Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa    Bangon mujallar Fim kenan ta watan Oktoba
FITOWA TA 34  Oktoba 2002              ISSN:1595-7780


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
HIRAR MUSAMMAN
Wasiku
KU TAMBAYE SU
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
RA'AYIN MUJALLAR FIM
Ra'ayi Ba Gaba Bane
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka
Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Fati Baffa Fagge

Yarinya mai fasali
*'Yar ina ce?
*Ta taba aure?
Ya aka yi ta shiga MASHI?

Jarumar shirin Mashi da Rawani ta ce ba ta jin za ta dade a harkar fim ba ta yi aure ba

Cikakken labari




Ni Al-Amin zai aura ba Wasila ba


-A'isha B. Umar

A'isha
A'isha B. Umar: Sabuwar tauraruwar Kaduna

BA kowace soyayya ba ce ake labarinta a fagen shirin fim irin wadda ke tsakanin darakta Al-Amin Ciroma da jarumar shirin Daren Farko, A'isha B. Umar. Wadannan 'yan fim su biyu sun sha tayar da muhawara a cikin fagen shirin fim na Kaduna, ba domin komai ba kuwa sai domin irin bayyananniyar sadaukarwarsu ga kaunar da ake ganin suna yi wa juna. A kullum tare suke, kuma duk inda ka ga zara, to babu shakka za ka ga wata.

Cikakken Labari




Ya aka yi Ciroki ya lafa?

An daina yayin Ciroki...Amma shi bai damu ba.

Ciroki
Bashir Bala (Ciroki)

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'una! Yanzu wai sai a yi fim babu Ciroki a ciki, kuma babu wanda zai lura! Duniya kenan! Sai da ta kai hatta Abida ta fi Ciroki tasiri a fim. Yanzu kuma yayin Ibro ake yi. Shin ina Ciroki? Me ya sa aka rage jin duriyarsa?

Ga cikakkiyar hirar



Dalilin shigata harkar fim

Cewar Laila Dogonyaro

Hajiya Laila
Hajiya Laila Dogonyaro
SUNAN Hajiya Laila Dogonyaro ba bako ba ne ga jama'ar kasar nan. Ta yi fice a siyasar Nijeriya tun zamanin Jamhuriya ta Farko, musamman a kan gwagwarmayar nema wa mata hakkinsu a kasar da maza ne suka mamaye komai. Hajiya Laila tana a sahun gaba a kan wannan aiki, ya-Allah karkashin mulkin soja ne ko na farar hula. Bugu da kari, kusan in ban da 'ya'yan sarkin Daura, babu macen da aka nada sarauta a kasar Hausa a wannan zamani, sai fa ita. Ita ce Garkuwar Garki. Shin me sa Hajiya Laila ta shigo harkar shirya fim? Wane buri take son ta cimmawa? Kuma menene ra'ayinta a kan ita kanta harkar fim da kuma su kansu masu shirya finafinan?

Cikakkiyar hirar



Adamu Halilu ya rasu

Marigayi
Marigayi Adamu Halilu, tshon Darakta

ALLAHU Akbar! Da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Lahadi, 1 da Satumba 2002 ne Allah cikin ikonsa ya yi wa shahararren daraktan nan Alhaji Adamu Halilin rasuwa. Ya rasu a gidansa da ke lamba 19, Kagoro Close, Sabon Garin Tudun Wada, Kaduna, bayan wata jinya mai tsawo da ya yi fama da ita. Marigayin, wanda muka taba yi wa lakabi da "baban daraktocin finafinai" a fitowarmu ta watan Agusta, 2000, ba bako ba ne ga makarantanmu, musamman 'yan fim na da da na yanzun.

Ga labarin:



Yadda Idris Danzariya ya zama sabon shugaban masu sayar da kaset

Idris
Idris Danzariya

RUWAN da aka rika zukawa tun da misalin karfe 7:00 na safe har zuwa 9:30 bai hana dimbin 'ya'yan kungiyar masu sayar da kaset na bidiyo da rikoda na Jihar Kano zuwa wurin zaben sababbin shugabanninsu ba. Ana dauke ruwan, jama'a kamar jira suke yi, sai suka rika yin tururuwa suna nufa gidan sinima na Oriya da ke bakin Kasuwar Kofar Wambai inda a can ne aka gudamar da wannan zabe a ranar Lahadi, 8 ga Satumba, 2002.

Cikakken Labari



Yadda nake waka da muryar Ibro

Sadi Sidi
Sadi Sidi Sharifai

SADI Sidi Sharifai yana daga cikin fasihan mawakan finafinan Hausa. Sunansa ya kasance ruwan-dare-game-duniya. In dai za a lissafa mawaka biyu ko uku, to Sadi, wanda akan kira da sunan Sharu, yana cikinsu.

Cikakkiyar hirar


 
  Gidauniyar Balaraba:

Ana so masoyanta su ba da taimako

Marigayiya Balaraba

SHUGABAN Gidauniyar Tunawa da Balaraba Mohammed, Malam Ishaq Sidi Ishaq, ya yi kira ga daukacin masoyan marigayiyar 'yar wasan da su ba da duk taimakon da za su iya bayarwa ga asusun da aka bude na agaza wa magadanta. Ya ce yin haka yana da muhimmanci domin zaiu nuna cewa an gamsu da gudunmawar da ta bayar ga ci-gaban harkar wasan kwaikwayo na Hausa da ake yayi a yanzu.

Ishaq, wanda shahararren darakta ne kuma dan wasan fim, ya bayyana haka ne a karshen taron musamman da 'yan Kwamitin Gidauniyuar suika yi a Kano kwanan nan. An kira taron ne don ci gaba da tattauna yiwuwar yin babban taron kaddamarwa na Gidauniyar, wanda a da aka niyyar yi a farkon wannan watan na Agusta. To amma saboda wasu matsaloli sai aka yanke shawarar a sanar da jama'a batun gidauniyar kurum ta kafafen yada labarai, tare da fatan duk mai iyawa ya ba da abin da zai bayar a matsayin sadakatul jariya.

Ishaq ya yi bayanin cewa duk abin da aka tara za a damka shi ne ga magadan marigayiyar a matsayin sadaka, kamar yadda aka taba yi wa daraktan nan da ya rasu a hadarin mota kan hanyar Kano zuwa Katsina, Malam Aminu Hassan Yakasai.

Ishaq ya yi nuni da cewa membobin Kwamitin Gidauniyar mutane ne masu gaskiya da rikon amana, kuma sanannu a wannan harka, don haka yana mai tabbatar da cewa sun dauki wannan aiki ne a kan amana da kuma sadaukarwa.

ZA KA IYA BA DA SADAKARKA TA HANNUN WADANNAN MUTANEN:

'Yan Kwamitin Gidauniyar Tunawa da Balaraba Mohammed suna sanar da jama'a cewa duk wanda ke son ya bayar da sadaka kamar yadda aka nema, zai iya bayarwa ta hannun membobin Kwamitin da kuma wakilan mujallar Fim a ko'ina a fadin kasar nan. Duk wanda ya ba da wani abu, za a rubuta sunansa da abin da ya bayar, kuma a nan gaba za a buga sunayen dukkan wadanda suka ba da taimako a cikin mujallun da ke ba da labaran harkar fim ta Hausa, ciki har da mujallar Fim. Ga sunayen 'yan Kwamitin:

Malam Ishaq Sidi Ishaq - Shugaba

M. Ashafa Murnair Barkiya - Editan mujallar Fim

Hajiya Balaraba Ramat Yakubu - Furodusa/Marubuciya

Malam Ibrahim Sheme - mawallafin mujallar Fim

Malam Hafizu Bello - daraktan finafinai

Hajiya Saratu Gidado - Fitacciyar 'yar wasa

Malam Ahmad S. Alkanawy - Furodusa, 'Iyan-Tama Multimedia'

Malam Bala Makosa Zaria - Editan Nishadi

Alh. Nata'ala Aliyu Zaria - shugaban 'Jari Film Production,' Zaria

Malam Abdurrasheed Moh'd Kankia - Furodusa

Malam Aliyu Abdullahi Gora - Mujallar Fim, Kaduna

Malam Bashr Yahuza Malumfashi - dan sanda a Katsina

Malam Bashir Abusabe - Sokoto

Sanarwa daga Ashafa Murnai Barkiya, Sakatare


BALARABA SAI MUN ZO
Daga Amina Abdulmalik, Marubuciyar littafin RUWAN RAINA

Balaraba ta shirya,
Ana ta biki gayya.
*
Lallenta majajaniya,
Gashin kanta na salkiya.
*
Zanin aurenta sassakiya,
Sakakke zubin koshiya.
*
Har ma ta sako 'yan wuya,
Ga kanbunta mai rawaya.
*
Asalin kakanta ne tun jiya,
Gida ta koma mazaya.
*
Tai kyalli gwanar kwalliya,
Ta yi kawa tana rausaya.
*
Shu'aibu ya yi shirin biya,
Amarya ta sako tsakiya.
*
Ya yi biya cikin magiya,
Ta karba tana godiya.
*
Shu'aibu ba ya zolaya,
Irin ta Ayyuba baban Liya.
*
Ayyuba miji na Munubiya,
Yai kauna ya mommoriya.
*
Daga baya ya tako kaya,
Yai furuci yana mamaya.
*
Gwani na gwanaye sha tambaya,
Kai Ali ya kake zolaya.
*
Danka na fari sha lailaya,
Yau ka ba da shi kan haya.
*
Munubiya tai hushi sankaya,
Angulu ce da ba a miya.
*
To yau tai miji hairiya,
Shi ba kishiya ba haya.
*
Shi furucinsa ba sakaya,
Idan ta haihu madalliya.
*
Dan su a nasu ba bayiya,
Ko Hajiya tana Saudiya.
* Ci gaban wakar


Ka aiko da tambayoyinka ko sharhinka ga: mujallarfim@yahoo.com