|
|
| BABBAN SHAFI |
|
| Mu Leka Mu Gani |
| Zuwa Ga Masu Karatu |
| Wasiku |
|
| Balaraba Muhammad (1983-2002) na 1 |
| Balaraba Muhammad (1983-2002) na 2 |
| Rayuwarmu |
|
| Mu Leka Hollywood |
| Malam Zurke |
| Mutanen Boye |
|
| Bukukuwa |
| Sauran Labarai |
| Ra'ayi Ba Gaba ne |
| Dangane Da Mu |
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS
|
|
Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet. An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo! A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu. JE KA TA NAN
| |
Je ka
Akwai:
NORTHERN STAR FILMS
KE GABATAR DA
GAGARABADAU
Shiryawa: MUJALLAR Fim
Darakta HAFIZU BELLO
Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.
Labari/Tsarawa: Iro mamman;
Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito
BABU IRINSA!
Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...
Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...
Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...
Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka!
Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka
| |
|
Mun yi rashi: Allah ya yi wa Musa Gambo Sheme da Bashir Zakari rasuwa
INNA lillahi wa inna ilaihi raji'un! Allah ya yi wa wasu fitattun 'yan jarida guda biyu rasuwa. Su ne Malam Musa Gambo Sheme da kuma Malam Bashir Zakari. Sun rasu a ran Jumma'a, 12 ga Afrilu, 2000, a wani mugun hadarin mota da ya ritsa da su a garin Katari, kafin a kawo Kaduna, a kan hanyarsu ta dawowa daga Abuja.
Dukkansu ma'aikata ne a kamfanin mujallar nan da ke Kano mai suna Nigerian Outlook.
Shi dai Musa, ya taba zama jigo wajen ciyar da mujallar Fim gaba. Ya kasance marubuci na musamman a mujallar, inda ya rika amfani da sunan Kallamu Shu'aibu. Da wannan sunan, Musa ya yi hirarraki da ''yan fim manya da kanana, kuma ya zakulo labarai wadanda suka kara tabbatar wa jama'a cewa Fim ce mujallar karantawa in dai ana son sanin abin da ake ciki game da harkar fim. Musa ne ya yi manyan hirarraki wadanda aka buga a bangon mujallar, kamar su hira da Ibrahim Mandawari, Abida Mohammed, Aminu A. Shariff (Momo), Umar yahaya Malumfashi, da kuma hirarmu ta farko da marigayiya Balaraba Mohammed. Shi ne ya yi hira da Jamila Haruna Yakasai da Halima Adamu Yahaya a kan mutuwar aurarrakinsu, kuma shi ne ya tattauna da Bashir Bala Ciroki da amaryarsa lokacin da suka yi aure. Hirarsa ta karshe da muka buga a bangon wannan mujallar ita ce wadda ya yi da Hadiza Kabara lokacin da ta fara bullowa, har muka sanya ta a bangon mujalla tare da taken "Hadiza Kabara: Sabon Yayi." Ya halarci dukkan daurin aure ko wani taro da aka yi na 'yan fim a lokacin.
Wannan tarayya da ya yi da 'yan fim ta sa, duk da yake ba ma'aikacinmu ba ne a lokacin, kusan kowa a tsakanin masu harkar fim a Kano ya san shi. Ya yi kyakkyawar hulda da mutane irin su Malam Isa Bello (Ja), Malam Umar Yahaya Malumfashi (Bankaura), Hajara Abubakar (Dumbaru), Ishaq Sidi Ishaq, Nura Ilu Dambazau, da sauransu.
Babban abin bakin cikin da ya samu Musa a tarayyarsa da 'yan fim shi ne wani hari da wani furodusa ya kai masa har ya nemi ya halaka shi don mun buga wata wasika a mujallar.
Musa dai dan'uwa ne kuma aboki ga mawallafin Fim, Malam Ibrahim Sheme. Haifaffen Karamar Hukumar Faskari cikin Jihar Katsina, Musa ya yi makarantar sakandare a Shinkafi cikin Jihar Zamfara, sa'annan ya yi karatunsa na gaba a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya sami digiri a fannin hulda da kasashe (International Studies). Kafin zuwansa mujallar Nigerian Outlook inda ya yi aikinsa na karshe, ya taba zama ma'aikacin kamfanin mujallun Hotline da Rana, inda ya nuna gogewa wajen yin rubutu da Hausa da kuma Ingilishi.
Musa mutum ne mai raha. Da wuya ka zauna da shi bai ba ka dariya ba. Mutane irin su Hajiya Balaraba Ramat Yakubu sukan kalle shi su ce, "Karamin Sheme kenan!"
Ya rasu yana da shekara 37 da haihuwa, ya bar matarsa Rabi da 'ya'ya uku mata, mahaifiyarsa, da kannensa.
Jama'a da dama daga jihohi daban-daban sun je ta'aziyyar rasuwarsa. Su ma 'yan fim, da yawansu sun je gidansa ko ofishin mujallar Fim sun yi gaisuwa. Sun hada da Hafizu Bello, Isa Ja, Umar Yahaya Malumfashi, Saratu Gidado, Mika'il Hassan (Gidigo), Fatima Ahmed, da Hajara Dumbaru wadda ta dinga rusa kuka da ta shiga falon gidansa da ke Gyadi-Gyadi, Kano, da sauransu da dama.
Shi kuma Alhaji Bashir Zakari, ya sami horaswa da kwarewa a matsayin furodusan talbijin. Ya yi aiki a Hukumar Watsa Labarai ta kasar Ghana (Ghana Broadcasting Corporation), da Hukumar Watsa Labarai ta Arewacin Nijeriya (BCNN), da gidan talbijin na NTA Kano inda ya kai mukamin darakta kafin ya yi ritaya.
Daga bisani Alh. Bashir ya yi aiki kamfanonin talbijin da na shirya finafinan Hausa kafin ya zama ma'aikaci a kamfanin mujallar Nigerian Outlook ta tsohon Janar Manajan gidan talbijin na Jihar Kano (CTV), Alhaji Wada Kachako.
Ya rasu yana da shekara 61, kuma ya bar mace daya, da 'ya'ya uku, da mahaifiyarsa da 'yan'uwansa. Dimbin jama'a daga ko'ina cikin sassaan kasar nan sun yi ta tururuwa zuwa gidansa da ke Hotoro don yi wa iyalansa gaisuwa.
Allah ya jikansu, ya sa Aljanna Firdausi ce makomarsu, amin.
An yabi Hindatu kan kokarinta na fadakarwa a shirin MAULA
FURODUSAR shirin Maula, Malama Hindatu Bashir, ta tafi gida tana murmushi a ran 6 ga Afrilu, 2002, bayan wani kasaitaccen biki da ta shirya don kaddamar da fim din nata ya samu nasara. A taron, an tara kudi kimanin sama da naira dubu dari tara. Kuma a ranar fim din ya fito kasuwa.
Hindatu Bashir, wadda kuma shahararriyar 'yar wasan fim ce, ta shirya Maula a matsayin fim dinta na kanta na farko, wanda ya sa ta shiga jerin mata da suka zama furodusa. Ta yi fadi-tashi matuka don ganin an kaddamar da shi.
An yi babban taron a otal din 'Tahir Guest Palace' da ke Kano da safe, sa'annan aka yi wani karamin taron kaddamarwar da dare.
A taron na safe, dimbin jama'ar gari da kuma wasu 'yan fim da dama sun halarta, ciki har da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Dr. Umar Ganduje, wanda ya wakilci Gwamna Kwankwaso domin ba ya gari. Babban mai kaddamar da fim din shi ne wani dan kasuwa, Alhaji Aminu Sulen Garo, sa'annan babban bako mai jawabi shi ne shugaban kwamitin magance matsalar barace-barace a Jihar Kano, Comrade Wada Waziri Ibrahim.
An fara taron da karfe 11:30 tare da jawabin Alh. Wada Waziri, wanda ya fara da nuna wa jama'a cewa ba a taba yin fim da Mataimakin Gwamna ya halarci taron fito da shi ba. Ya ce fim din Maula, wanda aka shirya don nuna illar barace-barace, wa'azi ne. Ya kawo hadisin da ya nuna cewa bara a addinance laifi ce, kuma ta saba wa al'ada.
Comrade Wada ya kara da cewa, "Duk kasar duniya ba a yin bara sai a nan kasarmu," kuma ya danganta matsalar ga al'ummar Hausawa. Ya ce, "Fim din ya zo daidai da tsarin gwamnatin Jihar Kano," kuma ya ci gaba ya nuna yadda kwamitin da gwamnati ta kafa don magance bara a karkashin Mataimakin Gwamna yake aikinsa da kuma kalubalen da yake fuskanta.
Comrade Wada ya yabi Hindatu kan kokarinta na yin fim din, daga nan ya yi kira ga sauran masu shirya finafinai da su ci gaba da yin finafinai na fadakarwa irin wannan.
Mai jawabi na biyu shi ne Alhaji Aminu Sulen Garo. Shi kuma ya nuna cewa Musulunci ya hori mutane da su yi "ko da sana'ar icce ne da su tsaya neman-na-Bello Badun." Ya ce yanzu ya dace a fadakar da jama'a a kan illolin maula.
Mai kaddamarwar ya yaba wa furodusar kan gagarumar gudunmawar da ta bayar wajen fadakar da jama'a illolin da ke akwai cikin maula.
"Duk lokacin da na ga wasan kwaikwayo, nakan ji dadi kan zaburar da mutanenmu suka yi na maye gurbin finafinan kasashen waje," inji shi. "Yanzu maimakon mutanenmu su ce 'Allah ya kai mu Indiya ko a buhun barkono ne' sai su ce Allah ya kawo su Kano don su gane wa idonsu yadda harkar take."
