"Matambayi ba ya bata"
Tambaya: Daga Nasiru Bello Abubakar Mai Awo, P.O. Box 3252, Sokoto.
"Don Allah Ali Nuhu me ya sa ba ka zuwa Sokoto? Me ya sa ba ka fitowa a fim din 'Iya-Tama Multimedia'? Na ji an ce aurenka ya matso ina son don Allah in lokacin ya yi ka aiko min da kati. Ina son cikakken adireshinka domin in samu damar ba ka shawara.
Meye cikakken sunnan B.R.H. Production?"
Amsar Ali Nuhu da ta Edita: "Na taba zuwa Sokoto har sau biyu. Lokacin fitowata a fim dinsu ne bai yi ba. Amma akwai fim din da za mu yi kwanan nan da Iyan-Tama; Insha Allah kwanan na za a yi bikina kuma za ka ga kati; Adireshina shi ne: c\o 'FKD Productions, Gidan Dan Asabe No. 105, Zoo Road, Kano."
"B.R.H. yana nufin Bashir Rabi'u Hadi."
*
Tambaya: Daga Auwal Rabi'u Dansadau, c/o Govt. Science Secondary School, Dansadau, P.M.B. 1030, Gusau, Zamfara State.
"Wai da gaske ne da ake yayatawa ana cewa tsakanin Ali Nuhu Da Aina'u Ade babu shiri shi ya sanya ba su fitowa a cikin fim a matsayin saurayi da budurwa?"
Amsar Ali Nuhu: "Wannan magana karya ce. A halin yanzu muna da fim biyu da ita-Tsokaci da Jalli-kuma akwai wani ma na kamfarin 'FKD Productions' da za mu yi tare insha Allahu."
*
Tambaya: Daga Isa Ibrahim, c/o Alhaji Salihu Baba & Sons, P.A. Gbajinba, Guma L.G.A., Benue State.
"Finafinai nawa ne Ali Nuhu ya fito a cikinsu? Kuma guda nawa shi ya zama jarumi? Fim nawa ya rubuta da kansa? Da gaske ne Alisai ya ba da cin hanci kafin a ba shi fim?"
Amsar Ali Nuhu: "Na fito a cikin finafinai kamar guda dari da ashirin. Na rubata fim da hannuna kamar guda goma sha biyu. Batun sai na ba da cin hanci, wannan kuma sai 'yan mujalla su ba ka amsa!"
*
Tambaya: Daga Maryam Mohammed Lakude, No. 1, Maigatari Road, Gumel, Jihar Jigawa.
"Su waye suke sharhi a kan finafinai, saboda muna son aiko da shawarwari."
Amsar editan Bidiyo: "A cikin mujallar Bidiyo ne aka fi yin sharhi kan finafinai. Ma'aikatan mujallar tare da wasu mutane masu karatu kan aiko da nasu a buga, haka kuma muna samun wasu sharhin daga masu aiko mana daga intanet. Duk abin da kike son bada shawara a kansa fili a bude yake. Mun gode."
*
Tambaya: Daga Baba Gana Yazarim, Baba Gana Koloye, Maina Bulama Massa Unguwar Maira N. Gudda Bama L.G.A., Borno State.
"Yaya ake ciki batun fim din Ahmed, wato Zubaida, kashi na 2? Ko babu kashi na biyun ne?"
Amsar Ali da Ahmed S. Nuhu: "Fim din Zubaida ba shi da kashi na 2, guda daya ne kawai."
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin