jarumai Mata yau shekara 74. Shi ya sa ake ganin lallai bikin na bana biki ne na bakaken fata.

Lokacin da Halle Berry ta zo yin jawabinta, ta yi ta rusa kuka, tana cewa, "Wannan zamani da muka shigo ya fi karfina. Wannan karramawa ce ga dukkan mata bakaken fata wadanda suka wuce ba a san su ba, wadanda sai yau aka bude masu kofa. Lallai a yau an rusa iyakar da aka yi mana (mu bakake) kuma ina fatan wannan rusawar da aka yi za ta kasance a haka har abada." Wai har wasu na ganin bai kamata ta fadi haka ba don kar a ce ta yi wa fararen fata shagube.

Shi ma Denzel sai ya ce a cikin raha, "Shekaru arba'in ina biye da sawun Sidney (Poitier) to me kuwa suka yi - in ba suka ba shi kyauta shi ma a wannan daren ba."

A cikin 1990 an ba Denzel kyautar Jarumin Jarumai na Biyu saboda wasansa a wani fim mai suna Glory.

A bikin na bana an ba fim din The Lord of the Rings: The Fellowship of the Ring kyaututtuka hudu, koda yake ba su kai matsayin Gwarzon Fim da aka yi zaton shirin zai ci ba. Sannan wasu finafinan da aka zaci za su doke kowanne, wato Moulin Rouge da Black Hawk Down, sun ci kyaututtuka biyu biyu kowannensu, sannan dan wasa Jim Broadbent ya ci kyautar Jarumin Jarumai na Biyu (Best Supporting Actor), irin matsayin da Ahmed S. Nuhu ya ci a gasar Arewa lokacin da Momo ya ci matsayin da a yau Denzel Washington yake a kai a Amerika.

Kada ku manta, a Amerika suna ba da kyauta ga Jarumar Wakar Fim wadda mu ba a ba da ita a nan. A Oscars, wakar "If I Didn't Have You" wadda Randy Newman ya rera aka sa a fim din Monsters, Inc., ita ta ci kyautar.

Bikin na Oscars, wanda kuma ake kira 'Academy Awards,' ya shero mutane kwarai musamman saboda yadda mai gabatar da bikin, jaruma Whoopi Goldberg, ta rika tsokanar mutane tana sa kowa tintsirewa da dariya.

A bara, fim din Gladiator ne ya ci Gwarzon Fim da kyaututtuka biyar, kuma aka nada Russell Crowe Jarumin Jarumai. A bana, duk sun zama 'yan kallo domin biki ne da bakar fata suka lashe suka sude.

A fitowarmu ta gaba: Za ku ji tarihin Denzel Washington da fadi-tashinsa a harkar fim, har ya kai ga wannan matsayi da ya hau a bana. Ku biyo mu!

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin