|
Lalacewa ta yi yawa a harkar fim - Tasalla
Daga SHAFI'U MAGAJI USMAN a Kaduna
YAR wasan nan mai suna Fatima Ibrahim (Tasalla) ta bayyana goyon baya ga sharhin da mawallafin Fim, Ibrahim Sheme, ya yi a watan Maris wanda ya jawo muhawara don ya soki wasu 'yan fim.
Fatima, wadda ta ce yanzu ta kada akalar harkokin fim dinta zuwa ga finafinan Musulunci, ta ce ita ba ta ga abin kai ruwa rana ba dangane da tsokacin da mai sharhin ya yi ba "don ya fadi gaskiya."
Idan kun tuna, Sheme ya soki wasu gungun 'yan fim da suka maida iskanci abin ado, wanda hakan yana bata sunan masu gaskiya a harkar. Fitowar sharhin ta jawo ka-ce-na-ce har wasu shakiyai suka yi amfani da sharhin suna sukar Fim da shi Sheme.
Tasalla, wadda ta fito a finafinai irin su Linzami Da Wuta, Sartse, Fa'idah, Sadiqa da kuma wasu finafinai guda bakwai na rundunar 'Yan'uwa Musulmi wadanda yawanci ba su fito ba tukuna, ta kada baki ta ce, "Ko me mutum zai fada ya fada don Allah ko ya yi don Allah. Na san ko a gidan giya za a samun nagari tunda kafiri yana haihuwar Musulmi. Don haka a duk inda aka tara jama'a dole a samu marasa kyau. Kamar yadda Annabi (SAW) ya fada mana, idan marasa kyau sun rinjayi masu kyau, suna iya sanya a kalli duk taron a marasa kyau. Haka kuma idan masu kyau suka rinjayi marasa kyau za a kalli duk jama'ar a matsayin masu kyau.
"A film industry lalacewa ita ta yi rinjaye. Babu mamaki da ake kallon dukkan 'yan fim a matsayin 'yan iska. Ni zan iya alfahari da kaina cewar a film industry babu wani namiji da wata harkar banza ta hada ni da shi; in kuma akwai ya fito ya fada wa duniya. Don haka ni ba na damuwa don an kira mu matan fim a matsayin karuwai tunda na san na tsare mutuncina."
'Yar shekaru 24 da haihuwa wadda kuma ta taba yin aure, Fatima ta kara da cewa a al'amarin lalacewar mata a harkar fim ta fi zargin su takwarorin nata mata, saboda wani al'amari ne da babu tilas a cikinsa. "Duk wacce ta yi nufin ta kare mutuncinta har kafin ta samu aure za ta iya. Amma saboda kwadayin abin duniya sai ka ga yarinya ta yi kaurin suna wajen aikata masha'a don kawai a ce ta samu kudi ko ta yi fice a manyan finafinan Hausa."
Fatima dai 'yar asalin Jihar Jigawa ce wadda ta yi dukkan rayuwarta a Kano. Ta yi karatun firamare a Kano, sakandae a Kazaure da Garki, kuma a yanzu tana karatun difloma a makarantar koyon aikin kiwon lafiya ('School for Health Technology') a Kano inda take nazari kan lafiyar muhalli ('Community Health' ).Tana yin wannan karatu ne a karkashin gwamnatin Jihar Jigawa inda take aiki.
A karshen tattaunawarta da wakilinmu, Fatima ta shawarci furodusoshi da daraktocin finafinan Hausa da su ji tsoron Allah wajen sanya 'yanmata a finafinansu ba tare da samun amincewar iyayensu ba. "In kuwa ba haka ba, to akwai fa ranar kin dillaci...," inji ta.
Fim din Kaddara ya saba wa Musulunci
In ji Dan Iya
FURODUSAN nan dan bagu mai suna Yakubu Lere ya sake tsokano muhawara kan dacewar finafinansa yayin da ya fito da wani wasa mai suna Kaddara, wanda masana suka nuna cewa sam bai yi wa addinin Musulunci adalci ba.
An kaddamar da fim din ne a dakin taro na Gidan Arewa da ke Kaduna a ran 1 ga Yuni, 2002.
Mai Girma Hakimin Kabala kuma Dan Iyan Zazzau, Alhaji Yusufu Ladan, ya jagoranci masu cewa fim din bai dace da Musulmi ba domin sakonsa ya yi hannun-riga da kyakkyawar tarbiyyar Musulunci, inda ya ce a fim din an nuna wa duniya cewa Musulmi Hausawa ba su da tausayi kuma su kadai ne ke tafka barna da sabon Allah.
Hakimin, wanda tsohon ma'aikacin rediyo ne da ya yi suna wajen tsara wasannin kwaikwayo na rediyo da talbijin irin su Gundumi Fasa Kwanya da Duniya Budurwar Wawa, shi ne Lere ya nada a matsayin wanda zai kalli fim din ya yi masa sharhi a taron kaddamarwar.
A sharhin da ya gabatar a gaban jama'a, Alhaji Yusufu Ladan ya kawo misalai da dama, kamar haka:
a fim din, an nuna matar da mijinta ya mutu ya bar ta da 'ya'ya, ita kuma ta kwanta ciwon ajali, amma ba a nuna wani mai taimakonta ba, kuma an nuna wa duniya ba ta da dangi kuma mijinta ba ya da su; masanin harkar fim din ya ce wannan da wuya ta kasance;
an nuna cewa a gidan haya matar take zaune, kuma gidan na Bahaushe ne, to amma duk da cewa tana cikin azabar ciwon ajali Bahaushen nan bai ji tausayin sallamarta daga gidan ba saboda ba ta iya biyan kudin hayar;
kuma duk mutanen da aka nuno sun kamu da cutar kanjamau ta hanyar iskanci Hausawa ne, kuma dukkansu Musulmi ne. Wannan, inji Dan Iya, zai nuna wa duniya cewa Musulmin Nijeriya Hausawa ne kawai ke yin iskanci. Masaraucin ya ba da shawarar cewa kamata ya yi a ce an yifyadar 'ya'yan kadanya, wato a nuno Musulmi da Kirista, wadanda su ne mazaunan Nijeriya.
Wani gyaran da Dan Iyan Zazzau din ya kawo shi ne inda ya ce an tsananta kwarai da aka nuna kabari ya maido gawar jarumin fim din saboda kasancewarsa mazinaci. Bugu da kari, inji shi, kuskure ne a gidan mutuwa na Musulmi a ce an barke da waka jim kadan bayan maigidan ya rasu.
Saboda haka ya ba da shawarar cewa kamfanin da ya shirya fim din, 'Lerawa Films,' ya yi kokari ya shirya kashi na 2 na fim din domin ya gyara kurakuran da ya tafka.
Da yake karin haske a kan yadda ya fahimci fim din, wani fitaccen furodusa da ya halarci taron daga Kano ya ce shi ma bai gamsu da sakon da fim din ya yi kokarin isarwa ba, musamman tunda ya saba al'adunmu da addininmu ta fuskoki da dama. Ya ba da nasa misalin, ya ce ba addini ba ne a nuno dan mamacin ya samu malamai domin su zo su binne gawar babansa amma suka ki a kan hujjar cewa uban fasiki ne, wai ya je ya nemi fasikai 'yan'uwansa su yi masa sutura. "Ka ga wannan ya nuna mana cewa kwata-kwata Lere bai da zurfin sani a addini, kuma bai yi bincike gun masana ba. Domin a Musulunci, ba a yarda da haka ba," inji furodusan, wanda yana da sani a hukunce-hukuncen addini. Ya kara da cewa, "Ba mamaki, da ma Lere bai yin binciken abin da ya shafi addini a fim dinsa. Ka tuna da muhawarar da fim dinsa Saliha? ya jawo?"
· Dubi sharhin Malam Zurke a shafi na 52 - Edita
Oscar ya lissafa rashin fa'idar dokar layin fitar da kaset
FURODUSAN fitattun finafinai su Dan Adam Butulu, Macijiya, da Abdulmalik, Prince Oscar Baker Anuruo, ya shiga sahun masu sukar tsarin bin layi wajen fito da finafinan Hausa kasuwa da ake aiwatarwa a yanzu. Ya ce, "Wannan tsarin ya gurgunta harkar shirya finafinan Hausa masu inganci da kuma dakushe aniyar masu sha'awar shiga harkar baki daya."
A wata hira da Fim ta yi da furodusan dan kabilar Ibo a ofishinmu na Kaduna, ya nanata cewar ya san an fito da tsarin ne bisa kyakkyawar manufa ta tallafa wa kananan furodusoshi, amma matsalolin da ke cikin tsarin sun fi fa'idarsa yawa. Kadan daga cikin matsalolin , inji shi, su ne rashin gata a tsakanin furodusoshi wanda ya haifar da rashin shirya finafinai masu kyau da inganci, kuma furodusa in bashi ya ciwo a banki ko wani wuri ya shirya fim, bai san ranar da fim din zai fita ba bare har ya biya bashin. Kuma ta yiwu furodusa ya shirya fim bana amma dokar bin layin ta hana shi fidda fim din har fiye da shekara guda, lokacin da yayinsa ya wuce.
"Ka ga kenan ya yi asarar abin da ya kamata ya samu in ya fito a lokacinsa," inji Prince Anuruo. Saboda haka, a ganinsa, ya dace a sake yi wa wannan tsari kallon basira a sake salo, kasancewar a duk inda yake da labarin masu harkar fim a duniya babu inda yake da labarin suna bin irin wannan layin.
Prince ya kuma tabo wasu al'umura masu dama a harkar shirya finafinan Hausa da suka hada da yadda ake samun matsalar nuna bambanci a tsakanin furodusan gari kaza da kuma na gari kaza ko furodusa dan wanan kabila da dan waccan kabila. A fahimtarsa, wannan matsalar ita ma ta taimaka gaya wajen rage bunkkasar finafinan Hausa. "Kamata ya yi mu dauki kanmu a matsayin iyali guda cikin wannan sana'a da kowa da inda ya sa gabansa," inji shi.
Oscar ya tabo batun karar da Yakubu Lere ya taba kai Ibrahim Mandawari, ya ce faruwar al'amarin shi ne abin kunya mafi muni da ya kasance a tsakanin furodusoshin finafinan Hausa. "A duk duniya haka bai faruwa wai furodusa ya kai karar dan'uwansa furodusa a kotu," inji shi.
Da yake tsokaci kan rawar da gwamnatoci ya kamata su taka a harkar shirya fim, furodusan ya ce da gwamnati, attajirai da malaman addini za su yi ruwa su yi tsaki a harkar shirya fim, to da an ilimintar da al'ummar Nijeriya kan illolin da suke faruwa kan yawancin rikice-rikicen da suke aukuwa na kabilanci ko na addini, al'amarin da har yanzu ya ki ci ya ki cinyewa. "Kuma in aka lura wasu 'yan kalilan din mutanen banza ne suke assasa fitinun saboda zalunci," inji shi.
Furodusan ya ce yadda harkar kasuwancin finafinan Hausa ke gudana, zai iya durkusar da furodusa komai karfinsa in ba a yi sa'a ba. Ya zargi diallalan kaset da cewa ko sun sayar da kwalin fim din mutun sai ya sha wuya kafin kudinsa su fita, sabanin yadda a kudancin kasar nan wasu finafinan ma 'yan kasuwan ne suke daukar nauyin shirya su ko su ba da gudunmuwa mai tsoka ga furodusa don a kammala aikin, kuma a karshe a rabu lafiya. Don haka ya yi kira da babbar murya ga 'yan kasuwar finafinan Hausa su gyara wannan matsala.
Mujalla ba ta wuce ni
-Dattijo
WANI dattijo dan shekaru 65 a duniya mai suna Malam Abdullahi Sarki Umar Warure ya kawo ziyarar jaje da ta'aziyya a ofishin mujallar Fim a Kano. Dattijon, wanda dan kasuwa ne a Kasuwar Sabon Gari, Kano, ya bayyana cewa dalilin ziyarar tasa shi ne don ya yi wa mawallafin mujallar, Ibrahim Sheme, jajen satar da aka yi a gidansa na Kaduna da kuma yin ta'aziyya dangane da rasuwar 'yar wasa Balaraba Mohammed.
"Bari ganina nan dattijo, to ni mujallar Fim ba ta wuce ni, kuma ina sayen kaset da kudina in kalla shi ya sa nake son 'yan fim da kuma mawallafin mujallar Fim," inji shi.
Da aka tambaye shi abin da ya sa yake sayen mujallar, sai dattijo Malam Abdullahi Sarki Umar ya ce, "Don ina karuwa ta bangaren labarai da kuma sadarwa duk a cikinta".
Amma babban abin da ya sa yake sayen kaset ya zama da iyalansa ya kalla, shi ne "Wani lokaci wani abin da ake koyarwa a fim yana yin daidai da koyarwar da muke yi a makaranta". Duk da haka ya yi kira da a rage yawan sa Turanci a cikin zantukan finafinai kuma a daina samun tsawon lokacin fitowa kasuwa tsakanin kashi na 1 na fim da kashi na 2.
A karshe ya ce shi bai ga aibin rawa da waka da ake sawa a finafinan Hausa ba matukar maza da mata ba za su hada jiki ba. Malam Abdullahi Sarki Umar ya kuma goyi bayan kafa Gidauniyar Tunawa da Balaraba Mohammed da aka yi.
Za a tsige Shugaban Furodusoshin Kaduna
Daga IRO MAMMAN a Kaduna
ANA nan ana zafafa wani tsohon yunkuri na ganin an tsige Shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kaduna, Malam Mohammed Adamu Bello (Ability), daga kan karagarsa bisa korafin cewa tun da aka zabe shi bai tsinana wa kungiyar komai ba.
Adamu Muhammad Bello (Ability), Shugaban Kungiyar Furodusoshi ta jihar Kaduna
| Wannan yunkurin ya samu ci-gaba ne a yayin da sakataren kungiyar, Malam Abubakar Ishaq, ya juya wa shugaban baya, ya shiga sahun gaba na 'yan tawayen kungiyar.
Kwanan nan, daga ran 29 ga Mayu, 2002, sakataren ya fara rarraba wata takardar kuka a kan shugabancin Ability, yana zarginsa da kasa kawo ci-gaba a kungiyar cikin watanni bakwai da ya yi yana mulki.An rarraba wannan takardar ga 'ya'yan kungiyar, ana neman su rattaba hannu a kanta don nuna amincewa da yunkurin tsige Ability shi kadai.
A takardar, wadda mujallar Fim tana da kwafe, Abubakar Ishaq ya rubuta cewa ana aiwatar da wannan yunkuri na yakice "baragurbi" ne don a "neman tsirar da mutunci da darajar kungiya a idon duniya." A cewarsa, salon shugabancin kungiyar na yanzu shi ne yake nema ya kai ta ya baro "kuma an yi ittifakin lallai shugaban kungiyar na yanzu shi ya zama uwa da makarbiya na wannan kungiya a yanzu saboda halayyarsa ta kankame komai daga shi sai kansa."
A cewar sakataren, shi Ability "tashi guda ya zama shugaban mulukiya, sai abin da ya ga ya masa daidai yake aiwatarwa dangane da harkokin gudanarwa na kungiyar, ba tare da yawun sauran 'yan kungiya ba. Haka tun lokacin da ya hau yau kusan watanni bakwai da zabensa ya rasa kawo wani abu na ci-gaba dangane da kungiyar."
Duk wannan, inji shi, ya sa "muka yanke shawarar jin ra'ayin 'ya'yan wannan kungiya." Ya kara da cewa idan "mutum ya ga murabus din shugaban shi ne mafita kamar yadda aka yi hasashe, to yana iya sanya hannu don ganin tabbatar haka. Haka ma in mutum ya ga cewar ya yaba da yadda ake gudanar da kungiya a yanzu to yana iya sa hannu domin ya tabbatar da shaidar haka, ka ga nan gaba ba zai kuka da kowa ba sai kansa."
A kasan takardar an bar fili inda mutum zai rubuta inda ra'ayinsa ya karkata, ko dai ya sa hannu a jerin 'yan tawaye ko kuma ya sa a jerin magoya bayan shugaba Ability.
Wakilinmu da ya tuntubi wasu daga cikin furodusoshin jihar ya fahimci cewa da wuya ne Ability ya kai labari domin, kamar yadda waninsu daga Zariya, inda Ability yake da zama, ya fadi, shugaban ya zama "kamar mujiya, shi kadai yake harkokinsa" saboda an kosa da shi.
Idan an tuna, kwanan baya sai da daya daga cikin 'ya'yan kungiyar, wanda kuma shi ne shugaban kamfanin 'El-Hadis Enterprises' da ke Zariya, kuma furodusan fim din Umar, Umar Isma'il Mamaya, ya yi kakkausar suka kan yadda shugabannin Kungiyar Furodusoshi ta jihar suke gudanar da jagorancin kungiyar. A hirar da ya yi da Fim ta watan mayu 2002, ya ce zaben-tumun-dare ne kawai aka yi. Shi din ma cewa ya yi tun daga lokacin da aka zabi shugabannin babu wani aiki na ci-gaba da suka yi wa kungiyar ko da na sisin-kwabo.
A lokacin, Umar ya nemi goyon bayan 'yan'uwansa furodusoshi a taru a tsige Ability.
Sakamakon wancan furuci da ya yi furodusoshi da dama a jihar sun ce in dai za a yi yunkurin, to suna ciki.
To amma wani furodusa mazaunin Kaduna ya ce takardar da Abubakar Ishaq ya sanya wa hannu tana nuni ne da "wayon a ci" na shi sakataren, domin idan har za a yi sauyi, to kada a cire Ability shi kadai, sai dai a rushekwamitin zartarwar baki daya a sake yin zabe. Ya ce Abubakar ya yi haka ne don a dora wa Ability laifi shi kadai, bayan kuwa "idan ma wata tabargaza aka yi, to kowane memba na Exco ba zai iya wanke kansa ba a dora wa mutum daya laifi."
"Ai Ability da aka ce ya ki yin komai kuma yana handama, ba aljani ko mala'ika ba ne; me ya sa aka kasa yin komai sai yanzu ake zare jiki?" inji shi.
Mujallar Fim ta ji daga wurin wasu 'ya'yan kungiyar cewa daga cikin zargin da ake yi wa Ability har da batun inda kudaden kungiya suke, kamar su kudin yin rijista da sauransu, da kuma daukar wasu matakai a madadin kungiya ba tare da ya kira taron kwamitin zartarwa ba. "Ya maida mu hoto kawai," inji wani memba na kwamitin tare da yin kyata. Ya kara da furta cewa, "Wallahi sai mun cire shi!"
Duk kokarin da wakilinmu ya yi domin ya ga Ability ya ci tura. Duk lokacin da ya je Hukumar Fasaha da Al'adun Gargajiya, inda yake aiki, sai a ce ya fita ko kuma ba a gan shi ba.
Sa'ida ta zo: Tace fim ba sai ka je Abuja ba!
Daga ASHAFA MURNAI BARKIYA a Kano
A KARSHEN watan jiya Hukumar Tace Finafinai ta Kasa (NFVCB) ta alkawarta fara tace finafinan Hausa a Kano. Wannan jawabi ya fito ne daga bakin Mista Bernard Boyit wanda shi ne babban jami'in tace finafinai a Abuja, wato Chief Film and Video Censors Officer, a wurin wani taro na 'yan fim na daukacin arewacin kasar nan da aka yi a Kano kwanan nan. An yi taron a gidan sinima na Marhaba a karkashin gayyatar Kungiyar Masu Shirya Finafinai ta Kasa reshen Arewa (MOPPAN).
Da mujallar Fim ta tuntubi Mista Boyit don yin karin bayani, sai ya ce, "Za a fara tace finafinan ne a Ma'aikatar Yada Labarai ta Jihar Kano" inda hukumar ta gwamnatin tarayya ta samu matsuguni kafin ta sami wurin tarewa na dindindin.
Wannan kalami na jimi'in ya faranta wa furodusoshi da dama rai a wurin taron har suka yi ta sowa da kuma tafi. Da ma an dade furodusoshi a arewacin kasar nan suna nuna matukar bacin rai dangane da zirga-zirgar da ake yi zuwa Abuja don tace finafinan Hausa.
Wani furodusa ya ce shi da ma ba son bin hanyar Abuja yake yi ba musamman saboda gwamnati ta yi watsi da ita babu gyara. Amma tunda za a rika tace mana finafinanmu a nan Kano ai shikenan mu nesa ta zo kusa," inji shi.
'Yan fim da yawa suna kokawa da bakar wahalar da sukan fuskanta idan sun je tace fim a Abuja. Baya ga nisa, akwai matsalar wurin kwana da tilas sai mutum ya kashe kudi ya kwana a otal. Kuma idan bai yi dace ba, sai an yi masa je-ka-ka-dawo. Wannan ya sa akwai 'yan fim da suka kware wajen karbar kwangilar kai fim Abuja domin tacewa. Akan ba su ladar wahalarsu abin da ya kama daga N5,000 zuwa sama ban da N10,000 da gwamnati ta kayyade domin biyan harajin tace kowane kaset daya na fim.
"Yanzu ka ga ba ruwana," inji wani sabon furodusa cikin annashuwa da bugun kirji, "da na gama editin sai kawai in hau acaba in tafi Information in bayar a tace a ba ni abina, ba kare bin damo."
Na daina shirya fim!
Daga Aliyu A. Gora II a Kaduna
FITACCEN furodusan nan da ke Kaduna, Malam Dan'azumi Usman (Kaftin Dafe-Dafe) ya zargi tabarbarewar shirin fim a Kaduna da cewa ya samo asali ne sanadiyyar gurbataccen shugabancin kungiyar masu shirin fim ta jihar. Dan'azumi, wanda shi ne ya shirya fim guda biyu, Dokin Kaddara da An Yanka..., ya bayyana wa wakilinmu cewa akwai matsaloli da yawa da yake son magana a kai, amma hakan ba za ta yiwu ba saboda ya taba takarar neman kujerar shugabancin kungiyar.
Duk da haka, ciyaman din na gidan wasannin gargajiya na Marhaba da ke Tudun Wada ya shawarci shugabannin da su duba su kuma yi gyara a kan yadda suke gudanar da shugabancin kungiyar.
Da wakilinmu ya tsokane shi a kan dalilin da ya sa furodusoshin Jihar Kaduna suka yi shiru da shirya fim ba kamar da ba, sai ya ce, "Ta wannan fanni, zan so in ba da hujja a kan abin da ke cikin zuciy ta ne, ban san saura ba. Allah ya sani ba rashin kudi ya hana ni ci gaba da shirya fim ba. Babbar matsalar da ni ta fi damuna, kuma na san akwai wasu wadanda yake da yawa abokaina ne wadanda mun tattauna wannan matsalar tare da su, ainihin abin da ke kwarar da mu masu shirya finafinai nan, na farko akwai rashin hadin kai a tsakaninmu ga baki daya a Arewa. Ta wajen fannin yadda za a tsara abubuwa, yadda kudin ka da za ka zuba jari ka kashe za su fito ka kuma fa'idantu da su. Domin kasuwanci ne, sana'a ce.
"Sannan na biyu, idan ka dawo kan wannan magana kamar a na Jihar Kaduna, alal misali, 'yan bidiyo kulob din nan, ka shirya fim dinka ka gama, madadin magidanta su je su saya a kasuwa, za ka ga akalla yanzu a Jihar Kaduna za a samu bidiyo kulob sama da dubu biyar inda za a fita kame, cutar da mu suke yi, piracy ne; madadin mutum ya je ya sayo fim din nan, sai mutum ya je ya yiwoi aro. Kai da ka shirya fim din za ka fa'idantu da abin da bai wuce naira arba'in da biyar ba a kan kowane kaset. Amma da mai bidiyo kulob ya je ya sayo fim dinka ya zo ya sake dubbing din su, unguwar nan gaba daya a zo ana mika mashi naira ashirin ashirin ko talatin ana karba. Ka ga kai ka cutu, shi ya fa'idantu, kuma mun yi mun yi don a zauna a tattauna yadda za a shawo kan wannan matsala abin ya gagara; ko wasukudi ne a rika sanyawa 'yan bidiyo kulob din nan su rika biya, abu ya faskara. Ka zo ka wahalu, wata biyu ko uku, ka kashe dubban kudadenka kimanin dubu dari uku, ka zo cinikinka ya tsaya a dubu dari biyu; shin riba ka ci ko faduwa ka yi?"
Dan'azumi ya kara da cewa matukar Kungiyar Furodushoshi ta Arewa ba ta magance wadannan matsaloli ba, to shi ba zai kara yin fim ba, domin a cewarsa asara ce kawai.
Wannan matsala ba Dan'azumi kawai ke kuka da ita ba, illa dai kawai sauran furodusoshi tsoron magana suke yi, domin manya-manyan furodusoshin Jihar Kaduna, duk sun kwanta, kowa ya karaya da shirin fim, 'yan wasa kuma sababbi da tsofaffi, sai gararamba kawai suke yi, ba su wannan ofis ba su wancan. Cikin furodusoshin da suka yi fim suka yi shiru akwai sakatare-janar na Kungiyar Furodusoshi ta Arewa, Abdullahi Maikano Usman.
Katsinawa za su kare mutuncin mujallar Fim
'YAN Kungiyar Makaranta Mujallar Fim da ke Katsina sun yi wani babban yunkuri domin tsara hanyoyin gudanar da aikace-aikacen kungiyar. A kwanakin baya ne suka gudanar da wani babban taro a ofishin kungiyar da ke unguwar Daki-Tara. A wurin taron, wanda wakilinmu ya halarta, 'yan kungiyar sun tattauna sosai kan alkiblar da za su tunkara wajen gudanar da ayyukansu.
Da farko shugaban riko na kungiyar, Malam Zaharaddin, ya yi jawabin maraba ga mahalarta taron, sa'annan ya gabatar da wakilin mujallar ga taron. Daga nan ya yi jawabi takaitacce kan nasarar da suka samu na hada wannan kungiya.
Shi kuwa sakataren riko na kungiyar, Malam Aminu Ahmed Muhammad, shi aka ba dama ya fayyace kadan daga kudirorin kungiyar. Bayan ya mike, sai ya fara gabatar da godiya ta musamman ga sabon furodusan nan, wato Abdu Boda, saboda ofishin da ya ba kungiyar aro don gudanar da ayyukanta kafin ta samu na kashin kanta.
Sakataren ya ci gaba da cewa: "Sanin kowa ne cewa mun kudiri kafa kungiyar nan ne musamman domin mu kare martabar mujallar Fim da ma'aikatanta. Za mu yi haka ta dukkan hanyoyin da suka dace, ba don komai ba sai don yadda mujallar ta zage damtse tana ba da gagarumar gudunmawa wajen bunkasa harkokin finafinanmu, da yadda kuma take kare martabar 'yan wasa da sauran masu sana'ar fim".
Haka kuma, sakataren ya jaddada cewa 'yan kungiyar za su zama tsintsiya madaurinki daya. Za su rika sada zumunta a tsakninsu, musamman idan abin farin cikin ya samu dan kungiya, za su hada taro don taya shi murna. Kuma ya nuna cewa za su rika kai ziyara a kai a kai zuwa ofishin mujallar domin sada zumunta, da kuma ba da shawarwarin da suka dace.
Taron ya samu nasara sosai, inda daga bisani wakilinmu ya nemi jin ra'ayin daya daga cikin membobin kungiyar, mai suna Dahiru Yusuf Kofar Marusa, inda shi kuma ya shaida wa wakilinmu cewa: "A gaskiya dukkanmu muna cikin farin ciki da kafa wannan kungiya, kuma za mu zage damtse, domin kara daukaka martabar mujallar Fim. Yana cikin kudirinmu cewa za mu sa kafar wando daya da duk wanda ya ce zai yi adawa da mujallar Fim".
An tashi taron lafiya, bayan an tanana ciki da kayan kwalama, sannan an dauki hotuna daban-daban domin tarihi. Nan gaba kadan za su fara raba fom ga duk mai son yin rijista, namiji ko mace.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|