|
|
| BABBAN SHAFI |
|
| GASKIYA DAYA CE |
| FADI SONKA |
| Wasiku |
|
| NEMAN MAFITA |
| DUNIYAR FINAFINAI |
|
| RAHOTO |
| Malam Zurke |
| RA'YIN FIM |
|
| Bukukuwa |
| Sauran Labarai |
| SABUWAR FUSKA |
| Dangane Da Mu |
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS
|
|
Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet. An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo! A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu. JE KA TA NAN
| |
Je ka






 
SABON FIM MAI FITOWA!! Daga Mujallar FIM
 KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
NORTHERN STAR FILMS
KE GABATAR DA
GAGARABADAU
Shiryawa: MUJALLAR Fim
Darakta HAFIZU BELLO
Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.
Labari/Tsarawa: Iro mamman;
Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito
BABU IRINSA!
Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da tunanin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: Wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...
Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...
Labari ne na soyayya, ban dariya, ta da jijiyar wuya, da ban tsoro...
Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka!
Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka
| |
|
In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
| |
|
| |
|
 Babu maganar aure kuma
Suleiman Sa'eed ne ya rusa soyayyarmu -Misbahu
Ban damu ba don mun rabu da Misbahu -Rukayya
Jarumi Misbahu M. Ahmad ya bayyana rushewar soyayyarsa da Rukayya Umar Santa a bisa zargin tana yin soyayya biyu; ya dora laifin a kan darakta Suleiman Sa'eed
Cikakken labari
Ba mu haihu a asirce ba!
-Al-AMIN DA A'ISHA B. UMAR
Al-Amin da masoyiyarsa A'isha
|
AL-AMIN CIROMA da A'ISHA B. UMAR (AMANI) sun karyata zargin da wasu ke yi cewa wai masoyan biyu sun haifi da a asirce.
Cikakken Labari
Ba don kudi nake yin fim ba
- Zuwaira Karishma
Zuwaira Karishma
|
ZUWAIRA ABDULSALAM RIJIYAR LEMO tana daga cikin fitattun 'yan wasa mata. A Kano take. An fi saninta da sunan Zuwaira Karishma, kuma ta samu wannan lakabin ne saboda iya wasanta, wanda ya sa ake kwatanta ta da jarumar Indiya din nan mai suna Karisma Kapoor.
An haife ta cikin 1981 a Legas, inda iyayenta suka zauna. Amma Bakanuwa ce. "Iyayena a Yakasai suke, amma asalinsu 'yan Karamar Hukumar Gezawa ne," inji ta. A Legas ta yi boko har zuwa sakandare, inda ta kare cikin 1996 a "State High School' da ke Iyana-Ikapaja.
Ga cikakken labarin
Hamza mijin Abida ya watsar da harkar fim ya koma cuwa-cuwa
Saima da Abida yayin wani shirn fim
| Mijin Abida ya dukufa harkar cuwa-cuwar mai don neman abin sawa a bakin salati!
Cikakken labarin
Ali Nuhu zai yi aure a wannan watan!
Ali Nuhu
|
Karshen tika-tika, tik! Shukakkar soyayyar nan da ta dade tsakanin fitaccen jarumi kuma furodusa, Ali Nuhu, da rabin ransa Maimuna Mohammed, kakar girbinta ta yi. Yanzu haka an kammala duk wasu shirye-shiryen yin auren, an kuma sa ranar daurin auren, wato ranar Asabar 15 ga wannan watan na Maris, 2003. A Zariya za a daura auren, inda iyayen amaryar suke zaune.
Ga cikakken labarin
M.D. Yusuf zai zama Furodusa
M.D. Yusuf, tsohon Shugaban ACF, kuma Shugaban jam'iyyar MDJ
|
Shugaban Kungiyar Tuntubar Juna ta Arewa ya ce a shirye yake ya agaza wa harkar fim na Hausa. Kuma ya ce ba rwan siyasarsa da wannan sabon yunkurin nasa.
Cikakken Labari
Gasar Finafinai: Aminu Shariff ya kalubalanci Mandawari kan rabon fom na shiga
WATA takaddama ta barke tsakanin wani fitaccen darakta kuma furodusa da shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Mohammed Mandawari. Furodusan, Malam Aminu Shariff Hassan, ya fito ne karara ya bayyana rashin gamsuwa kan yadda aka raba fom fom na shiga wata gasar finafinan Hausa.
Cikakken labarin
Finafinaina 12 da na fi so
Sani Musa Danja
|
Fitaccen jarumi SANI MUSA DANJA ya waiwaya baya tare da gaya mana manyan finafinansa guda goma sha biyu. Wadanne finafinai ne kuwa?
Cikakken Labari | |
|
O, wai har an shekara dayaAMMA DAI BA MU MANTA DA KE BA
Allah ya jikanki, ya sa kin huta. -Daga masoyanki, abokanki ma'aikatan mujallar FIM da kuma masu karatun mujallar
Gidauniyar Balaraba:Ana so masoyanta su ba da taimako
SHUGABAN Gidauniyar Tunawa da Balaraba Mohammed, Malam Ishaq Sidi Ishaq, ya yi kira ga daukacin masoyan marigayiyar 'yar wasan da su ba da duk taimakon da za su iya bayarwa ga asusun da aka bude na agaza wa magadanta. Ya ce yin haka yana da muhimmanci domin zaiu nuna cewa an gamsu da gudunmawar da ta bayar ga ci-gaban harkar wasan kwaikwayo na Hausa da ake yayi a yanzu.
Ishaq, wanda shahararren darakta ne kuma dan wasan fim, ya bayyana haka ne a karshen taron musamman da 'yan Kwamitin Gidauniyuar suika yi a Kano kwanan nan. An kira taron ne don ci gaba da tattauna yiwuwar yin babban taron kaddamarwa na Gidauniyar, wanda a da aka niyyar yi a farkon wannan watan na Agusta. To amma saboda wasu matsaloli sai aka yanke shawarar a sanar da jama'a batun gidauniyar kurum ta kafafen yada labarai, tare da fatan duk mai iyawa ya ba da abin da zai bayar a matsayin sadakatul jariya.
Ishaq ya yi bayanin cewa duk abin da aka tara za a damka shi ne ga magadan marigayiyar a matsayin sadaka, kamar yadda aka taba yi wa daraktan nan da ya rasu a hadarin mota kan hanyar Kano zuwa Katsina, Malam Aminu Hassan Yakasai.
Ishaq ya yi nuni da cewa membobin Kwamitin Gidauniyar mutane ne masu gaskiya da rikon amana, kuma sanannu a wannan harka, don haka yana mai tabbatar da cewa sun dauki wannan aiki ne a kan amana da kuma sadaukarwa.
ZA KA IYA BA DA SADAKARKA TA HANNUN WADANNAN MUTANEN:
'Yan Kwamitin Gidauniyar Tunawa da Balaraba Mohammed suna sanar da jama'a cewa duk wanda ke son ya bayar da sadaka kamar yadda aka nema, zai iya bayarwa ta hannun membobin Kwamitin da kuma wakilan mujallar Fim a ko'ina a fadin kasar nan. Duk wanda ya ba da wani abu, za a rubuta sunansa da abin da ya bayar, kuma a nan gaba za a buga sunayen dukkan wadanda suka ba da taimako a cikin mujallun da ke ba da labaran harkar fim ta Hausa, ciki har da mujallar Fim. Ga sunayen 'yan Kwamitin:
Malam Ishaq Sidi Ishaq - Shugaba
M. Ashafa Murnair Barkiya - Editan mujallar Fim
Hajiya Balaraba Ramat Yakubu - Furodusa/Marubuciya
Malam Ibrahim Sheme - mawallafin mujallar Fim
Malam Hafizu Bello - daraktan finafinai
Hajiya Saratu Gidado - Fitacciyar 'yar wasa
Malam Ahmad S. Alkanawy - Furodusa, 'Iyan-Tama Multimedia'
Malam Bala Makosa Zaria - Editan Nishadi
Alh. Nata'ala Aliyu Zaria - shugaban 'Jari Film Production,' Zaria
Malam Abdurrasheed Moh'd Kankia - Furodusa
Malam Aliyu Abdullahi Gora - Mujallar Fim, Kaduna
Malam Bashr Yahuza Malumfashi - dan sanda a Katsina
Malam Bashir Abusabe - Sokoto
Sanarwa daga Ashafa Murnai Barkiya, Sakatare
BALARABA SAI MUN ZO
Daga Amina Abdulmalik, Marubuciyar littafin RUWAN RAINA
Balaraba ta shirya,
Ana ta biki gayya.
*
Lallenta majajaniya,
Gashin kanta na salkiya.
*
Zanin aurenta sassakiya,
Sakakke zubin koshiya.
*
Har ma ta sako 'yan wuya,
Ga kanbunta mai rawaya.
*
Asalin kakanta ne tun jiya,
Gida ta koma mazaya.
*
Tai kyalli gwanar kwalliya,
Ta yi kawa tana rausaya.
*
Shu'aibu ya yi shirin biya,
Amarya ta sako tsakiya.
*
Ya yi biya cikin magiya,
Ta karba tana godiya.
*
Shu'aibu ba ya zolaya,
Irin ta Ayyuba baban Liya.
*
Ayyuba miji na Munubiya,
Yai kauna ya mommoriya.
*
Daga baya ya tako kaya,
Yai furuci yana mamaya.
*
Gwani na gwanaye sha tambaya,
Kai Ali ya kake zolaya.
*
Danka na fari sha lailaya,
Yau ka ba da shi kan haya.
*
Munubiya tai hushi sankaya,
Angulu ce da ba a miya.
*
To yau tai miji hairiya,
Shi ba kishiya ba haya.
*
Shi furucinsa ba sakaya,
Idan ta haihu madalliya.
*
Dan su a nasu ba bayiya,
Ko Hajiya tana Saudiya.
*
Ci gaban wakar
Ka aiko da tambayoyinka ko sharhinka ga: mujallarfim@yahoo.com
| | | | |