Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa    Bangon mujallar Fim kenan na wannan wata
FITOWA TA 29  Mayu 2002              ISSN:1595-7780


BABBAN SHAFI
Mu Leka Mu Gani
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 1
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 2
Rayuwarmu
Mu Leka Hollywood
Malam Zurke
Mutanen Boye
Bukukuwa
Sauran Labarai
Ra'ayi Ba Gaba ne
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Akwai:
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


Shu'aibu 'Kumurci'

Yadda muka rabu da Balarabata

Hirar musamman da Shu'aibu Kumurci

ABIN bakin cikin da ya samu Shu'aibu Lawan (Kumurci) zai iya samun kowa. To amma ba kowa ba ne zai iya karbar kaddara irin yadda shi Shu'aibu ya karba a kan rasuwar amaryarsa Balaraba Mohammed.

A cikin wannan hirar da suka yi da mujallar Fim mako uku bayan hadarin, Shu'aibu ya fadi yadda rabuwarsu ta kashe da Balaraba ta kasance a ranar da ta rasu, da yadda labarin ya zo masa, da kuma ra'ayinsa kan batun cewa wasu ne suka "jefe" ta, sa'annan da wani mafarki da ya yi game da Balaraba wanda a cewarsa zai iya kasance alkhairi gare shi da kuma iyayenta.

Cikakkiyar hirar




An yi karar wasu 'yan fim na Kano a kotun Abuja


KOTUN shiyya ta 2 (wato District Court II) da ke cikin unguwar Wuse Zone II a cikin babban birnin tarayya, Abuja, ba ta da wani bambanci da sauran kotunan da ke yawancin birane irin ta. Da shigar mutum zai tabbatar da haka idan ya fara yin arba da katifu, kekunan dinki, kujeru masu kushin, tsofaffin motoci, kyawaren dakuna masu tsada, tulin darduma, firji, da sauransu. Inda kawai za a iya cewa ta bambanta da ta wasu sassan arewacin kasar nan shi ne da yawa daga cikin ma'aikatan kotun ba Hausawa ba ne, sai dai suna dan fahimtar Hausa.

Cikakken Labari




Shin auren Saliha ya makale ne?


SHIN me ake ciki game da auren nan da aka yayata za a yi na fitacciyar jaruma A'isha Ibrahim (Saliha)? An fasa ne ko kuwa?

Wadannan tambayoyin ne mutane da dama a ciki da wajen fagen shirin fim suke ta yi a cikin 'yan watannin nan, ganin cewa an shafe watanni tun lokacin da aka ce za a yi auren amma shiru kake ji kamar an aiki bawa garinsu.

Cikakken Labari



An mari Rukayya Dawayya a Zariya


A KODA yaushe, idan aka ce mutane sun taru don gudanar da wadansu ayyuka, ya-Allah ko na suna ko na aure ko kuma makamancin wannan, za ka ga mutane da halaye daban-daban, wasu masu hakuri wasu kuwa ba su da hakuri. Dalilin haka ne za ka ga sababbin maganganu nama juna shigan giragizai, musamman a wannan lokaci na shirin finafinan Hausa.

Cikakken Labari



Assha! An soma yin finafinan tsiraici

Hattara! 'Yan kudu sun fito da sabuwar hanyar dulmiyar da jama'a tare da damfarar 'yan kallo.

Cikakken Labari



Fim ya fi wa'azi shiga, cewar Zakzaky

AN bayyana cewa wasan kwaikwayo babbar harya ce ta shigar da sakonni a zukatan mutane, musamman ganin cewa ba sosai jama'a kan dauki wa'azi a halin yanzu ba.

Shugaban Rundunar 'Yan'uwa Musulmi a Nijeriya, Malam Ibrahim Yakub Al- Zakzaky ne ya yi wannan furucin a babban dakin taro na otal din 'Royal Tropicana', Kano, lokacin da ake kaddamar da wani fim da 'Yan'uwa Musulmi Mata (Muslim Sisters) suka shirya mai suna Karbala.

Cikakken Labari



Mu rika karfafa shari'a a finafinanmu


Inji Amina Muhammad, jarumar shirin TABBAS

Cikakken Labari


 
  GIDAUNIYAR TUNAWA
DA
BALARABA
  Inkiya Mujallar Fim, No. 22, Zaria Road, Gyadi-Gyadi, Kano & S. 11, Ibrahim Taiwo Road, T/Wada, Kaduna

Muna sanar da jama'a cewa mun kafa Gidauniya ta musamman domin karrama marigayiya Balaraba Mohammed.

Manufar Gidauniyar ita ce mu tattara taimako na kudi ko makamancinsa wanda za mu mika ga magadan Balaraba.

Muna rokon jama'a ('yan fim da wadanda ba 'yan fim ba) su ba da dukkan abin da ya samu a matsayin alamar juyayi da nuna kauna da tausayawa kan nasarorin da Marigayiyar ta samu a harkar fim da kuma musamman gudunmawar da ta bayar wajen bunkasar harkar shirin fim na Hausa.

Babu ruwan wannan Gidauniya da siyasa. Ba wani ya sanya mu ba, mu muka ga dacewar yin wannan abu musamman bayan dimbin mutane sun waiwaye mu a kan batun irin wannan Gidauniyar.

Duk wadanda suka ba da wani abu za mu tattara sunayensu da adireshinsu da abin da suka bayar mu buga a mujallu domin duniya ta san abin da aka samu na taimakon. Mun kafa Kwamitin Amintattu da zai gudanar da Gidauniyar.

Sa hannun:

Malam Ibrahim Sheme, Mai sanarwa

Membobin Kwamitin Amintattu na Gidauniyar Tunawa Da Balaraba Mohammed su ne:

1. Ibrahim Sheme - Mujallar Fim 2. Balaraba Ramat Yakubu - Ramat Production 3. Ahmad S. Al-Kanawy - Iyan-Tama Multimedia 4. Ishaq Sidi Ishaq - I.S.I. Production 5. Bala Makosa Zaria - Mujallar Nishadi 6. Abdurrasheed M. Kankia - Abab Production 7. Aliyu Abdullahi Gora II - Mujallar Fim 8. Hafizu Bello - HB Entertainment 9. Ashafa Murnai Barkiya - Mujallar Fim 10. Bashir Yahuza Malumfashi - NPF, Katsina 11. Saratu Gidado - Kano 12. Nata'ala Aliyu Zaria - Jari Film Production

Za ku iya mika dukkan taimakon da ya samu ga kowane memba na wannan kwamitin, shi kuma zai mika ga Hajiya Balaraba Ramat Yakubu, wadda ita ce Ma'ajin wannan Kwamiti. Kamar yadda muka ce, za mu bayyana yawan abin da aka tara da kuma sunayen duk wanda ya ba da taimako. Allah ya ba da ikon taimakawa, amin.


Safiya Mu'azu tare da Balaraba Muhammad


Wasu Finafinan Balaraba:
 
  1. MARYAM 1* & 2*
  2. MATAR UBA*
  3. FURUCI 1* & 2*
  4. TAWAKKALI 2*
  5. ZAINAB*
  6. DAWAYYA 1* & 2
  7. BIYAYYA
  8. JAHEED 1* & 2
  9. MUJARRABI 1* & 2
  10. IKIRARI 2
  11. SO...
  12. YAQINI 1* & 2
  13. RIGAR 'YANCI 1* & 2
  14. NABILA
  15. KATA'I
  16. TANGARAN
  17. KACIBUS 1* & 2
  18. HALI 1* & 2
  19. DAFA'I
  20. TASIRI 1* & 2
  21. GUMBAR DUTSE (Kumurci ya shirya shi)
  22. SABABI
  23. KWANDALA
  24. AMALALA*
  25. BARAZANA
  26. SARKAKIYA 2*
  27. SHAHARA
  28. A BAR WA ALLAH
  29. BA A NAN TAKE BA
  30. TSIRA
  31. SABUWAR RAYUWA
  32. KASKA
Wadanda aka yi wa alama haka * su ne suka fito kasuwa.
KURAKURANMU
A
LABARAN
BALARABA

Bayan fitowar mujallar Fim ta watan jiya, mun yi la'akari da wasu kurakurai uku da suka fito a cikin labaran da muka bayar a kan bikin Balaraba da kuma rasuwarsu. Kurakuran sun auku ne saboda yanayin yadda muka yi aikin fito da mujallar da wuri; wakilanmu sun rika tattaro bayanai a cikin sauri suna kawo wa editocinmu domin gyarawa da kuma mikawa ga masu aikin komfuta, saboda haka aka samu 'yan bambance-bambance na bayanan. Mun bincika, mun ga kurakuran ba su da yawa, to amma ga gyaransu:

1. A wasu wurare, mun kawo shekarun Balaraba a mabambanta. Misali, a shafi na 34 mun ce shekarunta 21. To, shekarun rayuwarta da muka yi ta nanatawa a saman kowane shafi (wato 1983-2002), su ne daidai. Wato dai shekarunta 19 a duniya.

2. A gabatarwar da muka yi a shafi na 19 mun nuna cewa Abubakar yayan Balaraba ya kasance babban da a gidansu sakamakon hadarin da ya auku wanda ya yi sanadiyyar salwantar rayukan 'yan'uwansa. To amma kuma mun kawo hira da yayan Abubakar din, wato Abdullahi (Riskuwa) wanda Allah ya tserar daga hadarin. Bayanin da yake daidai shi ne, yanzu Abubakar shi ne da na biyu a gidan domin wansa Abdullahi yana nan da ransa.

3. Akwai inda muka nuna cewa an tafi kai Balaraba gidan miji ne aka yi hadarin. To, kamar kuma yadda muka nuna a wasu wuraren, an raka ta Kano ne domin halartar bikin Gala da abokan Shu'aibu suka shirya don taya su murnar auren, tare da nufin za su dawo washegari (Lahadi). Iyayen su Balaraba sun tsara cewa amaryar za ta yi zama a gidansu a Kaduna na kamar tsawon mako daya ko biyu kafin ta tare a Kano.

Idan kuma mai karatu ya ga wasu kurakuran ban da wadannan, to don Allah ya sanar da mu don mu gyara.

Edita

Ka aiko da tambayoyinka ko sharhinka ga: mujallarfim@yahoo.com