Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 28   Afrilu 2002


BABBAN SHAFI
Mu Leka Mu Gani
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 1
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 2
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 3
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 4
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 5
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 6
Malam Zurke
Ra'ayin Mujallar Fim
Hajjin Bana
Sauran Labarai
Ra'ayi Ba Gaba ne
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN

 
If you had a new browser, you would be able to view this java applet. Akwai:  


Ango Kumurci ya zayyana yadda rayuwarsa da Balaraba za ta kasance

'Daga aurenmu, Balaraba ta daina wasan fim'

A lokacin daurin aurensa, SHU'AIBU LAWAN KUMURCI bai samu sukunin tsayawa a cikin taron jama'a ba saboda masoyansa sun yawaita. Tilas ta sa aka saka shi cikin dakin wan amarya Balaraba (wato Abdullahi, wanda aka yi hatsarin motar da shi), aka kulle, aka sa sojoji su yi gadin kofar. Amma da yake mujallar Fim ce ta zo, an bude kofar, wakilinmu ya shiga ciki aka rufe su domin su tattauna a kan abin farin cikin da ya samu Shu'aibun. A tattaunawar tasu, Kumurci ya bayyana jin dadinsa, da kuma yadda yake son su yi rayuwar aure tare da kyakkyawar amaryarsa. Ga yadda hirar ta kasance:

Fim: Shu'aibu, ya za ka bayyana farin cikinka kan wannan aure naka da Balaraba?

SHU'AIBU: Gaskiya, ni ba zan iya kwatanta murnar da ta same ni a wannan rana ba saboda farin ciki ba nawa ne ni kadai ba har ma na jama'a; ya zamana ni kaina ma da na zo ban samu sake ba na gaisa da jama'a. (Dariya) Ya zamana ma ni kaina da kyar aka tsamo ni daga cikin jama'a aka ware ni a wani wuri. To kuma wannan duk farin ciki ne da jama'a suke nunawa, bayan ni kuma nawa.

A rayuwarka ka taba jin dadi kamar na yau?

SHU'AIBU: Gaskiya babu wani jin dadi da ya taba kama da irin na yau. Wannan shi ne dadin da ban taba ji ba a rayuwa, kuma shi ne (abin) tarihi. Na yi farin cikin da ban taba yi ba. Ba ni kadai ba, duk mutumin da aka ce zai yi aurensa na farko, matarsa ta farko, ita ma aurenta na farko - to ina ganin wannan ba wanda zai kai shi farin ciki.

Shin ka yi tunanin jama'a za su taru haka?

SHU'AIBU: Gaskiya abin da ya sa mutane suka burge ni (shi ne) ni da kaina ban taba tunanin za su iya baro Kano su zo nan su hallara haka ba, wanda ko da a can Kanon aka yi sai haka. Mutane sun ban mamaki kwarai da gaske. Na ga mutane bila adadin, ban san daga inda suke barkowa ba.

Kana da sako na musamman ga 'yan'uwa da abokan arziki da suka samu damar halartar daurin aurenka?

SHU'AIBU: Abin da nake son in gaya wa 'yan'uwa wadanda suka samu halartar wannan taro, sai tsabar godiya da nake gare su da kuma rokon Allah ya maida su gidajensu lafiya, kuma wadanda ba su yi ba (aure) Allah ya ba su ikon yi.

Ko akwai wani sako zuwa ga iyayen Amarya?

SHU'AIBU: E, sai dai godiya kawai da zan mika gare su.

Wane kira za ka yi ga Amarya? SHU'AIBU: Kiran da zan yi a gare mu, kowa ya riga ya san shi; yau in dai an ce an daura aure sai ai watsi da duk wasu abubuwa, sai a koma ga Allah, da kuma ibada, da rikon amana, da kuma hakuri.

Ya za ka kwatanta yawan jama'ar da ta halarci daurin aurenka da wadda ta halarci auren Fati da Sani Mai Iska?

SHU'AIBU: A gaskiya, mutane sun taru. Ni wannan nawa ban gani ba (saboda ina cikin daki), amma na Sani Mai Iska na gani saboda ni zan ba da labari saboda ni ma ina daga cikin wadanda suka je can. To wannan dai ni dai na ga jama'a ba masaka tsinke, na rasa inda za ni, sai boye ni ma ake yi, wanda shi ma a na Sani Mai Iska da Fati haka aka yi, kuma zai iya yiwuwa ma na Sani Mai Iska ya fi nawa yawan jama'a.

Kafin wannan rana ta daurin aurenka da kuma yanzu da aka daura Auren, akwai wani dan dar dar da kake ji cewa za ka shiga wata sabuwar rayuwa?

SHU'AIBU: E, duka na yi wannan, amma a yau da aka shafa Fatiha shikenan kuma sai na ji tamkar da ma can haka nake. Sai na ji ni na koma normal (wato daidai).

Jama'a 'yan kallo sun saba ganinka a finafinai kana fitowa a matsayin dan ta'adda. Shin kana nan a kan bakanka na yin wasa a matsayin dan ta'adda, ko kuwa za ka sauya tunda ka yi iyali?

SHU'AIBU: Kwarai ma kuwa, ina nan a kan yadda aka san ni! Kuma da ma ai ba nan kadai nake ba: ina buga nan in buga can wurare daban-daban. Wannan harkana ne, kuma mutane da suke kallo sun fahimci dai a gaskiya ba haka nake ba, kawai harka ce ta sana'a, kuma mutane sun fahimci a gaskiya ba haka nake ba, kuma sun sani. Saboda haka ba wani zancen dainawa.

Balaraba ta zama tauraruwar finafinai. Shin za ka bar ta ta ci gaba da wasanta, ko kuwa dai ajiye ta a gida za ka yi?

SHU'AIBU: E, to ai mu Islamically (wato a addinance) ba haka ba ne, kuma tun ma kafin haka ta faru mun riga mun yi magana da ita cewa in dai har mukai aure shikenan ita ta daina yin fim. Ba ita kadai ba ma, akwai sauran mata da dama wadanda suke yin wannan harkar, amma dukkaninsu wadda ta yi aure tana komawa gidan mijinta ta zauna. (Murmushi) To ni so ake in mun yi aure in kawo ta ta ci gaba da yin fim kenan?

Wace shawara za ka ba abokanka maza wadanda ba su sami damar yin aure ba?

SHU'AIBU: Wannan nufin Allah ne; lokaci ne kawai. Ni ma lokaci ne ya zo min, wanda ban taba tsammanin haka ba sai ga shi yau na wayi gari a haka. Kamar yadda na ga nawa haka su ma na san za su ga nasu. Sai dai fatan Allah ya ba mu sa'a.

Da kai da Sani Mai Iska kun kafa tarihi wajen auren 'yan wasa mata. Wace shawara za ka ba sauran 'yan wasa maza.

SHU'AIBU: E, Sani Mai Iska shi ya bude mana hanya kuma ga shi in Allah ya yarda ta yi ta tafiya kenan. Yau dai ga ni a cikinmu Sani ya yi na daya ni kuma na zo na biyu. Haka a cikinmu za a samu na uku, insha Allah har na hudu zuwa biyar.

Akwai wasu wadanda ke soyayya, kuma kana hangen za ta kai ga aure a cikin 'yan wasa?

SHU'AIBU: Kwarai ma kuwa, akwai masoya bila adadin; akwai wadanda ta fito fili akwai kuma wadanda kuma ba ta fito fili ba, wanda kuma da ma daga haka abin yake dorewa. Suna nan tafe. Su ma muna yi masu addu'ar Allah ya tabbatar da haka.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin