|
|
| BABBAN SHAFI |
|
| MU LEKA MU GANI |
| TALLA |
| Wasiku |
|
| KU TAMBAYE SU |
| Duniyar Finafinai |
|
| Rahoto |
| Malam Zurke |
| Rayuwarmu |
|
| Bukukuwa |
| Sauran Labarai |
| Fitattun Taurari |
| Dangane Da Mu |
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS
|
|
Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet. An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo! A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu. JE KA TA NAN
| |
Je ka





 
SABON FIM MAI FITOWA!! Daga Mujallar FIM
 KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
NORTHERN STAR FILMS
KE GABATAR DA
GAGARABADAU
Shiryawa: MUJALLAR Fim
Darakta HAFIZU BELLO
Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.
Labari/Tsarawa: Iro mamman;
Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito
BABU IRINSA!
Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...
Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...
Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...
Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka!
Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka
| |
|
In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
| |
|
| |
|
 Nakwango, Alasan Kwalle da S. Bello
Sun tsallake rijiya da baya a Nijar
A RANAR Jumma'a, 4 ga Oktoba, 2002, wadansu 'yan wasan fim daga Kano suka yi shiri don zuwa daurin auren kanen abokin jarumi Kabiru Nakwango a garin Tasawa cikin Jamhuriyar Nijar. Suna cikin motar Nakwango kirar Santana su biyar: Nakwango da ke jan motar, sai Alasan Kwalle, da gwanin yin kwalliya a fim Shehu S. Bello, da wani mutum mai suna Alhaji Lawan wanda ba dan fim ba ne, da kuma wani mai suna Sha'aibu da suka dauka don ya nuna masu hanya.
Kamar yadda Alasan Kwalle ya shaida wa Fim, "Muna cikin tafiya, mun kusa kai garin Matamai, cikin wani daji mai suna Tsamiya-Biyu, sai tayar mota ta baya ta fashe. Ko kafin Kabiru Nakwango ya samu ya tsayar da mota har daya tayar gaba ta sace."
Cikakken labari
Wasila ta yi aure a boye
Me ya sa?
Amarya Wasila tare da mata 'yan biki
|
Wasila Isma'il Ibrahim ta yi aure a yayin da surutu ya turnuke a kan yadda aka yi auren da makomarsa.
Cikakken Labari
Ibro zai yi karar 'yan hisba a kan sun doke shi?
Ashek Malam Ibro: An ce wai zai kai maganar kotu
|
Dakarun tabbatar da shari'a sun gwaggwabji dan wasan da ya ce bai tsoro uban kowa. Shin sun kyauta kuwa? Kuma wane mataki zai dauka?
Ga cikakken labarin
Soke-soke ba za su hana aurenmu ba
Cewar Misbahu Ahmad da Rukayya Dawayya
Rukayya da Misbahu a shirin DAWAYYA
| GARBA Supa ne yake cewa abu kamar wasa, karamar magana ta zama babba. Batun soyayyar shahararrun jarumai Misbahu M. Ahmad da Hajiya Rukayya Umar Santa ya soma ne kamar wasa, ko ma a ce wasan, to amma yanzu ya zama babbar magana, domin kuwa bayan Sallah ne za a daura masu aure!
Cikakken labarin
Hira da Baballe Hayatu
Baballe tare da Hadiza Kabara
|
BABALLE Hayatu yana daga cikin matasan 'yan wasa wadanda tauraruwarsu ke haske yanzu a fagen shirin fim a Kano. Tun daga fitowarsa ta farko a cikin Abin Sirri Ne a cikin 1996 ana ta damawa da shi a fagen shirin fim. Ya fito a finafinai sun fi gaban a kirga su. Kadan daga cikinsu su ne:Furuci, Tawakkali, Mashi, Mujadala, Sakiya, Sakamako, Biyayya, da kuma Murdiya.
Ga cikakkiyar hirar
An fasa auren Ahmed S. Nuhu da Maryam
Maryam Mushaqqa
|
WANI labari da muka samu da dumi-duminsa ya nuna cewa danyar soyayyar nan tsakanin Ahmad S. Nuhu da Maryam Aliyu (Mushaqqa) yanzu ta kare. Majiya mai tushe ta tabbatar mana da cewa Ahmed ya fasa auren Ba'abziniyar yarinyar bayan an dade ana ce-ce-ku-ce da zarge-zarge. Yayin da wasu 'yan fim suke zargin Ali Nuhu da kawo karshen soyayyar, wani abokinsa na kut da kut ya ce, "Ba ruwan Ali. Ahmed ne da kansa ya janye."
Cikakken Labari
Ana so 'yan fim su yi aiki da hukunce-hukuncen Musulunci
A WANI kwarya-kwaryan taro na wuni daya da aka gudanar don isar da sako da kuma jawo kan wasu fannonin fadakarwa da Musulmi ke da su, an bukaci masu shirin fim da su karkatar da akalar fadakarwarsu daga tsayawa kan batun aure da soyayya zuwa neman ilimin addini da na zamani, kishin kai da kuma kawo karshen matsalar cin amana musamman a cikin Hausawa Musulmi.
Cikakken labarin | |
|
Gidauniyar Balaraba:Ana so masoyanta su ba da taimako
SHUGABAN Gidauniyar Tunawa da Balaraba Mohammed, Malam Ishaq Sidi Ishaq, ya yi kira ga daukacin masoyan marigayiyar 'yar wasan da su ba da duk taimakon da za su iya bayarwa ga asusun da aka bude na agaza wa magadanta. Ya ce yin haka yana da muhimmanci domin zaiu nuna cewa an gamsu da gudunmawar da ta bayar ga ci-gaban harkar wasan kwaikwayo na Hausa da ake yayi a yanzu.
Ishaq, wanda shahararren darakta ne kuma dan wasan fim, ya bayyana haka ne a karshen taron musamman da 'yan Kwamitin Gidauniyuar suika yi a Kano kwanan nan. An kira taron ne don ci gaba da tattauna yiwuwar yin babban taron kaddamarwa na Gidauniyar, wanda a da aka niyyar yi a farkon wannan watan na Agusta. To amma saboda wasu matsaloli sai aka yanke shawarar a sanar da jama'a batun gidauniyar kurum ta kafafen yada labarai, tare da fatan duk mai iyawa ya ba da abin da zai bayar a matsayin sadakatul jariya.
Ishaq ya yi bayanin cewa duk abin da aka tara za a damka shi ne ga magadan marigayiyar a matsayin sadaka, kamar yadda aka taba yi wa daraktan nan da ya rasu a hadarin mota kan hanyar Kano zuwa Katsina, Malam Aminu Hassan Yakasai.
Ishaq ya yi nuni da cewa membobin Kwamitin Gidauniyar mutane ne masu gaskiya da rikon amana, kuma sanannu a wannan harka, don haka yana mai tabbatar da cewa sun dauki wannan aiki ne a kan amana da kuma sadaukarwa.
ZA KA IYA BA DA SADAKARKA TA HANNUN WADANNAN MUTANEN:
'Yan Kwamitin Gidauniyar Tunawa da Balaraba Mohammed suna sanar da jama'a cewa duk wanda ke son ya bayar da sadaka kamar yadda aka nema, zai iya bayarwa ta hannun membobin Kwamitin da kuma wakilan mujallar Fim a ko'ina a fadin kasar nan. Duk wanda ya ba da wani abu, za a rubuta sunansa da abin da ya bayar, kuma a nan gaba za a buga sunayen dukkan wadanda suka ba da taimako a cikin mujallun da ke ba da labaran harkar fim ta Hausa, ciki har da mujallar Fim. Ga sunayen 'yan Kwamitin:
Malam Ishaq Sidi Ishaq - Shugaba
M. Ashafa Murnair Barkiya - Editan mujallar Fim
Hajiya Balaraba Ramat Yakubu - Furodusa/Marubuciya
Malam Ibrahim Sheme - mawallafin mujallar Fim
Malam Hafizu Bello - daraktan finafinai
Hajiya Saratu Gidado - Fitacciyar 'yar wasa
Malam Ahmad S. Alkanawy - Furodusa, 'Iyan-Tama Multimedia'
Malam Bala Makosa Zaria - Editan Nishadi
Alh. Nata'ala Aliyu Zaria - shugaban 'Jari Film Production,' Zaria
Malam Abdurrasheed Moh'd Kankia - Furodusa
Malam Aliyu Abdullahi Gora - Mujallar Fim, Kaduna
Malam Bashr Yahuza Malumfashi - dan sanda a Katsina
Malam Bashir Abusabe - Sokoto
Sanarwa daga Ashafa Murnai Barkiya, Sakatare
BALARABA SAI MUN ZO
Daga Amina Abdulmalik, Marubuciyar littafin RUWAN RAINA
Balaraba ta shirya,
Ana ta biki gayya.
*
Lallenta majajaniya,
Gashin kanta na salkiya.
*
Zanin aurenta sassakiya,
Sakakke zubin koshiya.
*
Har ma ta sako 'yan wuya,
Ga kanbunta mai rawaya.
*
Asalin kakanta ne tun jiya,
Gida ta koma mazaya.
*
Tai kyalli gwanar kwalliya,
Ta yi kawa tana rausaya.
*
Shu'aibu ya yi shirin biya,
Amarya ta sako tsakiya.
*
Ya yi biya cikin magiya,
Ta karba tana godiya.
*
Shu'aibu ba ya zolaya,
Irin ta Ayyuba baban Liya.
*
Ayyuba miji na Munubiya,
Yai kauna ya mommoriya.
*
Daga baya ya tako kaya,
Yai furuci yana mamaya.
*
Gwani na gwanaye sha tambaya,
Kai Ali ya kake zolaya.
*
Danka na fari sha lailaya,
Yau ka ba da shi kan haya.
*
Munubiya tai hushi sankaya,
Angulu ce da ba a miya.
*
To yau tai miji hairiya,
Shi ba kishiya ba haya.
*
Shi furucinsa ba sakaya,
Idan ta haihu madalliya.
*
Dan su a nasu ba bayiya,
Ko Hajiya tana Saudiya.
*
Ci gaban wakar
Ka aiko da tambayoyinka ko sharhinka ga: mujallarfim@yahoo.com
| | | | |