"Matambayi ba ya bata"
TSAKANIN MAI ISKA DA DAWAYYA
TAMBAYA: Wai da gaske ne Sani Musa Mai Iska zai auri Rukayya Umar Santa (Dawayya)?
Daga Hauwa Kulu Ibrahim Sadiq, Hauwa Kulu Rilwanu Mohammmed, Sakina Abdullahi Kwami
Makarantar Makafi, Makama Ward, Jahun, Bauchi.
Amsar Sani Musa Mai Iska: "Ni wallahi ban san ma wannan maganar ba sai yanzu a wajenku 'yan mujallar Fim."
*
ME YA SA YAKE 'DANJA'?
TAMBAYA: Me ya sa ake kiran Sani Musa Danja da sunan Danja?
Daga Shehu Abdullahi, Yaron Mallam Abdu,
No. 19 Tudun Kofa, c/o Postmaster, Lafia. Jihar Nassarawa.
Amsar Sani Musa Danja: "Wannan suna na Danja na samo shi ne a dalilin nacin da nake da shi kan wani abu. Kuma na na yi bol lamba goma sha daya. Kuma in dai ka yi bol, ko ka san abin da mai lamba sha daya ke nufi."
*
TSAKANIN SANI DANJA DA FKD
TAMBAYA: Me ya sa ba ma ganin Sani Musa Danja a fim din FKD, kamfanin Ali Nuhu? Shin da gaske ba jituwa tsakaninku da Ali?
Daga Nuhu A. Ibrahim,
Govt. Sec. Sch. Kawaji, Jigirya Quarters, Hadejia Road, Kano.
Amsar Sani Musa Danja: "Wannnan ba zancen ba ma wata jituwa ba ne; akwai jituwa a tsakaninmu sosai, kuma mun gayyaci Ali finafinanmu kamar su Tsumagiya da Kwarya Ta Bi Kwarya. Ahmed ma mun gayyace shi a Jaheed, bai samu dama ba ne. Kuma shi ma Ali na san in har a fim dinsu akwai role din da ya dace da ni na san zai gayyace ni. Ba wata maganar rashin jituwa."
*
HIRA DA RABI'U MAI 'HRB'
TAMBAYA: Me ya sa ba za ku yi hira da Alhaji Rabi'u Harabs ba mai 'HRB Production'?
Daga Faridat Umar Kano,
Shagari Qrts, No. 12 block 216
Kumbotso Local Government, Kano.
Amsar Alhaji Rabi'u Ibrahim Harabs: "Gaskiya ni ba ni hira da 'yan jarida, sai dai ki yi hakuri."
*
'MUTU-KA-RABA' A TAWAKKALI
TAMBAYA: Ina da tambaya kan wani kuskure cikin fim din Tawakkali. Ya aka yi Ladi Mutu-Ka-Raba ta fito a kashi na 1 cikin 'yan waka, sannan a kashi na 2 ta fito a mai aikin Hindatu Bashir? Kuma shin Hadiza Kabara ce ta fito a matsayin Sa'a a kashi na 1?
Daga Murja Mohammmed Adam
Block K98 Kundila, Kano.
Amsar Editan Fim: Furodusan Tawakkali, Rabi'u Ibrahim, ya ce ba zai ce komai ba. Don haka ba ki da amsarsa.
*
KU BA NI TARIHIN NURA HUSSAINI
TAMBAYA:
In da hali muna son sanin tarihin jarumin nan Nura Husaini (Sahabi).
Daga Maryam Ali Fika,
High Court of Justice, P.M.B. 1027 Damaturu, Jihar Yobe.
Amsa: An haife shi a cikin Maris 1978 a Kano. Ya yi makarantar allo a wajen mahaifinsa, yanzu kuma yana karatu a Kwalejin Koyon Shari'a ta Kano. A cewarsa, ya nemi shawarar shiga harkar fim ta hanyar dan'uwansa Bashir Bala Ciroki inda ya fara da kungiyar tauraruwa. Daga nan ya yi finafinai kamar Zarge, Sangaya, Linzami Da Wuta, Sirace, Kudiri, Tsaro, Jirwaje, da dai sauransu. A yanzu haka malamin makarantar allo ne.
*
ME AKE NUFI A HUZNEE 2?
TAMBAYA: Menene ma'anar alamar tambayar da aka yi a karshen Huznee kashi na 2, kuna da shirin yin kashi na 3 ne?
Daga Hajiya Ni'imatu Sani Bature,
P.O. Box 90, Katsina.
Amsar darakta Sir Hafizu Bello: "Babu wani kashi na 3 a fim din Huznee."
*
ALEE BABA BAI ZUWA BIKI?
TAMBAYA: Me ya sa Alee Baba ba ya zuwa gidan biki da kayan da yake yi wa 'yan fim kida?
Haj. Ni'imatu Sani Bature,
P.O. Box 90, Katsina.
Amsar Alee Baba Yakasai: "Gaskiya Hajiya ba ma fita da kayan kidanmu saboda sai dai na bai wa (Muntari) Kwanzuma kudin ya fita. Sai dai in ta kure in je doan gudun kar a ce ina girman kai. Amma ina zuwa na 'yan fim; da ma da haka na fara."
*
ALEE BABA KADAI KE YIN KIDAN?
TAMBAYA: Shin Alee Baba kai kadai ne kake yin wannan kidan ko kana da mataimaki? Misali nakan ji kana kidan duma, da casa, da busa, da dai sauransu.
Daga Ahmed Iliya Sheme,
School of Health Technology, Kankia, Jihar Katsina.
Amsar Alee Baba Yakasai: "A fagen kida ba ni da mataimaki sai Allah. Ni kadai nake hada kidana - da duma, da busa da jita, da sauransu."
*
KUMURCI YA DAWO RUWA KUWA?
TAMBAYA: Shin Kumurci zai ci gaba da yin fim kuwa?
Daga Hauwa Kulu Ibrahim Sadiq, Hauwa Kulu Rilwanu Mohd, da Sakina Abdullahi Kwami,
Makarantar Makafi, Makama Ward, Jahun, Bauchi.
EDITA: E, Shu'aibu ya koma yana yin wasanninsa a finafinai kamar yadda ya saba.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin