Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 30   Yuni 2002


BABBAN SHAFI
RA'AYI
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) 
Rayuwarmu
Duk Sun Yi Aure
Malam Zurke
Ra'ayin Mujallar Fim
Bukukuwa
Sauran Labarai
Ra'ayi Ba Gaba ne
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


An karrama su Dumbaru a Misau

Dumbaru
Hajara Abubakar (Dumbaru
WATA kungiyar shirya wasan kwaikwayo a garin Misau cikin Jihar Bauchi mai suna 'Dan-Buram Memorial Drama Association,' ta karrama wasu fitattun 'yan wasan Hausa da katin shaidar shahara a fagen fim. Wadanda aka karrama a wani bikin bada kyaututtuka da aka yi a ranar 27 ga Afrilu, 2002 sun hada da Hajara Abubakar (Dumbaru), Alh. Musa Na Sale, Shu'aibu Katakore da kuma Labaran Dan Wanzam.

An shirya bikin a gidan mai martaba Sarkin Misau. Wadanda aka karrama din sun isa garin ranar Jumma'a da dare. Kafin zuwansu kuwa dandazon jama'a sun zauna yini guda suna jiran isowarsu don su yi wata 'yar gala.

Ranar Asabar garin ya cika makil da jama'a da suka rika kwararowa daga garuruwa da suke makwabtaka da Misau.

Mujallar Fim ta sami jin ta bakin Dumbaru wadda ta nuna matukar farin ciki da godiya da wannan karramawa da aka yi masu. Ta ce, "Wanda ya nuna yana sonka daga cikin mutum dubu ai mai kaunarka ne." Ta kuma gode wa jama'argari wadanda suka nuna masu matukar kauna.

A wurin karrama 'yan wasan an kuma rantsar da zababbun shugabannin kungiyar. Wani abin sha'awa kuma shi ne yadda shugabannni suka yi anko (yunifom) a wurin taron. Wadanda aka karrama sun kuma kai ziyarar ban girma ga mai martaba Sarkin Misau. Can baya kuma a daren da suka isa Misau sun dan yi wani kwarya-kwaryan wasa inda har Dumbaru tare da wani dan kungiyar garin suka yi wakar "Uwargida Dumbaru" ta cikin fim din Juyin Mulki na 2.

An tara makudan kudi a taron kaddamar da Raddi

Daga SANI MOH'D MAIKATANGA, a Kano

A RANAR Lahadi, 28 ga Aprilu, 2002, aka kaddamar da fim din Hausa mai suna Raddi wanda masu kamfanin 'Jibiralawa Investment', Kano., suka shirya. An yi taron a karkashin jagorancin mai girma Shugaban Karamar Hukumar Fagge, Hon. Sulaiman Muhammmed Chamber, wanda Alhaji Shehu Sani, mai ba shi shawara a harkar siyasa, ya wakilta.

Taron kaddamar da Raddi
Shugaban kungiyar Furodusoshi mata, Hajiya Umma Ali (a hagu) tare da Sakataren Kungiyar, Hajiya Balaraba Ramat a wurin taron kaddamarwar
An kaddamar da fim din ne a zauren taro na 'Kofar Mata Indoor Stadium' tare da bude taro da addu'a daga bakin Malam Mohammed Maileda Singa. Sannan sai Alh. Mu'azzam ya ci gaba da gabatar da manyan baki. Bayan wannan sai tsohon shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kano, Auwalu Marshal, ya gabatar da sharhi a kan Raddi inda ya yi bayanin muhimmancin fim din Hausa da kuma jinjina wa masu wannan fim din. A cewarsa, kalmar 'raddi' tana nufin kamar wani abu ne da wani yake son daukar fansa a kan wani abu da ya faru ko kuma maida martani.

Auwalu ya yi fatan Allah ya taimaki kowa a cikin wannan harka kuma Allah ya kare mu daga makiyanmu.

Babban bako mai jawabi a taron shi ne shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kano, Alh. Ibrahim Mandawari, wanda bayan jawabinsa sai aka kaddamar da fim din na Raddi. Wakilin shugaban Karamar Hukumar Fagge, Alhaji Shehu Sani, shi ne ya kaddamar yayin da ya sayi kaset hudu a kan N50,000. Mandawari ma ya sayi kaset daya a kan N1,000 sai Kungiyar Mata Furodusoshi ta sayi kaset a kan N1,000, sai Hajiya Umma Ali ta sayi kaset a kan N1,000. Haka dai aka yi ta sayen kaset din inda a karshen taron aka tara kudin da ba su gaza N500,000.

Manyan mutane da kuma shugabannin 'yan fim na Kano sun samu halarta taron. Sun hada da Muntari Kwanzuma, Umma Ali, Mu'azzam, Mandawari, Auwal Marshal, Sir Hafizu Bello, Zilkifilu Muhammad, Tijjani Faris, Alhaji M. Mamud wakilin shugaban karamar, Alhaji Badamasi, Alhaji Gali Ibrahim Shehu, da Alhaji Mansur Isa Yakasai.

Manufar hukuma ta kare al'ummarmu
Cewar A.A. Kurawa

Malam A.A. Kurawa
Malam A.A. Kurawa, Daraktan Sashen Habaka shirin fim a Hukumar tace finafinai ta jihar Kano
CAN a 'yan watannin baya wannan mujallar ta tattauna da darakta mai kula da sashen habaka shirin fim a Hukumar Finafinai ta Jihar Kano, ALHAJI ABDULKADIR ABUBAKAR KURAWA, wanda aka fi sani da sunan A.A. Kurawa. A hirar, mun waiwaye shi kan al'amura da dama da suka jibinci aikin hukumarsa, da dangantakar hukumar da masu shirya finafinai.

Matsayin Kurawa a hukumar ya ba shi damar kasancewa daya daga cikin manyan masu fadi-a-ji a harkar fim na Hausa, ta yadda duk abin da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta yi ko ta zartar za a ce shi ne ummulhaba'isi, ya-Allah abin mai dadi ne ga 'yan fim ko marasa dadi.

Malam Kurawa yana da tsananin masaniya a kan harkar fim, domin ya dade a kan aikin jarida, musamman bangaren aikin talbijin da na rediyo. Mukami na karshe da ya rike kafin zamansa darakta a wannan hukuma shi ne rikon da ya yi a matsayin shugaban Hukumar Rediyo da Talbijin ta Jihar Kano. (Dubi tarihinsa a nan kasa).

Editanmu, ASHAFA MURNAI BARKIYA ne ya tattauna da shi a ofishinsa. Ga abin da ya samu daga hirar:

Fim: Kwanakin baya hukumarku ta yi wata kakkabar 'ya'yan-kadanya inda ta rika bi tana kulle kantunan masu sayar da kaset. Wace nasara kuka samu kan wannan samame da kuka yi?

KURAWA: Aikin Hukumar Tace Fim ta Jihar Kano ba wai ya tsaya kan tace finafinan Hausa kadai ba ne. Doka ta ba mu damar duba duk wani irin fim da aka shigo da shi Jihar Kano. Aikinmu ne mu tabbatar duk wani fim bai saba wa addinin Musulunci ko al'ada ba. To duk kantrin da ka ga mun rufe ya saba wa doka ne. Gwamnati ce ta nada alkalin tafi-da-gidanka, da mai gabatar da kara da kuma dan sanda. Duk kantin da aka je za a tambayi ko yana da izinin sayar da kaset? Wadanne irin finafinai yake sayarwa? Shin hukuma ta yarda? Idan ya ce e, to ina shaida? Idan babu kuwa sai hukunci ya hau kan mutumin.

FIM: Wasu sun ce ba ku shiga cikin Sabon Gari inda kabilu suke ba. KURAWA: Ai an shiga Sabon Gari sosai; duk yawanci finafinan Inyamurai ne muka kama. Da dama daga cikinsu kai din nan ba za ka yarda ka sa a gida ka kalla ba. Mun kama da yawa, an kuma yanke wa wanda aka kama hukuncin dauri ko tara. Su kuma finafinan duk an kona su a kotu a gaban alkali gaban dimbin jama'a.

FIM: Kamar wadannne finafinai ne aka kona?

KURAWA: Ga wasu nan a rubuce. Akwai: The Adulteress, Osama Bin La 1&2, Outkast, Shattered Home, Married Woman, Say My Name, Lady Bianca, da Love Affair. Akwai kuma Ashawo, Ashes, The Prostitute, Shameless Woman, da Stubborn Grasshopper. Kuma kowanne da ka ji na lissafa an kama daruruwansu. Ka ji kadan daga cikin tasirin da wannan aiki ya haifar

FIM: 'Yan fim da yawa na kuka cewa kuna tilasta su biyan kudin rijista N5,000 kowane daya. Shi ya sa ma wasu ke cewa ai wannan wani yunkuri ne na neman dakushe kaifinsu. Me za ka ce?

KURAWA: Na yi manaki da na ji wannan magananr. Ba gaskiya ba ne. Yau na fara jin ta daga bakinka. Irin wannan ba ta taba fitowa daga ofishin Babban Sakataren wannan hukuma ba. Mutane su fahimta cewa harkar kudi ba wai damun gwamnati ta yi ba dangane da wannan harkar ta shirya finafinai. Tace finafinai don tabbatar da nagari a cikinsu shi ne aikinmu.

FIM: 'Yallabai, mu fada kan batun hana mace ko mace da namiyi rawa a cikin fim. Wasu na ganin tilas sai furodusoshi da daraktoci sun taimaka maku sa'annan abin zai yi tasiri sosai...

KURAWA: Su taimaka mana ko dai su taimaka wa kansu? Idan an kama fim dinka ai ka san hukuncin da za a yi maka. Ni ina ba su shawara su fito da wata hanyar da finafinansu za su karbu, ba tilas sai da rawa da waka ba. Ai da ba a yi, ko?

FIM: Su ma gidajen kallon bidiyo, musammmam na Video Centres, mun ga suna ta je-ka-ka-dawo a nan ofishinku kwanan baya. Shin me suka yi?

KURAWA: Na ji dadin wannnan tambaya. Ka san Majalisar Dokokin Jihar Kano ce ta kafa mu, shi kuma mai girma Gwamna ya sanya wa dokar da ta kafa mu hannu. Daga cikin ayyukanmu akwai kula da gidajen sinima, gidayen bidiyo da kuma na kallon bal (kwallo). Ba a yarda kana daya daga cikin wadannan ukun ba sai da izini. Kuma ba za ka hada biyu ba sai da wani izinin, tilas sai an ba ka lasisi. Hukuma ce ta nemi su zo su yi rijista da ita don a san guda nawa muke da su a jihar nan, kuma a san inda suke don a san abin da suke nuna wa jama'a.

Kafin mutum ya bude gidan kallo dole ne ya fara zuwa wurinmu mu ba shi takarda, shugaban karamar hukumarsa ya sa hannu, Hakimi ya amince, ya sa hannu, haka DPO na 'yan sandan yankin ya amince. Laifi ne wanda aka bai wa takardar izinin nuna bal ya rika nuna fim. Ina kuma yin kira ga jama'a su rika kai rahoton duk gidajen kallo da ba su bin ka'ida. Su kansu 'yan Hisba ya kamata idan sun ga gidan da ake nuna kallo su tambaye su ko suna da takardar izini? Idan ba su da ita, to sai 'yan Hisba su yi masu nasiha kuma su ba su shawara cewa su hanzarta su sami lasisi daga hannunmu.

FIM: Kai da wasu manyan 'yan fim kun san juna tun kafin yanzu. Shin kamar su wanene suka taba yin aiki a gidan talbijin a karkashinka?

KURAWA: Ai suna da yawa sai dai in fadi wasu: Ka ga dai Ibrahim Mandawari, Tijjani Ibraheem, Ishaq, Hajara Usman, Yakumbo, Kabiru Maikaba, Umar B. Hankaka, Danmagori, Mohammed Kabara, Shariff Ahlan, kai da yawa sosai. Kuma suna ba ni girmana, ni kuma na ji dadi don suna ci gaba sosai.

FIM: Wata biyu da suka wuce kun kira masu ba da umarni a fim, wato daraktoci, kuka ce su zo suyi rijista . Mun ci karo da takardar da shugaban kungiyar daractocin ya rubuto maku yana cewa ba za su yi rijista da dai-dai ba. Shin ina aka kwana?

KURAWA: Ai babu wanda ya isa Gwamnati ta ce ya zo ya yi abu ya ce ya ki. Mun zauna da su, (mun ga) akwai rashin fahimta don ba su fahimci abin da muka ce masu ba ne shi ya sa suka rubuto waccan takarda. Kuma da suka ce haka ai har yau (5/3/02) kungiyar tasu ba ta zo ta yi rijista da mu ba. Su fahimta fa, wannan hukuma riga da wando ce gwamnati ta dinka ta ba su ta ce su sanya. Ya kamata su rika tambaya su fahimci abu sosai kafin su rika zartar da wani abu.

Wani abu shi ne daga furodusoshin, daraktoci da 'yan wasan duk babu hadin kai da za su yi tutiya da su. Me ya sa har yanzu kan soyayya suke yin fim? Me zai hana su rika yi kan wasu al'amuran da suka shafi jama'a ko kasa, ko addini da makamantansu? To duk abin da babu hadin kai ci-gaba ba zai yiwu ba. Ga Inyamurai nan suna yin finafinan da ke nuna batanci kanmu. Me ya sa (na Hausa) ba za su rika haduwa suna yin wani wanda zai nuna wa jama'a yadda muke ba kamar yadda su Inyamurai ke nunawa ba? Ya kama mu ajiye wani muhimmin ginshiki don 'yan baya - 'ya'yanmu, jikoki da kanne.

FIM:Mu koma batun rufe kantuna...

KURAWA: (ya tatse tambayar) Kai kana ta maganar kantuna! Ba fa su kadai muka zura wa idanu ba. Kwanan nan (28 ga Fabrairu da 1 ga Maris 2002) mun rufe Raypower, DSTV, da Hashtronic, ba mu bude su ba sai da suka zo suka yi rijista da mu don mu san irin ayyukansu.

Mun gode.

KURAWA: Ni ma haka, na gode. Madalla.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin