Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 32   Agusta 2002
LABARAI


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
HIRAR MUSAMMAN
Wasiku
MU LEKA HOLLYWOOD
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
RA'AYIN MUJALLAR FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon Fim ta 31
Bangon Fim ta 30
Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Karkuzu ya soki lamirin gwamnatoci

Daga SHAFI'U MAGAJI USMAN a Kaduna

SHAHARARREN dan wasan kwaikwayo din nan mazaunin Jos cikin Jihar Filato, Alhaji Abdullahi Shu'aibu (Karkuzu-Na-Bodara), ya soki lamirin gwamnatocin kasar nan baki daya bisa abin da ya kira yadda har yanzu ba su san daraja da muhimmancin 'yan fim ba a harkokinsu na yau da kullum. Tsohon dan wasan wanda ya samu sama da shekaru 30 ana damawa da shi a wannan harka, ya amayar da abin da ke cikin zuciyarsa ne a Kaduna kwanan baya cikin wata zantawa da wakilinmu ya yi da shi a lokacin da ake bikin ba tsofaffin 'yan wasan Hausa lambobin yabo.

Karkuzu ya ce, "Akwai ban takaici yadda muka dauki tsawon shekaru masu yawa nuna fadakar da al'ummar kasar nan kan al'adu, addini, zaman lafiya da wasu manufofin gwamnati, amma har yan din nan gwamnati ba ta taba yi mana wani abin a zo a gani ba.

"Wani zai yi mamaki duk daukakar da na samu a wannan harka har yanzu ban da gidan kaina bare motar hawa," ya kara da cewa kuma haka al'amarin yake ga sauran takwarorinsa tsofaffin 'yan wasan Hausa.

Dan wasan ya ci gaba yana cewa ba shi da nufin hassada ko kyashi ga abin da yara 'yan fim suke samu a yanzu, har ya kada baki ya ce, "Mun zuba wa yara kwalta ne kawai a wannan hanya suna bi tiryan-tiryan suna samun daula, sabanin yadda mu muka bautu a sanan'ar ba tare da cin gajiyarta ba ta fuskar kudi."

Kwararren dan wasan ya bayyana matukar farin ciki dangane da lambobin yabo wadanda kungiya mai zaman kanta din nan 'Wisdom Promotion Project' tare da hukumar talbijin na kasa (NTA) ta Kaduna suka ba tsofaffin 'yan wasa irinsa. Ya kara da cewa wannan tunawar da aka yi da su wani abu ne muhimmi wanda ya kamata gwanatoci su rika aiwatarwa lokaci-lokaci.

Golobo ya kalubalanci mawakan finafinai

Daga SHAFI'U M. USMAN a Kaduna

ALHAJI Shehu Jibrin Talata-Mafara, shahararren tsohon dan wasa wanda jama'a suka fi sani da lakabinsa 'Golobo,' ya ce wake-waken da ake sanyawa a finafinan Hausa yanzu bai dauke su a matsayin wata hikima ko basira daga masu shirya finafinai ba. Don haka ya kalubalanci dukkan mawakan da masu shirya finafinan da in dai suna yi domin su amfanar da jama'a ne, to su komo ga wake-wake na al'adar Hausa, "ba su dinga koyi da munanan al'adun Turawa da Indiya ba."

Golobo, wanda ya yi fice tun fiye da shekaru 10 da suke wuce, ya bugi kirji ya kara da cewa, "Ni din nan in dai waka ce za a yi a fim, kuma waka mai ma'ana da karantarwa ga mai kallo, ban debe kowa ba, zan iya gogayya da dukkan wadanda suke tunanin su shahararrun mawakan finafinan Hausa ne na ko'ina. Hazikin dan wasan ya furta wadannan maganganun a cikin kakkausar murya a Kaduna cikin wata zantawa da wakilinmu ya yi da shi jim kadan da ba shi lambar yabo da wata kungiya mai suna 'Wisdom Promotion Project,' tare da hukumar NTA Kaduna suka ba shi kan gudunmawar da ya bayar ga harkar wasan kwaikwayo a tsawon rayuwarsa.

Alhaji Shehu, wanda a yawancin wasanninsa yakan fito ne a matsayin gabo ko sauna da makamantan haka, ya tabbatar wa wakilinmu cewa bai taba yin nadamar wannan matsayin da yake fitowa a fim ba. Ya ce kuma irin wauta da gabuncin da yake nunawa a fim ba irin tsarin rayuwarsa kenan a zahiri ba, yana yi ne don jama'a su koyi wani abu daga masu irin wannan hali. " Amma ga mai shakka ko tunanin ni wawa ne, ya bari wata larura ta hadu mu ya ga yadda zan kashe shi wajen ba da hujja," inji shi.

Dan wasan mazaunin Sokoto ya yi kira ga tsofaffin 'yan wasa da suka rage da su rika kusantar matasa wajen shiga finafinansuda kuma ba su shawarwarin da suka dace matukar finafinan ba su saba wa al'ada da addininmu ba. Don haka ma ya ce shi a shirye yake da ya amsa gayyatar duk wani furodusa da ya gayyace shi don ya yi masa wasa a fim dinsa, in dai fim din yana da ma'ana kuma bai saba wa addini ba. A karshe Golobo ya yi godiya ga wadanda suka ba su lambobin yabo, sa'annan ya yi kira ga takwarorin nasa da su hadu su shirya wani fim na musamman wanda zai sha bamban da finafinan da ake shiryawa a yanzu.

An karrama su Dumbaru

Daga Sani Muhammad Maikatanga

A RANAR Lahadi, 2 ga Yuni, 2002 wata kungiya mai suna 'Soli Drama and Cultural Promotion' da ke Na'ibawa, Kano, ta karrama wadansu 'yan fim, ciki har da 'yar wasan nan mai farin jini, Hajara Abubakar (Dumbaru). Wadanda aka karrama din tsofaffin 'yan kungiyar ne, kuma an yi taron a wajen da kungiyar take gabatar da wasanninta a unguwar ta Na'ibawa kusa da tasha.

Dumbaru
Dumbaru da Hajiya Tambaya rike da kyaututtukansu

An fara cika wajen domin ganin wannan karramawar tun da misalin karfe 4:15 n.y. 'Yan koroso sun cashe kafin a fara gabatar da abin da ya tara jama'a har wajen 5:30. Sannan aka gabatar da wata 'yar dirama. Bayan nan kuma aka fara biki inda aka fara kiran 'yan wasan daya bayan daya. An fara da Shu'aibu Dan Wanzan, sai Katakore, Hankaka, Cinnaka, Dandugaji, Golobo, Tambaya, Dumbaru, da dai sauransu. An kuma karrama wasu manyan mutane masu taimaka wa wannan kungiya, da kuma wasu kungiyoyin wasan kwaikwayo kamar su Janzaki.

Da wakilin mujallar Fim ya ji ta bakin sakataren kungiyar kan dalilin wannan karramawa, sai ya ce sun karrama wadannan muntane ne domin taimakon da suke yi masu da kuma gudunmuwar da suke ba su a duk lokacin suka nemi taimakonsu da kuma cancantarsu a kan hakan. Daga bisani shi ma a nasa bayanin, shugaban kungiyar, Malam Mohammed Danlami, ya fada a 'yar hirar da aka yi da shi lokacin da suka ziyarci ofishin wannan mujallar washegarn bikin karramawar, ya ba da takaitaccen tarin wannan kungiyar. Ya ce, "Wannan kungiya mai suna 'Soli Drama' an kafa ta ne a shekara ta 1991. Mun fara aiwatar da wasanmu da 'yan wasa kalilan har ta kai ta zama ta bunkasa. Katakore da Umar Sabo su ne muka fara wasa tare, sannan daga baya muka samu Shu'aibu (Dan Wanzan). A yanzu muna da mutane a kungiyar da Allah ya daukaka su ba su bar zuwa wajenmu ba. Shi ne mu kuma mu kayi alkawain karrama su inda har da wannan dan wasan da ke Sakkwato, wato Golobo. Mun gayyace shi kuma ya amsa gayyatar ya zo.

"Kafin wannan lokaci mun gabatar da wani wasa mai suna "Zaman Duniya" a gidan talabijin, kuma akwai wani fim da muke yi amma bai fito ba tukuna. Sannan wannan kungiya tamu tana alfahari kan abubuwan da take yi na fadakarwa, domin ya fi karfin wasa, da kuma bunkasa al'adun gargajiya na Hausawa da sauraransu."

