Daga WAKILANMU, a Kaduna
KWANAN nan za a fara sauraron wata kara wadda mijin marigayiya Jummai Mohammed, yayar fitacciyar 'yar wasa Balaraba Mohammed, ya kai mujallar Fim a kotun Abuja sakamakon ta'aziyyar da mujallar ta buga a fitowarta ta watan Afrilu 2002.
Idan an tuna, mujallar ta ware shafi daya musamman don yin ta'aziyya ga iyalai da magada da masoyan su 'yar wasan da danginta mutum uku, wadanda Allah ya yi wa rasuwa a hadarin mota a ran 16 ga Maris, 2002. A shafi na 5 na fitowar wancan watan ne aka yi ta'aziyyar, tare da buga hotunan mutum biyu da suka rasu, wato Balaraba da 'yar'uwarta Jummai.
Shi mijin Jummai, wani mai suna Adamu Umar wanda ke aiki a Abuja, bai ji dadin buga ta'aziyyar ba, musamman ma dai da aka buga hoton Jummai. Shi ya sa ya kai kara yana son kotu ta bi masa hakkinsa da ya ce yin hakan ya saba mawa.
A cikin takardar kara da lauyansa ya shigar a kotun, Adamu ya ce shi da matarsa Jummai sun san cewa tunda Balaraba fitacciyar 'yar wasan fim ce, to aurenta zai tara jama'a sosai, saboda haka ya hana matarsa ta dauki hoto ko ta fito a gaban kyamarar bidiyo ba tare da izininsa ba, kuma wai ita da Balaraba sun amince din. Ya ce shi ya sa ma Balaraba ta hana kowa ya dauki hoton Jummai.
Ya yi ikirarin cewa ya fada wa Jummai ta tafi 'boys' quarters' na gidan ta zauna domin ba ta ma dade da haihuwa ba.
A cewarsa, 'yan mujallar Fim sun halarci bikin auren na Balaraba kuma sun daddauki hotunan kati da na bidiyo a ranar auren da bayan ranar. Kuma wai ya gaya masu kada su kuskura su dauki hoton Jummai.
Adamu ya kara da yin bayanin cewa su Balaraba da Jummai sun rasu a hadarin ran 16 ga Maris, 2002, amma 'yarsa 'yar kwanaki 43 da haihuwa ba ta rasu ba.
Ya ce 'yan mujallar Fim sun dauki hotunan bidiyo na bikin da na hadarin da aka yi, kuma suna da niyyar yin kasa-kasai su sayar wa jama'a, wanda ba su da izinin yin hakan. Ya ce a ranar sadakar bakwai wasu mutane sun same shi sun bukaci su yi wani shiri na kaset din bidiyo a kan al'amarin Balaraba domin su sayar, kuma bai ji dadin hakan ba, kuma ya gargade su kada su sake su yi hakan. Ya ce ya hana kowa ya sa hoton matarsa a kaset din bidiyo ko wani shirin fim ko kuma mujalla ko jarida.
Adamu Umar ya ci gaba da cewa an zo an gaya masa akwai wasu 'yan fim da suke kokarin fito da wani kaset na bidiyo a kan aure da rasuwar su Balaraba inda har za a nuno matarsa a ciki. Wannan ya sa ya garzaya kotu domin ya hana su, kuma an yi yarjejeniya da su a kan ba za su buga hoton matarsa a mujalla ko a kaset ba. (Masu karatu za su tuno mun ba da labarin a Fim ta watan jiya inda Adamu ya so ya yi shari'a da wasu 'yan fim na Kano a kan hakan, amma aka sasanta).
Ya ci gaba da cewa duk da haka a ranar 31 ga Maris, 2002 a unguwar Maitama a Abuja ya ga mujallar Fim kuma tana dauke da hoton Jummai a shafi na 5, tare da cikakken rahoto kan auren Balaraba da hadarin da ya yi sanadiyyar rasuwarta. Ya ce abokansa da dama sun ce masa me ya sa ya bari hoton matarsa ya fito a mujalla?
A cewar Adamu, ganin hoton matarsa ya sa ya kidime har ya kasa yin komai, kuma ya sha wahala saboda tunaninta. Ya ce bai ba masu mujallar izinin buga hoton ba.
Bugu da kari, Adamu ya yi ikirarin cewa 'yan mujallar Fim suna nan suna shirin fito da kaset din bidiyo wanda suka yi a lokacin bukin Balaraba da kuma zaman makoki. "Wadanda ake karar sun yi rikodin na bikin auren, da ainihin yadda ma hadarin ya auku, da kuma ainihin matuwar matata da sauran mamata, sannan da yadda aka rufe su," inji shi.
Ya ce a gaskiiya idan har aka kyale su suka nuna wa dukkan duniyar nan wadannan hotunan, to shi dai haukacewa zai yi ko kuma ma ya mutu baki daya. Saboda haka dai yana so kotu ta hana mujallar fito da wannan kaset din. Haka kuma yana so kotu ta hana mujallar kara buga hoton Jummai domin idan ta yi zai shafi kwakwalwarsa. Yana kuma so a biya shi rabin miliyan saobda mujallar ta buga hoto wai bayan ya hana ta bugawa.
Wakilinmu ya waiwayi babban Editan Fim kuma mawallafin mujallar, Malam Ibrahim Sheme, don jin ta bakinsa. Sai ya ce "Ba zan so in yi bayani ba tunda maganar ta je kotu, amma ina so mutane su sani cewa ina tausaya wa Adamu Umar domin yana cikin garari."
Duk da haka, Sheme ya yi la'akari da cewa takardar karar cike take da karairayi marasa kan gado. "Kuma Malam Adamu ya gwamutsa batun shari'arsa da wasu mutane can daban da maganarmu. To Allah dai ya kai mu kotu lafiya."
Wata majiya ta shaida wa Wakilinmu cewa surukan Adamu sun damu matuka kan wannan magana. Kuma sun yi mamakin yadda mutumin da aka yi wa gaisuwa zai ji haushin gaisuwar har ya kai kara.