Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 29   Mayu 2002


BABBAN SHAFI
Mu Leka Mu Gani
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 1
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 2
Rayuwarmu
Mu Leka Hollywood
Malam Zurke
Mutanen Boye
Bukukuwa
Sauran Labarai
Ra'ayi Ba Gaba ne
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Akwai:
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


Zumunci da Shu'aibu ba zai yanke ba

Inji Baban Balaraba

Shi ma mahaifin marigayiya Balaraba da marigayiya Jummai, wato MALAM MUHAMMADU KAURA, ya nuna matukar sadaukarwa ga Ubangiji a kan wannan babban abin bakin ciki da juyayi da ya fada wa gidansa. A cikin hirar da suka yi da ALIYU ABDULLAHI GORA a Kaduna makwanni kadan bayan rasuwar 'ya'yansa, ya nuna cewa shi da iyalinsa sun karbi kaddarar abin da ya faru. Kuma ya ce huldarsu da Shu'aibu za ta ci gaba har illa masha Allahu. Har ya ce in ma ta kama wata 'yarsa kanwar Balaraba suka sasanta kansu da Shu'aibu, to a shirye yake ya hada su a aure. Ko Shu'aibu zai karbi wannan kalubalen, Allahu a'alamu!

Fim: Baba, za mu fara da yi maka ta'aziyya tare da jaje. Wadanda suka rasu Allah ya gafarta masu, wadanda suka samu raunuka kuma Allah ya ba su lafiya.

M. MUHAMMADU: Amin, amin.

Fim:Shin yaya ka ji dangane da faruwar wannan al'amari?

M. MUHAMMADU: Bismillahir Rahmanir Rahim. Inna Lillahi wa Inna Ilaihi raji'un! A hakikanin gaskiya, wato na san wannan abu daga Allah yake. Haka Allah ya so, amma a hakikanin gaskiya ina mai dimauta saboda rasuwar wadannan 'ya'ya nawa. Sai dai kuma ni na tuna, har yau dai ina yi wa Allah godiya. Bayin Allah, jama'a, ina yi masu godiya. Don wato a bakin jihohin nan na Arewa kaf, ba inda ba su ciko mota ba suka zo suka yi mani ta'aziyya; wanda ma ban taba gani ba ya zo. Kuma sun nuna rudewarsu, wanda a wani lokacin ma gaba daya ni nike ba su hakuri. To, ka ga ko ya zamana kai da ka haifi abu ma, wanda bai haifa ba, wani ma da yawa sai su ce, wani ya taso daga Ibadan, wani Legas, wani Taraba, wani Gombe, wani Maiduguri, su zo suna kuka, to kai me za ka ce wa wannan mutum? Wanda yake ya bar aikin da yake yi, ya dauki dukiyarsa ya biya mota ya zo, sanadiyyar rasa rayukan su Balaraba. Amma shi ma ya sadaukar da rayuwarsa ya zo ya yi mani ta'aziyya. Saboda haka in ka gan shi dole kai ma ka tausaya mashi. To, kuma sai dai godiya ga Allah. Allah Ubangiji shi ne zai saka ma kowa da alherinsa. To, ina yi wa kowa godiya. Kuma su ci gaba da yi mata addu'a. saboda akwai karshe, inda take cewa ta shiga Film Industry lafiya, ta kuma fita lafiya, amma masu zaginta, to su jira su ga yanda za su kare da tasu rayuwa.

Fim: Yaya dangantakarku za ta kasance da Shu'aibu, ganin cewa Balaraba ce ta hada ku da shi, kuma ga shi Allah ya karbi abinsa?

M. MUHAMMADU: Allahu Akbar! Ina tausaya ma Shu'aibu, ko da yake komai a hannun Allah yake, haka Allah yake son ganin abin. Amma Shu'aibu dai, ita Balaraba dai ita ta kawo shi, kuma na yi mata alkawarin cewa zan daura masu aure, ko ni na mutu zan bar wasiyya; abu daya zai hana, sai dai ko in ya zamana ita ba ta da rai. To Allah ya sa na daura masu aure.

To, kafin a daura auren nan ta fadi wasu halaye guda hudu na Shu'aibu. Ta ce tana sonsa saboda shi mutum ne mai hankali. Na biyu, ta ce shi mutum ne wanda ba makaryaci ba ne. Na uku, ta ce kuma ba ya gulma. Na hudu ba ya neman mata. To duk mutumin da ya hada wadannan in ana neman mutumin kirki, dattijo, to in an samu wannnan, walillahil hamdu. Saboda haka shi ya sa ni ma in Allah ya yarda zumunta ba za ta yanke ba tsakaninmu da Shu'aibu.

Fim: Yanzu kenan zumunta ta kullu tsakanin iyalan gidanka da kuma na gidan su Shu'aibu har abada?

M. MUHAMMADU: Kwarai da gaske! Na farko dai tukunna inda zumunci a kafa yake. Tunda shi yana tasowa yazo nan ya gaishe mu, mu ma haka za mu tashi mu je mu gaishe su. Ka ga zumunta ta kullu kenan. Kuma sauran wasu abubuwa Allah shi ne ya bar ma kanshi sani, wadanda za su faru a gaba.

Fim: Yanzu kenan duk hidimar da ta taso a gidan ka sai ka sanar da 'yan gidansu?

