|
|
| BABBAN SHAFI |
|
| GASKIYA DAYA CE |
| FADI SONKA |
| Wasiku |
|
| TSOKACI |
| DUNIYAR FINAFINAI |
|
| RAHOTO |
| Malam Zurke |
| RA'YIN FIM |
|
| Bukukuwa |
| Sauran Labarai |
| SABUWAR FUSKA |
| Dangane Da Mu |
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS
|
|
Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet. An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo! A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu. JE KA TA NAN
| |
Je ka







 
SABON FIM YA FITO!! Daga Mujallar FIM
 KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
NORTHERN STAR FILMS
KE GABATAR DA
GAGARABADAU
Shiryawa: MUJALLAR Fim
Darakta HAFIZU BELLO
Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.
Labari/Tsarawa: Iro mamman;
Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito
BABU IRINSA!
Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da tunanin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: Wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...
Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...
Labari ne na soyayya, ban dariya, ta da jijiyar wuya, da ban tsoro...
Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka!
Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka
| |
|
In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
| |
|
| |
|
 Abu kamar wasa..
Maryam Mushaqqa ta yi aure!
MARYAM ALIYU, daya daga cikin shahararrun jarumai ta bar fagen shirin fim. Wanda ta aura din dan Nijeriya ne mazaunin kasar Kamaru. 'Yan fim sun sha biki. A'ISHA ABBA AHMED, ABBAS SA'ID KIRU, da SANI MAIKATANGA ma sun halarci bukukuwan, kuma ga rahotonsu. SANI MAIKATANGA ya dauko mana hotunan bikin
Cikakken labari
'Yan '419' sun damfari Furodusa
SABON salon yaudara, cuta da zamba, ba ya kare wa mutane, shi ya sa mutane kan ce, "mai son abinka ya fi ka dabara". Idan ba ku manta ba, can a watannin baya mun ba ku labarin yadda 'yan damfara ('yan '419') suka yaudari Bashir Bala (Ciroki) suka raba shi da Besfarsa a Kano. To ga alama 'yan damfara suna hangen akwai romo a fagen shirin fim na Hausa, domin kuwa kwanan nan sun kutso kai a Zariya cikin Jihar Kaduna.
Cikakken Labari
Auren Misbahu ya yi armashi
Misbahu da amaryarsa suna addu'a
|
AN shafe watanni hudu yanzu tun da wannan mujallar ta ba ku labarin sabanin da ya shiga tsakanin jarumai biyu - Misbahu M. Ahmad da Rukayya Umar Santa (Dawayya). Binciken da muka yi ya nuna cewa Misbahu ya yi soyayya iri-iri- da 'yanmata daban-daban a lokuta daban-daban, kuma a garuruwa daban-daban. Wasu 'yan fim, wasu ba 'yan fim ba. Kowacce kuma da yanayinta. To amma babu soyayyar da ta girgiza jarumin/mawakin/furodusan irin wadda ya yi da Rukayya, jarumar shirin Dawayya. Kun dai san yadda wannan soyayyar ta kare, a cikin ce-ce-ku-ce da zargi da zage-zage.
Ga cikakken labarin
Kalaman Rukayya kan auren Misbahu
Misbahu kenan da Rukayya, a da masoyan juna ne
| LOKACIN da labarin bikin Misbahu ya bullo, mutane da dama sun zuba ido, kuma sun kasa kunne, su ji me fitacciyar jaruma RUKAYYA UMAR SANTA (DAWAYYA), wadda Misbahu ta taba nema da aure amma Allah bai yi ba, za ta yi ko za ta ce. Wasu suna zaton za ta dora kai a gwiwa ne ta yi ta rusa kuka kawai; wasu kuma na ganin ai tunda yarinya ce mai karfin hali, da wuya ne abin ya dame ta. To, wata majiya ta shaida wa Fim cewa labarin ya dan dami Rukayya din, kamar yadda zai iya damun kowace budurwa da saurayinta ya yi aure ya bar ta, to amma sai ta yi tawakkali, ta bar wa Allah komai. Da wata kawarta ta yi mata zancen ma, cewa Rukayya ta yi, "To me zan ce? Ai an ce matar mutum kabarinsa. Don haka ni ba na yin bakin ciki. Ita (Zainab) ce Allah ya kadarto zai aura. Wallahi ba na jin haushi."
Cikakken labarin
'Macutan Daraktoci Sun Cika Industiri Suna Bata Mana Aiki'
SAIFULLAHI Tukur Yola ba mutumin Adamawa ba ne. Mutumin Kano ne, dan unguwar Yola ta cikin Birni. A halin yanzu yana daga cikin matasan daraktocin finafinan Hausa da aka sanya wa ido saboda hangen irin basira da Allah ya yi musu. Akwai finafinai da yawa wadanda wannan hazikin darakta ya shirya wadanda ake jin yin irinsu zai iya sauya akalar finafinanmu na Hausa. Daya daga cikinsu shi ne Hairani, wanda ya fito dauke da labarin rikicin wani gida inda suruka ba ta kaunar matar danta, suka hada kai da matar wan dan nata suka dinga musguna wa yarinyar. Wani fim din na Saifullah shi ne Judah, wanda ake ganin babu shakka sai ya fi Hairani karbuwa da gawurta.
Ga cikakken labarin
H I R A D A F U R O D U S O S H I
Sabuwar furodusa AISHA TIJJANI tana so matan da ke shirya finafinai su hada kansu, kuma su guji hassada, don samun ci gaban junansu.
Ga cikakken labarin
| |
|
O, wai har an shekara dayaAMMA DAI BA MU MANTA DA KE BA
Allah ya jikanki, ya sa kin huta. -Daga masoyanki, abokanki ma'aikatan mujallar FIM da kuma masu karatun mujallar
Gidauniyar Balaraba:Ana so masoyanta su ba da taimako
SHUGABAN Gidauniyar Tunawa da Balaraba Mohammed, Malam Ishaq Sidi Ishaq, ya yi kira ga daukacin masoyan marigayiyar 'yar wasan da su ba da duk taimakon da za su iya bayarwa ga asusun da aka bude na agaza wa magadanta. Ya ce yin haka yana da muhimmanci domin zaiu nuna cewa an gamsu da gudunmawar da ta bayar ga ci-gaban harkar wasan kwaikwayo na Hausa da ake yayi a yanzu.
Ishaq, wanda shahararren darakta ne kuma dan wasan fim, ya bayyana haka ne a karshen taron musamman da 'yan Kwamitin Gidauniyuar suika yi a Kano kwanan nan. An kira taron ne don ci gaba da tattauna yiwuwar yin babban taron kaddamarwa na Gidauniyar, wanda a da aka niyyar yi a farkon wannan watan na Agusta. To amma saboda wasu matsaloli sai aka yanke shawarar a sanar da jama'a batun gidauniyar kurum ta kafafen yada labarai, tare da fatan duk mai iyawa ya ba da abin da zai bayar a matsayin sadakatul jariya.
Ishaq ya yi bayanin cewa duk abin da aka tara za a damka shi ne ga magadan marigayiyar a matsayin sadaka, kamar yadda aka taba yi wa daraktan nan da ya rasu a hadarin mota kan hanyar Kano zuwa Katsina, Malam Aminu Hassan Yakasai.
Ishaq ya yi nuni da cewa membobin Kwamitin Gidauniyar mutane ne masu gaskiya da rikon amana, kuma sanannu a wannan harka, don haka yana mai tabbatar da cewa sun dauki wannan aiki ne a kan amana da kuma sadaukarwa.
ZA KA IYA BA DA SADAKARKA TA HANNUN WADANNAN MUTANEN:
'Yan Kwamitin Gidauniyar Tunawa da Balaraba Mohammed suna sanar da jama'a cewa duk wanda ke son ya bayar da sadaka kamar yadda aka nema, zai iya bayarwa ta hannun membobin Kwamitin da kuma wakilan mujallar Fim a ko'ina a fadin kasar nan. Duk wanda ya ba da wani abu, za a rubuta sunansa da abin da ya bayar, kuma a nan gaba za a buga sunayen dukkan wadanda suka ba da taimako a cikin mujallun da ke ba da labaran harkar fim ta Hausa, ciki har da mujallar Fim. Ga sunayen 'yan Kwamitin:
Malam Ishaq Sidi Ishaq - Shugaba
M. Ashafa Murnair Barkiya - Editan mujallar Fim
Hajiya Balaraba Ramat Yakubu - Furodusa/Marubuciya
Malam Ibrahim Sheme - mawallafin mujallar Fim
Malam Hafizu Bello - daraktan finafinai
Hajiya Saratu Gidado - Fitacciyar 'yar wasa
Malam Ahmad S. Alkanawy - Furodusa, 'Iyan-Tama Multimedia'
Malam Bala Makosa Zaria - Editan Nishadi
Alh. Nata'ala Aliyu Zaria - shugaban 'Jari Film Production,' Zaria
Malam Abdurrasheed Moh'd Kankia - Furodusa
Malam Aliyu Abdullahi Gora - Mujallar Fim, Kaduna
Malam Bashr Yahuza Malumfashi - dan sanda a Katsina
Malam Bashir Abusabe - Sokoto
Sanarwa daga Ashafa Murnai Barkiya, Sakatare
BALARABA SAI MUN ZO
Daga Amina Abdulmalik, Marubuciyar littafin RUWAN RAINA
Balaraba ta shirya,
Ana ta biki gayya.
*
Lallenta majajaniya,
Gashin kanta na salkiya.
*
Zanin aurenta sassakiya,
Sakakke zubin koshiya.
*
Har ma ta sako 'yan wuya,
Ga kanbunta mai rawaya.
*
Asalin kakanta ne tun jiya,
Gida ta koma mazaya.
*
Tai kyalli gwanar kwalliya,
Ta yi kawa tana rausaya.
*
Shu'aibu ya yi shirin biya,
Amarya ta sako tsakiya.
*
Ya yi biya cikin magiya,
Ta karba tana godiya.
*
Shu'aibu ba ya zolaya,
Irin ta Ayyuba baban Liya.
*
Ayyuba miji na Munubiya,
Yai kauna ya mommoriya.
*
Daga baya ya tako kaya,
Yai furuci yana mamaya.
*
Gwani na gwanaye sha tambaya,
Kai Ali ya kake zolaya.
*
Danka na fari sha lailaya,
Yau ka ba da shi kan haya.
*
Munubiya tai hushi sankaya,
Angulu ce da ba a miya.
*
To yau tai miji hairiya,
Shi ba kishiya ba haya.
*
Shi furucinsa ba sakaya,
Idan ta haihu madalliya.
*
Dan su a nasu ba bayiya,
Ko Hajiya tana Saudiya.
*
Ci gaban wakar
Ka aiko da tambayoyinka ko sharhinka ga: mujallarfim@yahoo.com
|
| | | |