Alhaji Aminu ya yi kira ga 'yan fim su kare al'adu da addininmu. Ya kuma yi tsokaci kan cewa lokacin da waka da rawa ke ci a cikin fim ya yi yawa, sa'annan sai ka ga saurayi ya yi ado fes da ta-zarce, to amma bai sa hula ba.
A nasa jawabin, shugaban gidan Rediyon Jihar Kano ya yi alkawarin za su taimaka wa 'yan fim a duk lokaci da aka bukace su.
Da jawabi ya kawo kansa, Mataimakin Gwamna, Dokta Ganduje, ya bayyana jin dadi kan kokarin da Hindatu ta yi na fadakar da jama'a kan illar bara da maula, ya ce wannan ya yi daidai da kudirin gwamnatin Jihar Kano. Ya yi bayani a kan kokarin da gwamnatin take yi na magance bara wadda matsala ce da ta fi karfi a Jihar Kano a duk fadin Nijeriya.
Daga nan wasu 'yan fim (Shehu Hassan Kano, Nura Imam, Amina Garba, Hajjo, da sauransu) suka gabatar da wani takaitaccen wasan kwaikwayo wanda ke nuna illar bara.
A jawabinta na godiya, Hindatu Bashir ta ce wannan rana ta kasance daya daga cikin ranaku mafi farin ciki a gare ta. Ta ce ta shirya fim din ne domin ta ba da tata gudunmawar ga kokarin da gwamnatocin Arewa ke yi na kawo karshen tumasanci. Ta gode wa manyan baki, da mahaifiyarta, da 'yan kwamitin shirya kaddamarwar, da kuma Dan'azumi Baba saboda shi ne silar shigarta harkar fim.
Alhaji Aminu Sulen Garo dai ya ba da kyautar N200,000 lakadan; Gwamnatin jiha ta ba da N100,000; Hajiya Maryam Abacha ta aiko da N50,000; Galadiman Kano ya aiko da N100,000, kuma Kungiyar Mata Furodusoshi ta ba da N10,000. An ci gaba da tara kudi har suka kai N420,000 tsaba, kuma an lissafa kudin alkawurra N350,000.
Comrade Wada Waziri Ibrahim ya yi wani jawabi a karshe a kan batun kin sanya hula da matasan Hausa suke yi, yana mai kwakkwarar suka a kan wannan dabi'a wadda ya ce ta saba wa al'adun Hausawa.
An tashi taro lafiya da karfe 1:05 na rana.
Ana nuna wa 'yan fim soyayya a Saudiyya
Sakataren Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kano, Alhaji Baba Sheriff, ya ce a kasar Saudiyya masu kallon fim suna nan suna jiran fitowar shirin nan mai suna Ibro Osama, wanda camama ne. Ya bayyana haka ne a hirarsa da mujallar Fim bayan dawowarsa daga aikin hajji na bana Baba Shariff, wanda ko a bara ma ya je Makka, shi ne jami'in alhazai na Karamar Hukumar Dala ta Jihar Kano (wato Centre Officer).
Alhaji Baba ya shaida wa wakilinmu cewa dan fim zai tabbatar da ana sha'awarsa da zaran ya dira kasar Saudiyya. Ya ce jama'a da yawa sun yi ta zuwa wurinsa a unguwar da ya sauka mai suna Shahr Sittin. "Duk wadanda kan zo wurinmu suna zuwa suna yi mana tambayoyi kan wasu ji-ta-ji-ta da suke ji dangane da 'yan fim. Ni kuma ina ba su amsa da kuma gaskiyar al'amarin," inji shi.
Ya kara cewa duk inda za su sayi abinci ko wani abu akan nuna masu karamci sosai. Abin da ya fi ba shi mamaki shi ne yadda Hausawa mazauna Saudiyya suka san labarin fim din Ibro Osama "kuma duk masu zuwa wurinmu suna tambayarmu wai yaushe Ibro Osama zai fito?"
Baba ne mai kamfanin 'Fatima Production' wanda ya shirya wasu finafinai da suka hada da Surukin Zamani, Haka Allah Ya So, da kuma Samodara. Yanzu kuma sabon fim dinsa mai suna Hakki yana nan tafe wanda za a yi karkashin aikin darakta Tijjani Ibraheem. A cewarsa, kamfaninsa din ne ya fara saka Abida Mohammed a fim inda ta fara fitowa cikin wani fim da suka shirya mai suna Zato.
Da ya juya kan marigayiya Balaraba, Alhaji Baba Shariff ya yi mata addu'ar samun gafarar Allah madaukakin Sarki. Ya ce, "Balaraba yarinya ce mai halaye nagari. Allah ya sa sauran mata su yi koyi da ita".
Baba Shariff ya yiaiki tare da Balaraba inda suka shirya fim din nan mai suna Amalala.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|
|
|
| |