M. MUHAMMMADU: E, kwarai da gaske. Ai sha'anin arziki ne, kuma abinda Allah ke so kenan, zumunta.

Fim: Me za ka ce dangane da zargin da wasu ke yi cewa asiri ne aka yi mata?

M. MUHAMMADU: Allahu Akbar! E, to mutumin da ya zamana Musulmi ne, kuma har ya yi imani da Allah, to ai ina jin ma ba zai kawo wannan ba. Saboda ba mutumin da bai son abin alheri. To amma in Allah bai ba shi ba ka ga sai ya yi hakuri. To ashe da wani na sa a yi wani abin, da sai ya sa a je a yi mashi. Saboda haka ni na dauka komai daga Allah ne, kuma uwarta ma haka man. Amma fatan da nake yi, Allah Ubangiji ya gafarta masu. Ni dai na gafarta mata. A hakikanin gaskiya na rasa 'ya'ya masu ladabi. Allah ya gafarta masu. Kamar kuma yadda Balaraba ta ce a hirarta ta karshe inda take cewa jama'a su yafe mata kuma su ci gaba da yi mata addu'a, to ina fata duk wani masoyin wadannan 'ya'ya da ni kaina, to ya ci gaba da yi masu addu'a.

Fim: Bayan rasuwar su Balaraba, kun yi tunanin ku aurar wa Shu'aibu da wata 'ya daga cikin zuriyarku?

M. MUHAMMADU: E, to, a yanzu dai wato abin da ya sa ni ba zan yi saurin cewa haka ba, don dukkansu da suka yi auren nan, ba wani mutum da na taba kawo masu na ce su aure shi. A'a, tsakaninsu ne suke kawowa su ce wannan suke so, kuma in daura masu aure. Dalili kuwa, Alllah ya kawo mu zamani. Da, da muka tashi muna yara, aure yaro sai dai ya ga kawai an yi, kuma ba yadda zai yi. To, amma yanzu Allah ya kawo mu zamani, duk wanda ke saurin yin wanan abin, in ba a ci sa'a ba wato sai ka iske an bata goma ba a gyara daya ba; kai dai a matsayinka na uba ka ce ga yadda kake so, a ce ba za a yi ba. To ka ga in ka ce za ka dauki wani mataki mai tsauri, to karshenta sai ka iske ranka ya baci, na ita yarinyar ya baci, na shi wanda ka ba don ka dadada mashi, shi ma ranshi ya baci.

To saboda haka, amma in Allah ya sa daya daga cikinsu, wato cikin zuciyar tamu, wata, saboda hankalinshi, saboda ka san halayen mutum su ke jawo mashi yabo, shi ke kuma jawo a guje shi, saboda haka in wata ta ce tana son shi, wa lillahil hamduu, da na yi farin ciki a haka ma.

Fim: Shin akwai wasu 'ya'yanka da suka taba rasuwa kafin su Balaraba?

M. MUHAMMADU: E, na taba experiencing wannan, to ammma ba zan kwatanta shi da wannan ba, saboda babban wansu ai rasuwa ya yi, sai dai shi ba zan kwatanta shi da wannan ba, tunda ya rasu ma ina jin ko wata daya ma bai cika ba a duniya. Saboda haka ka ga ba zan kwatanta shi da wannnan ba.

Fim: Yanzu baba za ka iya barin wasu daga cikin 'ya'yanka su shiga harkar fim?

M. MUHAMMADU: Wato ku 'yan jarida kun sha tambayata bayani wanda ya danganci wannan. A hakikanin gaskiya ina gaya maku cewa Balaraba fa ban taba mafarkin cewa za ta yi fim ba. Kuma yarinya ce mai kunya, mai hankali, amma wani ya ce za ta yi fim sai in ce a'a saboda, wato tana da kawaici. Amma da Allah ya kaddara za ta je har ta yi tashe duniya ta san ta, ka ga ta je, kuma haka ta fada ta ce tana so ta je duniya ta san ta, kuma daga nan aurenta za ta yi, ta bari. Idan Allah ya kaddara wata za ta yi, ba zan iya cewa a'a ba.

Fim: Wane sako gare ka ga shi mijn Balaraba, wato Shu'aibu?

M. MUHAMMADU: Addu'a zan yi wa Shu'aibu. Allah Ubangiji ya ba shi lafiya, kuma ya ba shi karfin jure wannnan rashi da muka yi. Bayan haka kuma, kamar yadda ya ce abin nan daga Allah yake, ina fatan ya tsaya a haka. Kuma duk lokacin da Allah ya sa ya samu hali, ya samu hanya, ya zagayo mu gaisa. Kamar yadda na gaya maka, ya zo nan ya yi mani alkawari cewa yanzu Balaraba ba ta nan. Saboda haka sai dai in ce Allah ya yi mashi albarka, na gode.

Fim: Za ka iya tsaya wa Shu'aibu a matsayin uba don ya samo mata daga wani wuri?

M. MUHAMMADU: Af, ni da ni kaina ma nake fatan Allah ya sa cikin 'yan'uwanta wata ta ce mani Shu'aibu take so! Ina wannan roko balle kuma a ce ya samo daga wani wuri, yau ai ni ne a gaba ma.

Fim: To baba mun gode. -

M. MUHAMMADU: Allah ya yi maku albarka. Ni ma na gode.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin