Jarumin duniya: Denzel Washington
Daga IRO MAMMAN
DENZEL Washington yana daga cikin 'yan wasan fim bakar fata da Allah ya tarfa wa garinsu nono har suka yi fice a Amerika. Hasali ma dai shi ne ya cinye kyautar Jarumin Jaruman duniya a bikin gasar finafinai ta 'Oscars' ta bana. Wannan ya biyo bayan shekaru 25 da ya shafe yana hakilo a fagen shirin fim. Sau uku yana kaiwa matakin karshe na gasar ana kada shi. A cikin 2000, sauran kiris ya ci gasar da shirin The Hurricane, to amma ina! A cikin fim din ya fito a matsayin dan damben boksin wanda ake tuhuma da laifin kisan gillar mutum uku a cikin 1966. Duk da ganin da aka yi cewa ya cancanci zama Jarumin Jarumai a shekarar, sai ba a ba shi ba.
Denzel ya saba fitowa ne a matsayin mutumin kirki, to amma da ya sauya kamanni a cikin fim din Training Day, ai fa shikenan sai ya zama zakara. Ya fito ne a matsayin mugun dansanda, mara mutunci, mai cin hanci da rashawa. Yin wannan wasan ya janyo masa yabo a kafafen yada labarai, kuma an yi cinikin fim din.
Denzel Washington dai ya dade yana gogewa a wasannin kwaikwayo na talbijin da kuma finafinai. Ubansa limamin coci ne, uwarsa kuma makitsiya ce a garin Mount Vernon na jihar New York, kuma kaunar da iyayensa ke wa shirin fim ta taimaka masa wajen kara azama a sana'ar wasan kwaikwayo.
Matakin farko da ya dauka a kan sana'arsa shi ne wani kwas da ya yi a kan aikin jarida, to amma da ya kare kwas din sai ya tafi birnin San Fransisco domin yin karatun wasan kwaikwayo. Ba a jima ba ya rika fitowa a wasanni na talbijin, har dai a cikin 1982 ya samu ya shiga cikin 'yan wasan wani shirin dirama na talbijin wanda aka dade ana gutsura wa masu kallo shi, mai suna St. Elsewhere. A wasan ne Denzel ya fara samun yabo sosai.
Daga nan sai manyan furodusoshi da daraktocin Hollywood suka fara ankara da shi. Suka fara ba shi matsayi mai kyau a finafinai. Da farko ya fito a matsayin jarumin Cry Freedom, fim din da aka shirya kan gwagwarmayar ganin bayan mulkin wariya a Afrika ta Kudu. Wannan fim din ne ya sa ya ci matsayin mataimakin Jarumin Jarumai a bikin Oscar na lokacin. Bayan shekara biyu sai fim din Glory ya biyo baya, inda Denzel ya fito a matsayin wani bawa mai juriya.
Ya zuwa lokacin, Denzel ya shiga sahun manyan jarumai, sahun da ake kira 'A-List,' har suka yi aiki a kan finafinai uku tare da daraktan nan bakar fata dan taratsi mai suna Spike Lee. Hasali ma dai, fim din da Lee ya yi a cikin 1992 a kan rayuwar bakar fatan nan mai nema wa bakake 'yanci, wato Malcolm X (sunan fim din ma kenan), shi ya jawo Denzel ya kara kaiwa matakin karshe na zama Jarumin Jarumai.
A cikin 1993 Denzel Washington ya gwada wa duniya cewa shi ma ba kashin yadawa ba ne a fim din gumurzu (action) lokacin da ya fito a shiri mai suna The Pelican Brief. A cikin 1999 kuma ya fito a wani fim din na gumurzu mai suna The Bone Collector, a matsayin masanin magunguna wanda barin jikinsa ya shanye, amma ya hada gwiwa da wata yarinya 'yarsanda (Angelina Jolie ce a matsayin) suka yi bincike kan wani mutum da ke ta kashe jama'a ba a gane ko waye ba.
Wani wasa na kwallo, Remember the Titans, tare da shirin The Pelican Brief su ne shaidar cewa Denzel mutum ne wanda zai iya yin kowane irin wasa inda ake motsa jiki sosai. To amma in akwai fim da ya jijjiga jikin Denzel, bayan The Training Day yake. A cikinsa ya sauya yanayin da aka fi saninsa da shi. Har wasu na ganin ganganci ya yi da ya sauya din. To amma masoyan Denzel, wanda yana da mata da 'ya'ya, suna ganin fim din ya kara masa kwarjini ne, kuma ya kara masa masoya.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin