Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa    Bangon mujallar Fim kenan na wannan wata
FITOWA TA 30  Yuni 2002              ISSN:1595-7780



BABBAN SHAFI
RA'AYI
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) 
Rayuwarmu
Duk Sun Yi Aure
Malam Zurke
Ra'ayin Mujallar Fim
Bukukuwa
Sauran Labarai
Ra'ayi Ba Gaba ne
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


Shahararriyar 'yar wasa Fati Muhammad'

Labarin zuwan Fati London

Da rayuwarta da Sani Mai Iska

Rabo na minallahi, tauraruwar taurari Fati Mohammed tana daga dakin mijinta ta samu gayyata zuwa London. Babban dan rakiyarta shi ne mijinta Sani Mai Iska. Me suka je yi? Me suka gano? Me suka koyo? ASHAFA MURNAI BARKIYA ya fahimci cewa ba wanda ya fi SANI MAI ISKA sanin yadda tafiyar ta kasance daga bangaren Fati. Don haka sun tattauna.

Cikakkiyar hirar




Dalilin mutuwar auren Dayyaba Isyaku

Dayyaba Isyaku
Dayyaba Isyaku.. ta fito daga 'auren dole'

YANZU dai ta tabbata cewa auren fitacciyar 'yar wasan nan da ke Zariya cikin Jihar Kaduna, Dayyaba Isyaku, ya mutu mut, kuma jarumar ta shirin Asin Da Asin tana nan tana shirin dawowa harkar fim. Dayyaba ce da kanta ta tabbatar wa da wakilinmu haka a hirar da suka yi kwanan nan a gidansu da ke Kings Road, Muchiya, Zariya.

Cikakken Labari




Finafinan Hausa suna tarbiyyantarwa, cewar A.A. Rasheed


A.A. Rasheed
A.A. Rasheed, shahararren mai sai da kaset na bidiyo

A. RASHEED ba bakon suna ba ne ga masu karanta mujallar Fim ko kallon finafinan Hausa. Yana daya daga cikin manyan dillalan sayar da kasakasan finafinai da kuma na wakokin rediyo a arewacin kasar nan. Shagonsa da ke cikin tashar mota ta Kawo, Kaduna, ba boyayya ba ce.

Kwanan baya wannan hamshadin dan kasuwa ya tattauna da wakilinmu ALIYU ABDULLAHI GORA II inda ya bayyana muhimman ra'ayoyi dangane da shirin fim na Hausa.

Ga yadda tattaunawar ta kasance:



A yi adalci kafin a zarge mu - Maikano


Abdullahi Maikano Usman
Abdullahi Maikano, Sakataren kungiyar Furodusoshi

Ba wannan bane karo na farko da mujallar Fim ta tatauna da Babban Sakataren Kungiyar Furodusoshi ta Arewa, Malam Abdullahi Maikano Usman. A baya, ya sha yi mana bayani kan alkiblar kungiyar da kuma nasarorinta.

A wannan hirar da suka yi da Fim, Malam Maikano ya yi kokarin kare Shugabannin kungiyar daga zargin da ake yi masu na ba a ga aikin da kungiyar ta yi na a-zo-a-gani ba.

Cikakkiyar hirar:



Manufar Gidauniyar Balaraba, Cewar Ishaq

Ishaq Sidi Ishaq
Ishaq Sidi Ishaq, Shugaban Gidauniyar tunawa da Balaraba

KWANAN nan wani gungun masu harkar shirya finafinan Hausa suka taru suka kafa kwamiti domin tunawa da jarumar 'yan fim din nan wadda Allah ya yi wa rasuwa a hadarin mota kwana daya bayan an daura mata aure, wato Balaraba Mohammed. Mun ji cewa nan ba da dadewa ba za a yi gagarumin taron kaddamar da Gidauniyar Tunawa da Balaraba inda ake sa ran tara kudi ko wani taimako don bai wa magadan marigayiyar. Shugaban kwamitin shi ne shahararren dan wasan nan kuma darakta, ISHAQ SIDI ISHAQ.

A cikin wannan hirar da Ishaq ya yi da wakilinmu a Kano, ya bayyana manufar kwamitin, da ra'ayoyinsa kan yadda yake ganin ya dace 'yan fim su tashi tsaye wajen karrama kansu da kansu, ba sai wani ya ce masu su tashi su yi abu kaza ba.

Bismilla:



Musulunci bai kafu ba sai ta hanyar wasan kwaikwayo
Inji Shaikh Yusuf Ali

A KOKARINSA na nuna muhimmanci da halascin wasan kwaikwayo a cikin addinin Musulunci, fitaccen malamin nan mazaunin Kano mai suna Sheikh Yusuf Ali, ya ce duk wani mutum da zai fito ya ce bai dace a yi wasan kwaikwayo ba, to wannan mutum bai fahimci Musulunci ba ko kuma yana da wata manufa daban.

Cikakken Labari



Yadda hadarin jirgi ya shafi wasu 'yan fim


A FARKON watan jiya ne bala'in hadarin jirgin sama ya auka wa birnin Kano, ya jawo salwantar rayuka kimamin 100. Yawancin mazauna gidajen da jirgin ya fada kuma sun sami munanan raunuka. Daga cikin wadanda dukiyarsu ta salwanta ta hanyar gobara, akwai wani dan wasan fim mai suna Haruna Rabi'u, wanda aka fi sani da Baba Kusa. Cikin wannan labari za ku ji asarar da dan wasan ya yi da kuma wasu bayanai da sauran mujallu ko jaridu ba su ba ku su ba.

Cikakken Labari


 
  GUGUWAR AURE A FAGEN SHIRIN FIM: Halima Adamu Yahaya Aminu A. Sharif (Momo) Dan'azumi (Dafe-Dafe) tare da amaryarsa Abida da Angonta Hamza Ta nan za ka sha cikakken labari
GIDAUNIYAR TUNAWA DA BALARABA   Inkiya Mujallar Fim, No. 22, Zaria Road, Gyadi-Gyadi, Kano & S. 11, Ibrahim Taiwo Road, T/Wada, Kaduna

Muna sanar da jama'a cewa mun kafa Gidauniya ta musamman domin karrama marigayiya Balaraba Mohammed.

Manufar Gidauniyar ita ce mu tattara taimako na kudi ko makamancinsa wanda za mu mika ga magadan Balaraba.

Muna rokon jama'a ('yan fim da wadanda ba 'yan fim ba) su ba da dukkan abin da ya samu a matsayin alamar juyayi da nuna kauna da tausayawa kan nasarorin da Marigayiyar ta samu a harkar fim da kuma musamman gudunmawar da ta bayar wajen bunkasar harkar shirin fim na Hausa.

Babu ruwan wannan Gidauniya da siyasa. Ba wani ya sanya mu ba, mu muka ga dacewar yin wannan abu musamman bayan dimbin mutane sun waiwaye mu a kan batun irin wannan Gidauniyar.

Duk wadanda suka ba da wani abu za mu tattara sunayensu da adireshinsu da abin da suka bayar mu buga a mujallu domin duniya ta san abin da aka samu na taimakon. Mun kafa Kwamitin Amintattu da zai gudanar da Gidauniyar.

Sa hannun:

Malam Ibrahim Sheme, Mai sanarwa

Membobin Kwamitin Amintattu na Gidauniyar Tunawa Da Balaraba Mohammed su ne:

1. Ibrahim Sheme - Mujallar Fim 2. Balaraba Ramat Yakubu - Ramat Production 3. Ahmad S. Al-Kanawy - Iyan-Tama Multimedia 4. Ishaq Sidi Ishaq - I.S.I. Production 5. Bala Makosa Zaria - Mujallar Nishadi 6. Abdurrasheed M. Kankia - Abab Production 7. Aliyu Abdullahi Gora II - Mujallar Fim 8. Hafizu Bello - HB Entertainment 9. Ashafa Murnai Barkiya - Mujallar Fim 10. Bashir Yahuza Malumfashi - NPF, Katsina 11. Saratu Gidado - Kano 12. Nata'ala Aliyu Zaria - Jari Film Production

Za ku iya mika dukkan taimakon da ya samu ga kowane memba na wannan kwamitin, shi kuma zai mika ga Hajiya Balaraba Ramat Yakubu, wadda ita ce Ma'ajin wannan Kwamiti. Kamar yadda muka ce, za mu bayyana yawan abin da aka tara da kuma sunayen duk wanda ya ba da taimako. Allah ya ba da ikon taimakawa, amin.


Safiya Mu'azu tare da Balaraba Muhammad
TUDU NAWA HABIBU YARO YAKE CI?
Kuma me ya hana shi auren 'yar fim?
Habibu Yaro
Danna nan ka sha labari


Mu San 'Yan Wasa
KISISINA
Hadiza Usman

Hadiza Usman
SUNA: Hadiza Usman
RANAR HAIHUWA: 3/5/85
GARIN HAIHUWA: Pambeguwa, Jihar Kaduna
LAKABI: Kisisina
MATSAYIN KARATU: Ina SS II ne
SHEKARAR FARA FIM: 2001
FIM DIN FARKO: Kisisina
FINAFINANKI: Kisisina, Asali, Tijara, Gudun Hijira Salsala, Manufa, Nasir, Harkalla, Janhuru
WANENE GWANINKI?: Zulkifilu Muhammad
KALAR DA KIKA FI SO: Fari
DARAKTOCIN DA KIKE SON YIN AIKI DA SU: Tijjani Ibraheem, Ishaq Sidi Ishaq, Magaji Suleiman, Adamu Bello, Tukur El-Wadawiy
ABIN KI: Munafinci
ABINCI DA KIKA FI SO: Tuwon shinkafa ko doya
SHA'AWA A FIM? Zaman lafiya
MOTAR DA KIKA FI SO: Honda Civic


Ka aiko da tambayoyinka ko sharhinka ga: mujallarfim@yahoo.com