"Matambayi ba ya bata"
TAMBAYA: Daga Yayani Popular Guy Isawa, P.O. Box 279, Isawa, Giade L.G.A., Jihar Bauchi.
"Don Allah ina so in tambaye ka Ibrahin M. Mandawari: yaya aka yi ka yi sanyi da finafinai? Ko ba ka samun dama ne? Kuma yaya aka yi ba ma ganin Tahir Moh'd Fagge yana fitowa a finafinai? Ka san ka fi kowanne dan wasa ko furodusa ko darakta."
Amsar Mandawari: "Da farko dai gaskiya ban fi kowa ba, kuma finafinai ba dainawa aka yi ba, suna nan. Fitowa ne ba su yi ba, amma suna kan hanyar fitowa, su wajen guda hudu, su ne: Mahandama, Namshaza, Dawainiya, da kuma Hannun Dama. Sannan maganar Tahir Fagge, yana nan kuma yana fitowa a finafinai. Ofis dinsa ma yana nan Murtala Mohammed Way kusa da Sack & Motors yana kallon masallacin Fagge. In ka duba fim din Sharadi ma za ka gan shi a ciki."
*
TAMBAYA: Daga Sakina Sani Gwarzo, No 536, Dala Road, B.U.K. New Site, P.M.B. 3011, Kano.
"Ina so in tambayi Ibrahim Mandawari kan hirar da aka yi da shi inda ya ce ba fim din da zai shirya ya yi rawa a ciki. To sai kuma ga shi a Mu Shakata na3 ya yi rawar. Me ya sa?"
Amsar Mandawari: "Na yi rawa ne a Mu Shakata na 3 saboda murnar bikin 'yata Fati Mohammed."
*
TAMBAYA: Daga Mohammed B. Aliyu Dan Fulani Warra.
"Shin don Allah Ibrahim Mandawari, wato baban soyayya, shekarunsa nawa da fara finafinan Hausa?"
Amsar Mandawari: "Ni dai na fara harkar wasan Hausa a 1979 kuma wannan abu ne daga Ubangiji."
*
TAMBAYA: Daga Shu'aibu Mohammed Zazzau, Central Registry Office, Command and Staff College,P.M.B.2234,Jaji Jihar Kaduna.
"Don Allah me ya sa ina yo wa 'Mandawari Enterprises' takarda ba sa son aiko min da tasu takardar?"
Amsar Mandawari: "Ka yi hakuri, ayyuka ne suka yi mana yawa. Amma yanzu mun sami filin ba da amsar wasiku a cikin filin Mu Shakata sai ku saurare mu."
*
TAMBAYA: Daga Amina Zubairu Ibrahim, Yahaya Madaki Way, beside Gidan Ibrahim Katsina, Katsina.
"Ina so in tambaye ku ko za ku iya gaya min inda Asma'u, uwargidan fim din Hakuri, take."
Amsar furodusan shirin, Ahmad S. Alkanawy: "Asma'u ta yi aure tun tuni. Tana gidan mijinta."
*
TAMBAYA: Daga Mohammed Jamilu Mohammed Jangwa, Anguwar Wadata ,Azara Local Govt, Jihar Nasarawa.
"Shin Sani Musa Danja da Yakubu Muhammad, wato 'Two Effects,' sun taba yin aure ne?"
Amsar Sani da Yakubu: "Gaskiya ba mu taba yin aure ba."
*
TAMBAYA: Daga Baba Gana Yazarim da Baba Gana Kolaye sannan da Maina Bulama Massa, Unguwar Mairi Nguadda, Bama Local Govt., Jihar Borno.
"Me ya sa Salisu Yomen ya shirya fim mai suna Abida amma kuma bai sa Abida a matsayin jarumar shirin ba sai Balaraba kuma Abidar tana nan raye? Bai yi daidai ba. Ya kamata Abida ta zama jarumar fim din don ya daga ta kamar Wasila Isma'il a cikin Wasila."
Amsar Rabi'u kanin furodusa Salisu Yomen: "Ba kin sa Abida muka yi ba, wasa ta yi ta yi mana da hankali, shi ne mu kuma da Allah ya hada mu da Balaraba sai muka ba ta fim din. Da ai Abida din ce a fim din."
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin