Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa    Bangon mujallar Fim kenan ta watan Disamba
FITOWA TA 45  Disamba 2003              ISSN:1595-7780

If you had a new browser, you would be able to view this java applet.

BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
HIRA DA DARAKTOCI
Wasiku
NEMAN MAFITA
SHARHI KAN FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
ADABI
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon FIM TA 44. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 43. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 42. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 41. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 40. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 39. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM YA FITO!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

KASH! Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

'Yan wasa: Farida Jalal, A.A. Shariff (Momo), Kasimu Yero, Bashir Nayaya, Abubakar Yusuf Ladan, Hajara Usman, Sani Idris Moda, Sani Garba S.K, da Rashida Bello.

Darakta: Aminu A. Shariff

BABU IRINSA!

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Fati da Sani lokacin bukinsu
HIRAR MUSAMMAN, Fati Moh'd/ Sani Musa

RAYUWARMU A LONDON
INJI SANI DA FATI

Daga birnin London, Fati Mohammed da Sani Mai Iska sun yi bayani kan ji-ta-ji-tar cewa wai sun rabu, kuma wai Fati za ta auri Bature. Jaruman sun karyata ji-ta-ji-tar, suka ce aurensu na nan daram-dakam

Cikakken labari




Dirama na da asali a Islam

inji Sheikh Karibullah

Sheikh Karibullah
Sheikh Karibullah Nasiru Kabara

SHEIKH KARIBULLAH NASIRU KABARA, Shugaban darikar Tijjaniyya ta Afrika ta Yamma, ya gabatar da wannan jawabin ne a wajen bude taron duniya kan finafinan Hausa wanda Cibiyar Nazarin Al'adun Hausawa, Kano, ta shirya a Kano cikin Agusta 2003

Cikakkiyar hirar




Ba wanda ya isa ya hana harkar fim na Hausa

A cewar HUSSAINI SULE KOKI

Husaini Koki
Husaini Sule Koki

HUSSAINI Sule Koki yana daga cikin 'yan wasan fim din Hausa wadanda Allah ya tarfa wa garinsu nono. Domin kuwa yana cikin ajin gaba na 'yan wasan da suka fi shahara, ake damawa da su, kuma suke cin moriyar harkar. Bayan haka Malam Husaini yana daga cikin dattawan industiri wadanda ake kallonsu a matsayin iyaye abin girmamawa. A yau shekararsa ashirin yana sana'ar wasan kwaikwayo, domin kuwa daga wasan talbijin ne wasan bidiyo ya riske shi, kuma ya rungume shi ake tafiya tare da shi.

Ga cikakken labarin



Mu Guji Abubuwan Zubar Da Mutunci

inji RAHAMA ISA

Rahama Isa
Rahama Isa

RAHAMA Isa tana daga cikin 'yan wasa da shigo harkar fim ba da dadewa ba, wadanda suke kokarin yin suna su ma a san su sosai. A industiri, an fi saninta da sunan Rahma Sirace, saboda rawar da ta taka a fim din "Sirace" na kamfanin Sarauniya Films. Makasudin hirarmu da ita shi ne don mu zanta game da halayyar 'yan matan fim da suka yi fice kuma suke amfani da wannan dama suke wulakanta wadanda ba su yi suna ba. Tana bai wa 'yan'uwanta shawara da su yi koyi da 'yan fim kamar su Fati Mohammed, Abida da marigayiya Balaraba wadda har ta koma ga Ubangiji ana yabonta. Ta ce, "Mu yi koyi da irin wadannnan halayen domin kowa ya karbe mu hannu biyu-biyu, shi ne mutuncinmu, shi ne darajarmu. Wasu matan idan sun karbu sai su rika tinkaho wanda babu kyau".

Cikakken labarin




Usaina: Soyayyar Mijinta Ta Maida Ita Zabiya

Usaina
Usaina

WASU 'yan shekarau kadan da suka wuce, fitaccen daraktan nan da ke Jos, Magaji Mijinyawa, yana zaune a wani falo na furodusa Sani Muhammad Sani, shi kuma furodusan yana cikin uwardaki sa'annan uwargidansa Usaina tana safa da marwa tsakanin kicin da sauran bangaren gidan domin ta ga mijinta da amininsa sun samu maganin yunwa. Tana yi tana rera wakoki daban-daban. Magaji ya kame a kan kujera kamar gunki yana sauraren wakokin. Ya kasa motsawa. Can sai ya yi wuf! ya tashi tsaye ya kwala wa mai gidan kira. Ita kanta Usaina sai da ta tsaya cak! a cikin tafiyarta. Sani ya fito da sauri, ya dauka wani abu ne ya faru.

Ga cikakken labarin




Aminu Moh'd (H.R.B.): Ya Soma Kwatar Muryarsa

Aminu M.HRB
Aminu muhammad (HRB)


Daga wakilinmu a Kano

WANI lokaci, fasihi yakan bullo ne a inda ba ka tsammani ko a lokacin da ba ka tsammani, ko kuma wanda kake zaton bai iya yin abu ashe ya iya. AMINU MOHAMMED, wanda ake kira Aminun H.R.B., ma'aikaci ne a kamfanin shirya fim na 'H.R.B. Enterprises' da ke Kano, wato kamfanin da finafinansa ke tashe a yanzu. Shi ne yake kula da bangaren rikodin na finafinai ko wakoki.

Ga cikakken labarin


 
  Sabuwar Gasar Kacici-Kacici!

WACECE WANNAN?

Wanda ake so a gano ko wanene

Shin ka san ta?
Za ku ci kyaututtukan musamman daga wannan gasar!


A wannan watan kuma ga mu dauke da wata sabuwar gasar ta kacici-kacici mai farin jini.Sai dai sabanin watannin baya.Daga yanzu zamu rika bada kyaututtuka na musamman ga mutane Biyar na farko da suka gane amsar gasar a tsarin gasar (raffle)da za'a rika yi a ofishin mujallar Fim! wannan hoton dake hannun daman ku, na wata yarinya ce lokacin tana kankanuwa (har ta iya zama!)amma yanzu fitacciyar 'yar wasan fim ce. muna son ku rubuto ku gaya mana sunanta.


WANNAN GARABASAR HAR INA!

Kyaututtukan da za mu bayar:



1. Agogon Bango

2.Kwafen Mujallar Fim har na watanni Shida

3.Rediyo Rikoda

4.Kwafe guda Daya na sabon Littafin Ibrahim Sheme,wato 'yartsana

5.Kwalbar Turare na Zamani

Ga satar Amsa!


1.A kano take.

2.Itace jarumar wani fim da aka yi don gargadin jama'a kan wata muguwar cuta.

3.Sun fito kwanan nan tare da Maijidda Ibrahim da Farida Jalal a wani fim.

4.Acikin wannan shekarar ta taba zama yarinyar Bangon mujallar Fim.


Ka aiko da tambayoyinka ko sharhinka ga: mujallarfim@yahoo.com