Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 31   Yuli 2002
Balaraba Muhammad (1983-2002)


BABBAN SHAFI
RA'AYI
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) 
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
Ra'ayin Mujallar Fim
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon Fim ta 30
Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


'Yan wasan Kaduna sun shirya taron addu'ar Balaraba

Daga ALIYU ABDULLAHI GORA II a Kaduna

KAMAR yadda aka aiwatar da addu'a a Kano domin nema wa 'yar wasan nan marigayiya Balaraba Mohammed gafarar Ubangiji kwanaki kadan bayan rasuwarta, Kungiyar 'Yan Wasa ta Jihar Kaduna ma, a karkashin shugabancin Malam Yahuza Abubakar Ilu, ta yi addu'a a wani babban taro kwanan baya.

Taron, wanda aka gudanar a harabar Hukumar Al'adun Gargajiya da Fasaha ta Jihar Kaduna, ya samu halatar malamai da suka hada da Babban Sakataren kungiyar Izala ta kasa, Sheikh Umar Hassan, wanda kuma shi ne limamin Jumma'a a masallacin Kwalejin Rimi da ke Kaduna, da Sheikh Salisu Mu'azu. Akwai mahaifin Balaraba, Malam Muhammadu Kaura, da yayyenta maza Abdullahi da Abubakar, wasu furodusoshi da daraktoci da kuma fitattu da sababbin 'yan wasa masu yawa a wurin.

Bayan addu'o'in da malaman suka jagoranta, a lokacin taron an gabatar da jawabai masu ratsa zukata kan al'amrin rayuwar duniya, wa'azin da ke kunshe da neman imani kan mutuwa da matsayin shi kansa wasan kwaikwayo a Musulunci.

Sheikh Umar Hassan ya tabbatar wa mahalarta taron cewa wasan kwaikwayo ko fim kamar yadda ake daukarsa a yanzu yana da asali a Musulunci. Sai dai ya ja hankalin duk masu yin wannan sana'a da su rika tsarkake sana'ar daga abubuwan da aka haramta a shari'a. Malamin ya kara da cewa harkar kunshe take da abubuwa haramci masu yawa wadanda Allah zai tuhumci bawansa a kan aikata su idan har ya mutu bai tuba ba.

Shari'a da mujallar Fim kan ta'aziyyar su Balaraba:
Kotu ta ce Adamu Umar ya kawo shaidu

IDAN mai karatu bai manta ba, a watan jiya mun ba da labarin karar da mijin Jummai, yayar marigayiya Balaraba Mohammed, Malam Adamu Umar, ya kai mujallar Fim a kan sakon ta'ajiyyar su Balaraba da ta buga a fitowarmu ta watan Afrilu na bana.

Jummai (A'isha) ta rasu a hadarin mota tare da wasu 'yan'uwanta a kan hanyar zuwa Kano domin halartar walimar da abokan ango dan wasa Shu'aibu Lawan (Kumurci) suka shirya saboda aurensa da kanwar Jummai, fitacciyar 'yar wasa Balaraba Mohammed.

To, a ran Litinin, 10 ga Yuni, 2002, aka fara sauraron karar a babbar kotun Abuja da ake 'Zone 5' a birnin na Abuja.

Da misalin karfe 10:15 na safe Adamu ya isa kotun tare da wasu abokansa, yayin da Malam Aliyu Abdullahi Gora II ya je a madadin hukumar mujallar Fim. Alhaji Sani Mohammed Katu, Esq., na cambar lauyoyi ta 'Mamman Nasir and Co.', Kaduna, shi ne ya halarci kotun ya wakilci mujallar Fim.

Da za a fara sauraron karar, an umurci Adamu ya tsaya a kejin mai kara, shi kuma Aliyu ya tsaya a kejin wanda ake kara.

Lauyan mujallar Fim ya fara yin bayani dangane da wadanda ake kara, ya gabatar da kansa, sannan ya bayyana wa kotu cewa shi ne ya tsaya wa kamfanin Fim tare da ma'aikatansa.

Bayan ya zauna sai lauyan mai kara ya mike ya nuna rashin amincewa a kan tsayawar da lauya Sani ya yi wa ma'aikatan mujallar Fim.

Da ya zauna sai alkalin kotun, Hon. Justice M.B.D. Mensen ta yi bayani, inda ta nuna wa lauyan mai kara cewa ba ta ga wani abin damuwa ba don lauyan Fim ya ce ya tsaya wa dukkan wadanda Adamu Umar yake kara.

Haka dai aka yi ta bayani tsakanin lauya da lauya, daga karshe lauyan Adamu ya ce za su iya kawo shaidu mutum biyar a kan abubuwan da ake zargin mujallar da su, wato buga hoton marigayiya Jummai a cikin mujalla ba tare da izinin Adamu ba. A haka alkalin ta dage ci gaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 30 ga Yuli, 2002 (wato wannan watan da muke ciki). Allah ya kai mu lafiya, amin.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin