Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 30   Yuni 2002
Duk sun yi aure


BABBAN SHAFI
RA'AYI
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) 
Rayuwarmu
Duk Sun Yi Aure
Malam Zurke
Ra'ayin Mujallar Fim
Bukukuwa
Sauran Labarai
Ra'ayi Ba Gaba ne
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


Momo ya yi aure American Style!
Ya ba wasu 'yan fim haushi

Daga MUHAMMED NASIR a Kano

Momo
Aminu A. Shariff (Momo)
FITACCEN dan wasa Aminu A. Shariff (Momo) ya yi auren ba-zata, inda ya shammaci 'yan fim ta hanyar kin gaya wa kowa cewa zai yi aure. Ya tura waliyyai aka daura masa aure da masoyiyarsa, wata zabiyar finafinai mai suna Maryam Mohammed.

An daura auren 'yan fim din biyu a ran Lahadi, 19 ga Mayu, 2002 a kasar Nijar inda dangin amaryar suke. Da yawan 'yan fim a Kano ba su gaskata labarin ba a ranar da abin ya faru, suna ganin ba yadda za a yi Momo ya yi aure bai gayyace su ba.

Mun ji 'yan fim da dama suna zunde suna cewa, "Momo ya kyauta da ya yi mana haka." A Kaduna, lokacin daukar fim din Daren Farko wanda aka yi a daidai lokacin daurin auren, 'yan fim da dama sun nuna bacin rai da abokin nasu ya share su ya yi aure bai gaya masu ba. Har wani yana cewa, "Yasin idan na ga Momo ba zan ce masa muna murna ba, domin ya nuna mani bai san da zamana ba." A Kano kuma, masu tunanin ko da kasar 'Gaban Gabas' za a dauro auren Momo sai sun je, sun bayyana rashin jin dadi kan kin gayyatarsu da jarumin finafinai kamar Kauna, Ukuba da Jumurda ya yi.

Bayan an daura auren, wakilan mujallar Fim sun yi kokarin jin ta-bakin angon, amma bai ganu ba. Duk da haka wata majiya ta shaida masu cewa, "Aure kawai aka daura amma za a yi shagalin tarewa nan gaba kadan."

Soyayya tsakanin Aminu da Maryam ta dade kuma ta yi danko matuka. Zabiyar ta sha nuna aniyarta a fili cewa Momo ne mijinta, kuma ta fafata da 'yan mata da dama masu son su auri jarumin wanda yake da dimbin farin jini ga 'yan mata. Wannan mujallar ta taba kawo maku hira da Maryam a watan Nuwamba 2001. Daga cikin wakokin da ta rera a finafinai ta fi son wakar "Lale Alalo Lale" ta cikin shirin Alqibla.

Tambayar da ake yi a fagen shirin fim ita ce: me ya sa Momo ya yi auren ba tare da sanarwa ba, abin da wata 'yar wasa ta kira "American-style"? Ga tsokacin da wani furodusa ya yi: "Ba mamaki yana gudun 'yan hana-ruwa-gudu ne don kada a sanar kowa ya ji a nemi yi masa kafar angulu." Shi ma wani mai tsara fostar finafinai a komfuta cewa ya yi Momo ya burge shi domin "auren Fati da na Balaraba duk an samu mahassada." Amma Momo da ya yi haka, inji shi, "shikenan, da mai kaunar abin da mahassada sai dai kawai su ji har an yi an gama."

Tun tuni mujallar Fim ta fahimci alamun Momo zai aikata abin da ya yi. Wakilanmu sun sha tuntubarsa zancen aurensaa Maryam amma sai ya ce a jira sai an sa rana tukuna. Ita ma Maryam ko mako daya kafin a daura auren mun nemi yin hira da ita, amma sai ta ce, "A bari sai an sa rana, idan na samu izininsa sai a tattauna da mu tare."

Ba shakka da a ce an gayyaci mutane, to kuwa da al'ummar Nijar sun yi kallon 'yan wasan da ba su taba ganin yawansu a kasar ba. Rashin tara mutane a rankaya daurin auren ya nuna cewa har yanzu akan sami wasu masu yin kutungwila a inda duk suka ji wani abin alheri zai bayyana. To irinsu ake kauce mawa kenan?

Irin wannan ya sha faruwa a fagen shirin fim na Amerika da Indiya. Misali, lokacin da shahararren jarumin finafinan Amerika din nan Tom Cruise zai auri fitacciyar jaruma Nicole Kidman, sun boye wa duniya abin da suke ciki. Suka sulale aka daura masu aure a wani tsauni da ke lullube da dusar kankara cikin Jihar Kolorado da ke Amerika a daidai lokacin da hankalin jama'a ya koma kan shagulgulan Kirsimati da ake yi a ranar, cikin Disamba 1990.

Amma duk da yake sun guje wa manema labarai, ba su tsira ba. Bayan angon da amaryar sun tare sai kuma bayan 'yan shekaru masu sa ido kan al'amarin suka rika yi masu munanan kalamai. Ganin ba su haihu ba kuma sun dauko 'ya'yan riko har guda biyu sun maida su nasu, sai aka rika cewa da ma ba su haihuwa, wai shi ya sa suka yi aure don kawai sha'awarsu ta yin ba-saje.

Momo da Maryam, Allah ya ba da zaman lafiya da zuri'a dayyiba, amin!

... Walimar auren Momo da Maryam ta kayatar

Maryam
Maryam Mohammed
A ranar Juma'a, 24 ga Mayu aka yi walimar auren Aminu Shariff (Momo) da Maryam Mohammed, a dakin cin abinci na otal din Durbar da ke kan hanyar zuwa Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano a Kano. Kamar yadda 'yan fim da yawa ba su san an daura auren ba, ita ma walimar da yawa daga cikinsu ba su san am yi ba duk kuwa da cewa an raba katin gayyata ga wasunsu, abin da ya kara harzuka wasu da suke ganin Momo bai kyauta masu ba.

An fara walimar da misalin karfe 6:30 na yamma. Bayan an bude taron da addu'a sai aka kira wasu aka ce su zauna a babban tebur. Na farkonsu shi ne babban aboki, Ibrahim Maishunku, sai Aina'u Ade da wata mai suna A'isha. Daga nan sai aka ba shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kano, Ibrahim Mandawari, fili ya yi jawabi kan auratayya da aurarraki na 'yan fim. Bayan haka sai aka fara cashewa da wakokin finafinai daban-daban, inda babban makadin fim Alee Baba Yakasai na kamfanin 'Iyan-Tama Multimedia' ya rika rafsa kida.

''Yan'uwan ango da na amarya da dimbin abokan arziki sun halarci walimar wadda saboda cikowar jama'a sai da dakin ya yi kadan.

Ana cikin cashewa, daidai lokacin da ake watandar cin abinci, sai wutar lantarki ta dauke. Har wasu 'yanmata sun fara hargowa sai nan da nan hukumar otal din ta tada janareto, wuta ta zo. Ango da amarya ma sun cashe lokacin da aka kada masu kidan wakar "Rabbi Allah Sarki Wahidun, Taimaka Mana Ummi Ta Yi Lafiya" ta cikin fim din Maqabuli. Tun ba su kai ga sakan 30 da fara rawar ba sai aka baibaye su ana yi masu liki. 'Yan likin sun yi yawa har ta kai ba a iya ganin ma'auratan biyu.

Manyan 'yan fim maza da mata sunh halarci wurin. Kadan daga cikinsu akwai shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Arewa, Hamisu Lamido Iyan-Tama, da Nura Ilu Dambazau, Hafizu Bello, Rabi'u Ibrahim HRB, Bala Anas Babinlata, Ahmad S. Alkanawy, Malam Sheikhmai 'Godiya & Danhassan,' Aminu Ilu Dambazau, Baballe Hayatu, Lawan Dansokoto, Hamza Danyaro, da sauransu.

A bangaren mata kuwa akwai Hindatu Bashir, Saima Mohammed Raga, Abida Mohammed, Fatima Ahmed, da sauransu.

Abu ya yi armashi. Duk da haka, Momo da kansa ya so ya bata rawarsa da tsalle lokacin da ya shiga zagin masu daukar hoton biki, wai shi ba ya so a buga shi a mujalla ko a kalanda kamar yadda aka saba yi wa dukkan dan fim din da wani abin alheri ya same shi. Wakilinmu ya lura cewa Momo ya yi dukkan yadda zai yi ya ga ba a fada waq duniya batun aurensa ba. A wurin walimar, an ji wani furodusa yana tsaki yana cewa, "Gaskiya Momo ya ba da mu. Sai ka ce ba wayayye ba! Ko me yake boyewa? Oho!"

Wata kawar amarya kuma ta ce, "Wallahi Maryam ba ta ji dadin yadda Momo ya hana a sa su a mujallu yadda akan yi wa kowa ba. Ta so a ce sun tattauna da mujallar Fim an sa su a cover. Mu ma dai abin bai yi mana dadi ba a ce wai ana boye wannan abin tarihi kuma na farin ciki."

Wani fitaccen jarumi kuwa cewa ya yi, "Allah ya kai mu lokacin nawa auren. Ba abin da zan boye. Kuma 'yan mujalla su ne na farko da zan ba katin gayyata zuwa aurena."

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin