Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 28   Afrilu 2002


BABBAN SHAFI
Mu Leka Mu Gani
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 1
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 2
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 3
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 4
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 5
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 6
Malam Zurke
Ra'ayin Mujallar Fim
Hajjin Bana
Sauran Labarai
Ra'ayi Ba Gaba ne
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN

 
If you had a new browser, you would be able to view this java applet. Akwai:  


Kungiyar Dillalan Kaset ta shiga rudani a Kano

Daga WAKILINMU, a Kano

BISA dukkan alamu, ko da shugabancin sababbin shugabannin Kungiyar Dillalan Kaset na Jihar Kano ya dore, to kujerar mulkin ba za ta yi wa shugabannin dadin zama ba. Don kuwa tun ba a dade da ba su kujerar ba har sun fara samun adawar rashin yarda da cancantar zaben nasu da aka yi. Yayin da su shugabannin ke ta kumajin kama aiki, tuni har an fara sukarsu, ana zarginsu da cewa ba zabensu aka yi ba, "dauki-dora" aka yi.

Jaridar nan ta Turanci da ake bugawa a Kano, The Triumph, ta ranar 19 ga Fabrairu, 2002, ta bugo sunayen sababbin shugabannin kamar haka: Alh. Garba Sidi, Shugaba; Alh. Rabi'u B.K., mataimakin shugaba; Alh. Salisu, sakataren kudi; Alh. Muhammadu Kalarawi, ma'aji; Alh. Sanusi Kalarawi da Alhaji Aminu H. su ne jami'an hulda da jama'a.

Sauran sun hada da Alh. Danlami Sani, mai bincike; Alh. Habibu Ahmed, mai ba da shawara a kan al'amurran shari'a; Alh. Bala ABM, sakatare, da kuma Alh. Bala Sunnah a matsayin mataimakinsa.

Alamomin rikici sun fara kunno kai 'yan kwanaki kadan bayan an bayyana sunayen shugabannin a jaridar a shafinta na 4. Ranar 18 ga Fabrairu Alh. Ahmed Mohammed Amge, wanda shi ne tsohon sakatare na kungiyar, mai suna 'Kano State Cassettes Sellers and Recording Cooperative Society (KESRCS)', ya rubuta takardar rashin yarda da sababbin shugabannin zuwa ga Hukumar Adana Tarihi da Al'adu ('Kano State History and Culture Bureau') ta Jihar Kano.

Kafin hukumar ta kai ga aiwatar da wani ba'asi, tuni har sababbin shugabannin sun rubuta wa tsohon shugaban kungiyar, Alh. Musa Na Sale, takarda a ran 21 ga Fabrairu don neman ya damka masu takardun ofis da sauran kaya domin su kama aiki. Ganin ana neman a kai ruwa rana, sai Hukumar Adana Tarihin, a ran 27 ga Fabrairu, ta aika wa babban jami'in 'yan sanda da ke Kwalli takarda. Takardar, mai lamba HCB/CP/614/1, an aika da ita ga wadansu muhimman wurare, ciki har da ofishin mujallar Fim.

Wani sashe na takardar ya nuna cewa ita hukumar ba ta yarda da sababbin shugabannin ba. Wadanda ta sani har yanzu su ne shugabancin da Alh. Musa Na Sale ke yi da kuma shi Alh. Amge a matsayin sakatare. Takardar, wadda Adamu I. Datti ya sanya wa hannu, ta nemi jami'an tsaro da kada su yi hulda da mutanen da ta ce "su ke kiran kansu sababbin shugabanni."

Mujallar Fim ta tuntubi Musa Na Sale ganin cewa mujallar tana da cikkaken bayanin saukarsa. Alh. Musa ya tabbatar wa Fim cewa shi ya sauka kuma ya ajiye kayan aiki. Da aka tambaye shi cewa har yanzu Hukumar Adana Tarihi da Al'adu ta ce ita shugabancinsa ta sani, sai Na Sale ya furta cewa, "Abin da ya sa suka ce haka, shi ne su ba su yarda da sabon zabe ba, domin sun san lokacin da muka sauka kuma an nada kwamitin rikon kwarya. To kwamitin an ba shi lokacin da zai yi kafin a yi zabe sabo."

Ya kara da cewa to lokacin da aka bai wa 'yan rikon kwaryar bai yi ba, sai aka yi wani zabe, kuma an yi da su sai sun aiwatar da wasu ayyuka kafin zabe. To ba su aiwatar din ba. Wannan, inji Na Sale, shi ya sa hukumar ta ki yarda da sababbin shugabannin.

Fim ta dawo wurin Alh. Amge don neman jin dalilan rashin yardarsu da sababbin shugabannin. Farkon kukan da Amge ya yi, shi ne, "Babu yadda za a yi a rusa kungiya a yi zabe ba tare da yawun 'yan kungiya ba. Lokacin da suka ce za a yi zabe, idan dan kungiya ya je wurin, korarsa ake yi su ce ka tafi ba a gayyato ka ba, 'yan kungiya na ji suna gani ba yadda suka yi."

Da aka tambaye shi yadda aka yi zaben, sai Amge ya ce, "Mutum daya ne ya haddasa wannan rudani, shi ne Rabi'u B. K. Ya ce shi ba zai taba bin kungiya ba, kuma wai babu yadda za a yi bakki su rika zuwa suna shugabantarsu."

Amge dai cikin bacin rai ya zargi wani jami'in hadaddiyar kungiyar gama-kai (Co-operative Society) mai suna Baba Gwarzo. A cewarsa, an game kai da Baba Gwarzo da Rabi'u B.K. suka gayyaci wasu mutane suka zauna suka nada kansu. Wani bincike da Fim ta yi ya gano cewa a 'Festival Primary School' da ke Kofar Wambai ne aka yi taron da aka nada sababbin shugabannin.

Lokacin da aka nemi jin ta bakin Alh. Rabi'u B.K., ya tabbatar da cewa ai tuni su sun kama ragamar mulki babu ruwansu da rigima. Don jin ta bakin bayanan da Amge ya yi a kansa kuwa, B.K. ya tabbatar da cewa shi ya ce bai yarda wasu mutane da ya kira "baki" su shugabance su ba. "Ai dokar kasa ta ba da sharuddan yadda za a yi zabe a cikin kasa, wanda ba dan kasa ba kuwa ina ruwansa da shiga cikin zaben kasa?" inji Rabiu B.K.

Shi kuwa Amge, ya nuna cewa kungiyar tana karkashin Hukumar Adana Tarihi da Al'adu ce ba a karkashin cooperative society ba. Kuma ya furta cewa an rusa co-operative tuni. Sai ya kada baki ya ce suna nan suna shirin gurfanar da Baba Gwarzo a kotu saboda katsaladan din da ya yi a cikin kungiyar.

Nishadi za ta dawo da zafinta -

Cewar mataimakin Edita

MUJALLAR nan mai ba da labaran finafinai, Nishadi, tana nan kan hanyarta ta dawowa don ci gaba da buga labarai kamar yadda take yi. Wannan batu ya fito ne daga bakin Mataimakin Editan mujallar, Malam Abdurrahaman Tonga, lokacin da ya kai ziyara ofishin mujallar Fim a Kano.

Mataimakin editan ya ce babban abin da ya kawo shi shi ne don ya yi wa mawallafin Fim jajen satar da barayi suka yi masa kwanakin baya a gidansa da kuma taya sabon edita murnar samun mukamin da ya yiu. Ya ce ya ji takaici matuka da ya karanta labarin satar da aka yi a gidan Malam Ibrahim Sheme. Sai ya yi addu'ar Allah ya maida masa da alherin abin da aka rasa.

Da ya dawo kan sabon edita, Malam Ashafa Murnai Barkiya, Abdurrahman ya ce ya yi farin ciki sosai kuma ya nuna cewa Malam Ashafa kwararren marubuci ne kuma mai himma da kwazon aiki. Sai dai kuma ya roki editan da sauran ma'aikatan Fim da su kara himma don kara inganta martabar finafinan Hausa.

Malam Abdurrahman ya dawo kan Nishadi ya kara tabbatar da cewa, "Nishadi za ta dawo da zafinta nan ba da wani dogon lokaci ba." Ya furta wadansu dalilai da ya ce su ne suka hana mujallar fitowa har tsawon wasu watanni. Daga cikin dalilan da ya bayar kuwa, akwai matsalar kudi da kuma kasancewa editan mujallar, Malam Bala Makosa, yana fama da dimbin ayyuka a gabansa. "Ni kuma ina yin wani dan kwas a Jami'ar Bayero. To wadannan da kuma wasu 'yan matsaloli su suka dan taka mana burki," inji shi.

Kan haka ne ya ce su yanzu suna cigiyar wanda zai zo ya karbi ragamar editan mujallar daga hannun Bala Makosa yayin da shi Makosa zai koma Babban Edita. "Ka ga ko yana nan ko ba shi gari, aiki ba zai tsaya ba," inji shi. Sai dai kuma ya ce ba kowa suke bukata ya zama editan ba sai wanda bai sha nonon tsoro ba ga uwa ko a fura. "Irinsa muke so ya zo mu yi aiki tare da shi, mu goya masa baya domin yin gwagwarmaya da wasu mutane 'yan kakuduma masu bukatar rugujewar mujallun Hausa."

Abdurrahman Tonga ya kuma nuna bacin rai dangane da wasu masu yawo suna addu'ar Allah ya karya mujallar Fim. "Ina so su fahimta cewa idan 'yan mujallar Fim suka daina buga ta, ai za su iya bude wata sabuwar mujalla mai dauke da labaran siyasa, addini da al'adu, kuma ba za a hana su buga labarin finafinai ba," injiAbdurrahman.

Dan jaridar ya furta cewa aikin jarida ba kamar yadda wasu mutane suka dauka yake ba. "A iyar sanin da na yi, ko shugaban kasa ba zai ce ga yadda dan jarida zai a yi ba, sai dai akwai ka'idojin aikin jaridar wadanda idan mutum bai bi su ba, sai kotu ta shiga tsakani." Ya kuma kara ba da misali da 'yan jaridu masu bin shugaban kasa ko wani gwamna duk inda za su. Ya ce, "Ai ka ga su ne ke zakulo labaran da shugabanni ba su so a sani, su kuma su buga, kuma doka ce ta ba su izini."

A karshe Abdurrahman ya kara yin nuni da cewa abin da aka sani ga aikin jarida shi ne ilimantarwa, fadakarwa, nishadantarwa da kuma uwa-uba babban aikin da duk dokar duniya ta ba su izini shi ne "Matsa wa shugabanni lamba yadda tilas hakan zai sa su shiga taitayinsu. Amma ba a san jarida da bambadanci ba, kowane iri ne, kuma a kowace kasa," inji Tonga, wanda aka fi sani da lakabin A.U.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin