|
|
| BABBAN SHAFI |
|
| MU LEKA MU GANI |
| HIRAR MUSAMMAN |
| Wasiku |
|
| MU LEKA HOLLYWOOD |
| Rahoton Musamman |
|
| Rahoto |
| Malam Zurke |
| RA'AYIN MUJALLAR FIM |
|
| Bukukuwa |
| Sauran Labarai |
| Fitattun Taurari |
| Dangane Da Mu |
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS
|
|
Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet. An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo! A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu. JE KA TA NAN
| |
Je ka 

 
NORTHERN STAR FILMS
KE GABATAR DA
GAGARABADAU
Shiryawa: MUJALLAR Fim
Darakta HAFIZU BELLO
Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.
Labari/Tsarawa: Iro mamman;
Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito
BABU IRINSA!
Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...
Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...
Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...
Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka!
Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka
| |
|
In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
| |
|
| |
|
 Ibro
*Ban tsoron uban kowa!
*Yadda ya mamaye kasuwar finafinai da 'Ibro kaza, Ibro kaza'
*Ya kare kansa kan sukar malamai
*Hira da Kulu Wazirin Ibro
FURODUSOSHI. DARAKTOCI. 'YAN WASA. MAKADA DA MAWAKA. KU FARA SHIRIN BARIN GARI. IBRO YA SHIGO GARI. YA AMSHE KASUWAR. TO FA! YAYA KENAN!
Cikakken labari
Me Fatima Ahmed take ciki bayan an sake ta saboda fim?
Fatima Ahmed
|
A FITOWARMU ta 21 ne muka fara buga labarin wata rigima tsakanin Fatima Ahmed da mijinta, wadda aka tafka a kotu tsawon watanni hudu. Fatima, wadda ta fara fim a lokacin, ta kai kara kan cewa Malam Ahmed ya sake ta, shi kuma ya tsaya a kan cewa bai sake ta ba har ta shiga harkar fim. A karshe dai mijin ya saduda, ya gaji ya rubuta mata takarda saki daya, ya ba ta. Daga lokacin zuwa yau, Fatima ta kara shiga harkar fim tsundum.
Cikakken Labari
Aikin Darakta ba nawa bane Cewar Hamisu Iyan-Tama
Hamisu Iyan-Tama
|
HAMISU LAMIDO IYAN-TAMA yana daga cikin 'yan wasa 'yan kalilan wadanda tauraruwarsu ta ki gushewa: an gan ta da dare, kuma an gan ta da rana, sa'annan an ci gaba da ganinta babu yankewa. Ba mamaki, shi ya sa wasu suke danganta dadewar kwarjininsa da ta jarumin Indiya din nan Amitab Bacchan. Kwanan nan sababbin finafinansa masu suna Buri da kuma Halak suka fito kasuwa. Shi Hamisu tare da wata 'yar wasan wadda ita ma tauraruwarta ba ta dushewa, wato Hauwa Ali Dodo (Biba), su ne jaruman fim din Buri. Fim ne wanda ya burge masu kallo. Za ma a iya cewa tun da kamfanin 'Iyan-Tama Multimedia' suke yin fim, ba su taba yin mai ma'ana da kuma cin kudi irin Buri ba. Manta da abin da aka ce game da Hakuri ko Fallasa, shi Buri ajinsa daban yake. Kafin fitowar fim din, Alhaji Hamisu, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Arewa, ya zanta da wakilinmu a Kaduna, Aliyu Abdullahi Gora II, kamar haka:
Ga cikakkiyar hirar
Malamai sun ragargaji harkar fim
Manyan bakin taron Nazarin Hausa
|
Mahalarta taro a Cibiyar Nazarin Hausa ta Jami'ar Danfodiyo sun kayar da harkar fim da rubuta littattafai rigingine sun yanka ta sun fede. Me suka gani a cikinta? Wakilinmu ya halarci taron na kwana biyu kuma ya aiko mana da cikakken rahoto.
Cikakken bayanin
Mahaifin Maryam Umar Aliyu zai kai su Abida kotu
Maryam Umar Aliyu
|
WANI attajiri dan kasuwa dan asalin kasar Nijar mazaunin Katsina, Alhaji Umaru Aliyu, ya bara kan bilinbituwar da 'yarsa yarinyar nan Maryam ta shiga. Ya zargi wasu fitattun 'yan fim da ke Kano da cewa su ne suka hure mata kunne suka gudu da ita, sa'annan kuma suka cusa ta cikin sana'ar fim.
Ga labarin:
An daura auren A'isha Musa da Ali Nayara
A'isha Musa da Angonta Ali Nayara
|
Rashin amincewar iyaye da 'yan uwa, ko rade-radi, bai hana tauraruwar Kaduna auren rabin ranta Ali Nayara ba.
Cikakken Labari
Daren farko: Yau da kallo, gobe da labari
A lokacin daukar shirin Daren Farko
|
'Yan fim sun ji dadin yadda aka shirya fim din mujallar Fim na biyu, har wasu na cewa 'Allah-ya-maimaita-mana!'
Cikakken Labari | |
|
Gidauniyar Balaraba:Ana so masoyanta su ba da taimako
SHUGABAN Gidauniyar Tunawa da Balaraba Mohammed, Malam Ishaq Sidi Ishaq, ya yi kira ga daukacin masoyan marigayiyar 'yar wasan da su ba da duk taimakon da za su iya bayarwa ga asusun da aka bude na agaza wa magadanta. Ya ce yin haka yana da muhimmanci domin zaiu nuna cewa an gamsu da gudunmawar da ta bayar ga ci-gaban harkar wasan kwaikwayo na Hausa da ake yayi a yanzu.
Ishaq, wanda shahararren darakta ne kuma dan wasan fim, ya bayyana haka ne a karshen taron musamman da 'yan Kwamitin Gidauniyuar suika yi a Kano kwanan nan. An kira taron ne don ci gaba da tattauna yiwuwar yin babban taron kaddamarwa na Gidauniyar, wanda a da aka niyyar yi a farkon wannan watan na Agusta. To amma saboda wasu matsaloli sai aka yanke shawarar a sanar da jama'a batun gidauniyar kurum ta kafafen yada labarai, tare da fatan duk mai iyawa ya ba da abin da zai bayar a matsayin sadakatul jariya.
Ishaq ya yi bayanin cewa duk abin da aka tara za a damka shi ne ga magadan marigayiyar a matsayin sadaka, kamar yadda aka taba yi wa daraktan nan da ya rasu a hadarin mota kan hanyar Kano zuwa Katsina, Malam Aminu Hassan Yakasai.
Ishaq ya yi nuni da cewa membobin Kwamitin Gidauniyar mutane ne masu gaskiya da rikon amana, kuma sanannu a wannan harka, don haka yana mai tabbatar da cewa sun dauki wannan aiki ne a kan amana da kuma sadaukarwa.
ZA KA IYA BA DA SADAKARKA TA HANNUN WADANNAN MUTANEN:
'Yan Kwamitin Gidauniyar Tunawa da Balaraba Mohammed suna sanar da jama'a cewa duk wanda ke son ya bayar da sadaka kamar yadda aka nema, zai iya bayarwa ta hannun membobin Kwamitin da kuma wakilan mujallar Fim a ko'ina a fadin kasar nan. Duk wanda ya ba da wani abu, za a rubuta sunansa da abin da ya bayar, kuma a nan gaba za a buga sunayen dukkan wadanda suka ba da taimako a cikin mujallun da ke ba da labaran harkar fim ta Hausa, ciki har da mujallar Fim. Ga sunayen 'yan Kwamitin:
Malam Ishaq Sidi Ishaq - Shugaba
M. Ashafa Murnair Barkiya - Editan mujallar Fim
Hajiya Balaraba Ramat Yakubu - Furodusa/Marubuciya
Malam Ibrahim Sheme - mawallafin mujallar Fim
Malam Hafizu Bello - daraktan finafinai
Hajiya Saratu Gidado - Fitacciyar 'yar wasa
Malam Ahmad S. Alkanawy - Furodusa, 'Iyan-Tama Multimedia'
Malam Bala Makosa Zaria - Editan Nishadi
Alh. Nata'ala Aliyu Zaria - shugaban 'Jari Film Production,' Zaria
Malam Abdurrasheed Moh'd Kankia - Furodusa
Malam Aliyu Abdullahi Gora - Mujallar Fim, Kaduna
Malam Bashr Yahuza Malumfashi - dan sanda a Katsina
Malam Bashir Abusabe - Sokoto
Sanarwa daga Ashafa Murnai Barkiya, Sakatare
BALARABA SAI MUN ZO
Daga Amina Abdulmalik, Marubuciyar littafin RUWAN RAINA
Balaraba ta shirya,
Ana ta biki gayya.
*
Lallenta majajaniya,
Gashin kanta na salkiya.
*
Zanin aurenta sassakiya,
Sakakke zubin koshiya.
*
Har ma ta sako 'yan wuya,
Ga kanbunta mai rawaya.
*
Asalin kakanta ne tun jiya,
Gida ta koma mazaya.
*
Tai kyalli gwanar kwalliya,
Ta yi kawa tana rausaya.
*
Shu'aibu ya yi shirin biya,
Amarya ta sako tsakiya.
*
Ya yi biya cikin magiya,
Ta karba tana godiya.
*
Shu'aibu ba ya zolaya,
Irin ta Ayyuba baban Liya.
*
Ayyuba miji na Munubiya,
Yai kauna ya mommoriya.
*
Daga baya ya tako kaya,
Yai furuci yana mamaya.
*
Gwani na gwanaye sha tambaya,
Kai Ali ya kake zolaya.
*
Danka na fari sha lailaya,
Yau ka ba da shi kan haya.
*
Munubiya tai hushi sankaya,
Angulu ce da ba a miya.
*
To yau tai miji hairiya,
Shi ba kishiya ba haya.
*
Shi furucinsa ba sakaya,
Idan ta haihu madalliya.
*
Dan su a nasu ba bayiya,
Ko Hajiya tana Saudiya.
*
Ci gaban wakar
Ka aiko da tambayoyinka ko sharhinka ga: mujallarfim@yahoo.com
| | | | |