|
|
| BABBAN SHAFI |
|
| RA'AYI |
| Zuwa Ga Masu Karatu |
| Wasiku |
|
| Balaraba Muhammad (1983-2002) |
| Rahoton Musamman |
|
| Rahoto |
| Malam Zurke |
| Ra'ayin Mujallar Fim |
|
| Bukukuwa |
| Sauran Labarai |
| Fitattun Taurari |
| Dangane Da Mu |
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS
|
|
Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet. An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo! A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu. JE KA TA NAN
| |
Je ka 
 
NORTHERN STAR FILMS
KE GABATAR DA
GAGARABADAU
Shiryawa: MUJALLAR Fim
Darakta HAFIZU BELLO
Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.
Labari/Tsarawa: Iro mamman;
Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito
BABU IRINSA!
Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...
Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...
Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...
Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka!
Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka
| |
|
In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
| |
|
| |
|
 Hira da 'Yaro Mai Tashi'
Shin me AHMED SADIQ NUHU zai ce game da tashen da Allah ya sa ya yi a Kano bayan ya zo daga Jos? Me zai ce kan batun da ake yi cewa ya yi kama da Tukur S. Tukur (Dandugaji)? Wace wasiyya ce mahaifinsa ya yi masa kafin ya rasu? Mecece dangantakarsa da Ali Nuhu da kuma Maryam Aliyu? Me zai ce kan masu cewa Ali yana da 'jan aji'? Wace wakar fim ce bai so a rayuwarsa? Wace morewa su Fati da Abida suka yi masa kafin su yi aure? Wace wahala ya sha a lokacin daukar Sharadi? Me zai ce kan masu cewa FKD suna halin hankaka ne, maida-dan-wani-naka? Shin zai so ya karo karatu? Ya yake ji game da gasar Arewa ta bana da ke tafe - yana jin zai ci Best Actor kuwa?
Cikakkiyar hirar
Maryam Aliyu: Me ya same ta ta bace?
Maryam: 'Ba wanda ya yi mani asiri'
|
Ta bace daga fagen shirin fim tsawon wata daya. Kuma ta bar baya da kura, ana ta cewa ba ta da lafiya ... Shin ina jarumar shirin Mushaqqa da Sharadi ta shige ne? Kuma me take ciki? Ta bar shirin fim babu ko bankwana kenan?
Cikakken Labari
Wai Balaraba za ta dawo!
Balaraba Muhammad: Allah ya ji kanta
|
IDAN kana da rai babu abin da ba za ka ji ba. Kuma babu abin da ba za ka gani ba. Abin da al'ummar kasar nan suka ji a cikin ''yan makwannin nan, daga tsakiyar watan jiya zuwa yau, shi ne wai shahararriyar 'yar wasan fim din nan Balaraba Mohammed, wadda ta rasu a ran 16 ga Maris na bana, za ta dawo duniya! Wai ba ta mutu ba! Wai wani Banufe ne ya dauke ta, ya musanya ta da wata gawa mai kamanninta! Wai idan za a ba shi aurenta zai iya dawo da ita!
Ga cikakken labarin
Nura Imam: Dashen da Allah ke so..
Nura Imam, dan gidan Limamin Kano
|
NURA Imam yaro ne matashi dan shekara 21. Fari ne, kyakkyawa, wanda wasu mutane idan sun gan shi sukan yi tunain ko dan wani mai hannu da shuni ne ya kyamaci dukiyar mahaifinsa ya shiga harkar fim. To, baban Nura dai ba wani hamshakin attajiri ba ne, amma kuma hamshaki ne a matsayin da aka san shi a Kano kafin ya rasu a cikin 1984. Jin sunan baban Nura zai tabbatar wa mutum da cewa hakar fim ta tara jinsin mutane daban-daban.
Cikakken bayanin
Ba damuwa don na yi aure a kauye - Halima
Halima Adamu Yahya a ranar aurenta
|
IDAN akwai wata 'yar wasan fim wadda batun aurenta ya jawo ka-ce-na-ce da tausayawa, to shahararriyar jaruma Halima Adamu Yahaya ce. Lokacin da ta aure Alhaji Sa'idu Hashim (Malam Wane), wani kansila a Kano, al'amarin ya burge jama'a. To sai kuma auren ya mutu bayan watanni, ta fito da ciki. Wannan kuma ya jawo surutai. To yanzu kuma sai ga shi ta kara yin wani auren a lokacin da ko yaye danta Al-Amin ba ta yi ba. Wannan kuma ya burge mutane sosai, ya nuna cewa lallai dai Halima ba kin yin aure take ba.
Ga labarin:
Kasimu Yero ya zama Sarki
A RANAR Asabar, 8 ga Yuni, 2002 aka nada shahararren dan wasan kwaikwayo din nan Alhaji Kasimu Yero a matsayin sarkin dukkan masu finafinan Hausa na Nijeriya. An yi masa nadin ne a lokacin da ake bikin bai wa wasu shahararru kuma tsofaffin masu wasan kwaikwayo na Arewa lambobin yabo na musamman bisa la'akari da dimbin gudunmawar da suka bayar ga wannan harka. Alhaji Yusuf Ladan, Dan Iyan Zazzau kuma Hakimin Kabala, Kaduna, shi ne ya yi nadin a gaban dimbin jama'a.
Cikakken Labari
Wulakanci a bikin Abida!
Ba kowa ba ne yake kaunar ABIDA MOHAMMED ba. Musamman ma dai 'yan kallon finafinan Hausa, inda jarumar ta yi tashe, kuma ta kasance Jarumar Jarumai Mata (Best Actress) ta shekarar 2001 saboda iya wasanta. Masu kallo da yawa suna kallonta a matsayin yarinya mai wulakanta maziyartanta, su kuma wadanda ba su zo Kano wurinta ba ko suka gan ta a wani garin, sun rika mayen son su gan ta a fili. Duk da haka, akwai wadanda suka gan ta din, amma ba su ga wani wulakanci tare da ita ba. To amma in dai suna ne, Abida ta yi, ya Allah mai kauri ne ko mai kanshi.
Amarya Abida: Ta jefar da kwallon mangwaro...
|
Masoyanta da dama sun dauka abokan ango da kawayen amarya za su yi amfani da shagalin aurenta su gyara mata tarihi, ta fuskar gayyatar masoya da kyautata wa mutanen da suka zo wurin daurin auren ko suka halarci walimar da aka shirya don taya ma'auratan murna. Sai dai kash! tarihin da suka sa Abida ta bari a Film Industry, ba ya da dadi. Tun kafin a daura auren, an shirya cewa a tabbatar an hana yawaitar mutane. Wata majiya ta zayyana wa mujallar Fim shirin da aka yi a boye na a hana mutane yin yawa a wurin daurin auren, kuma a zabe wadanda za a yarda su shiga zauren walimar auren wadda aka yi a otal din Ni'ima da ke Kano.
Cikakken Labari | |
|
Gidauniyar Balaraba:Ana so masoyanta su ba da taimako
SHUGABAN Gidauniyar Tunawa da Balaraba Mohammed, Malam Ishaq Sidi Ishaq, ya yi kira ga daukacin masoyan marigayiyar 'yar wasan da su ba da duk taimakon da za su iya bayarwa ga asusun da aka bude na agaza wa magadanta. Ya ce yin haka yana da muhimmanci domin zaiu nuna cewa an gamsu da gudunmawar da ta bayar ga ci-gaban harkar wasan kwaikwayo na Hausa da ake yayi a yanzu.
Ishaq, wanda shahararren darakta ne kuma dan wasan fim, ya bayyana haka ne a karshen taron musamman da 'yan Kwamitin Gidauniyuar suika yi a Kano kwanan nan. An kira taron ne don ci gaba da tattauna yiwuwar yin babban taron kaddamarwa na Gidauniyar, wanda a da aka niyyar yi a farkon wannan watan na Yuli. To amma saboda wasu matsaloli sai aka yanke shawarar a sanar da jama'a batun gidauniyar kurum ta kafafen yada labarai, tare da fatan duk mai iyawa ya ba da abin da zai bayar a matsayin sadakatul jariya.
Ishaq ya yi bayanin cewa duk abin da aka tara za a damka shi ne ga magadan marigayiyar a matsayin sadaka, kamar yadda aka taba yi wa daraktan nan da ya rasu a hadarin mota kan hanyar Kano zuwa Katsina, Malam Aminu Hassan Yakasai.
Ishaq ya yi nuni da cewa membobin Kwamitin Gidauniyar mutane ne masu gaskiya da rikon amana, kuma sanannu a wannan harka, don haka yana mai tabbatar da cewa sun dauki wannan aiki ne a kan amana da kuma sadaukarwa.
ZA KA IYA BA DA SADAKARKA TA HANNUN WADANNAN MUTANEN:
'Yan Kwamitin Gidauniyar Tunawa da Balaraba Mohammed suna sanar da jama'a cewa duk wanda ke son ya bayar da sadaka kamar yadda aka nema, zai iya bayarwa ta hannun membobin Kwamitin da kuma wakilan mujallar Fim a ko'ina a fadin kasar nan. Duk wanda ya ba da wani abu, za a rubuta sunansa da abin da ya bayar, kuma a nan gaba za a buga sunayen dukkan wadanda suka ba da taimako a cikin mujallun da ke ba da labaran harkar fim ta Hausa, ciki har da mujallar Fim. Ga sunayen 'yan Kwamitin:
Malam Ishaq Sidi Ishaq - Shugaba
M. Ashafa Murnair Barkiya - Editan mujallar Fim
Hajiya Balaraba Ramat Yakubu - Furodusa/Marubuciya
Malam Ibrahim Sheme - mawallafin mujallar Fim
Malam Hafizu Bello - daraktan finafinai
Hajiya Saratu Gidado - Fitacciyar 'yar wasa
Malam Ahmad S. Alkanawy - Furodusa, 'Iyan-Tama Multimedia'
Malam Bala Makosa Zaria - Editan Nishadi
Alh. Nata'ala Aliyu Zaria - shugaban 'Jari Film Production,' Zaria
Malam Abdurrasheed Moh'd Kankia - Furodusa
Malam Aliyu Abdullahi Gora - Mujallar Fim, Kaduna
Malam Bashr Yahuza Malumfashi - dan sanda a Katsina
Malam Bashir Abusabe - Sokoto
Sanarwa daga Ashafa Murnai Barkiya, Sakatare
BALARABA SAI MUN ZO
Daga Amina Abdulmalik, Marubuciyar littafin RUWAN RAINA
Balaraba ta shirya,
Ana ta biki gayya.
*
Lallenta majajaniya,
Gashin kanta na salkiya.
*
Zanin aurenta sassakiya,
Sakakke zubin koshiya.
*
Har ma ta sako 'yan wuya,
Ga kanbunta mai rawaya.
*
Asalin kakanta ne tun jiya,
Gida ta koma mazaya.
*
Tai kyalli gwanar kwalliya,
Ta yi kawa tana rausaya.
*
Shu'aibu ya yi shirin biya,
Amarya ta sako tsakiya.
*
Ya yi biya cikin magiya,
Ta karba tana godiya.
*
Shu'aibu ba ya zolaya,
Irin ta Ayyuba baban Liya.
*
Ayyuba miji na Munubiya,
Yai kauna ya mommoriya.
*
Daga baya ya tako kaya,
Yai furuci yana mamaya.
*
Gwani na gwanaye sha tambaya,
Kai Ali ya kake zolaya.
*
Danka na fari sha lailaya,
Yau ka ba da shi kan haya.
*
Munubiya tai hushi sankaya,
Angulu ce da ba a miya.
*
To yau tai miji hairiya,
Shi ba kishiya ba haya.
*
Shi furucinsa ba sakaya,
Idan ta haihu madalliya.
*
Dan su a nasu ba bayiya,
Ko Hajiya tana Saudiya.
*
Ci gaban wakar
Ka aiko da tambayoyinka ko sharhinka ga: mujallarfim@yahoo.com
| | | | |