Furodusan Kacibus ya yaba wa mujallar Fim

SHugaban kamfanin shirya finafinai na 'Kullum-Kullum Ventures' kuma furodusan fim din Kacibus, Malam Ado Mohammed Kullum-Kullum, ya yi yabo ga ma'aikatan mujallar Fim saboda yadda suke gudanar da ayyukansu wajen bunkasa harkar fim din Hausa.

Furodusan ya yi wannan yabon a ziyarar da ya kai wa mujallar a ofishinta da ke Gyadi-Gyadi, Kano, a ranar Asabar 2/03/02. Ya nuna farin ciki saboda irin karbar da editan Fim, Ashafa Murnai Barkiya, ya yi masa. Ya lura cewa Fim ce mujalla ta farko da ya gamsu da ayyakanta musamman wajen tantance sahihancin labari kafin ta buga shi da bai wa kowa damar fadin albarkacin bakinsa.

Dags karshe Ado ya yi godiya ga dimbin masu kallo saboda irin shawarwarin da suka ba shi da gyare-gyare da suka yi wa fim dinsa.

A nasa jawabin, Malam Ashafa ya ba shi tabbacin 'yan mujallar Fim za su ci gaba da aiki tukuru wajen ganin sun bunkasa harkar fim din Hausa a duniya baki daya. Daga karshe ya yi godiya ga furodusan saboda wannan ziyarar da ya kai masa.

Rikicin dillalai: Hukuma ba ta yarda da su Rabi'u B.K. ba

RIKICIN nan da ya dade da dabaibaye Kungiyar Dillalan Kaset ta Jihar Kano yanzu ya sami wata fuska, domin Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta shigo ciki tsindum inda ta ba da sanarwar cewa ba ta yarda da shugabancin sababbin shugabannin kungiyar ba. A cikin wata takarda wadda ta aika wa sababbin shugabannin, hukumar ta bayyana cewa ita har yanzu ba ta san da wani shugaba ba sai Alhaji Musa Nasale.

Kadan daga wani bangare na takardar ya nuna haka: "Hukuma ta sami labarin su Alhaji Sidi Garba, Rabi'u B.K. da Alhaji Bala Mohammed (ABM) suna kiran kansu shugabannin kungiyar masu ayar da kaset. To ina shaida maku cewa mu a nan kungiya har yanzu tana da rijista ne a karkashin shugabancin Alhaji Musa Nasale."

Can gaba kuma sai takardar, wadda Malam Sabo Nayaya ya sanya wa hannu a madadin Babban Sakataren hukumar, ta umarci su Rabi'u B.K. da su daina kiran kansu shugabanni.

Wannan takarda, wadda aka aiko da kwafenta ofishin mujallar Fim, a cikinta an gargadi su sababbin shugabannin da cewa "idan ba su daina kiran kansu shugabanni ba, to za a dauki matakan shari'a a kansu kamar yadda doka ta tanada."

Tuni dai aka aika da tardar a ofishin daraktan hukumar kungiyoyin game kai na Jihar Kano, Daraktan Bincike na 'yansanda da ke Bompai, na jami'an tsaro na ciki (SSS), daraktan Hukumar Adana Tarihi da Al'adu, kungiyar masu shirya finafinai ta jiha, da kuma ofisoshin mujallun da ke ba da labarin al'amurran da suka shafi finafinai.

An dai rubuta takardar mai lamba CB/ADM/18 a ranar 12 ga Yunin da ya wuce.

Mujallar Fim ta tuntubi mataimakin shugaban kungiyar dillalan, Alhaji Rabi'u B.K. Tashin farko B.K. ya ce, "Hukumar Tace Finafinai ba ita ta ba mu satifiket ba, saboda haka babu ruwanmu da ita, aikinta tace kaset kawai."

Wakilinmu ya nemi sanin shin wane bangare ne na shugabannin ke zaune a cikin harabar ofishin kungiya? Sai Rabi'u B.K. ya nuna cewa "wadancan ba za su ce ga ofishinsu ba. Mu kuwa ko yanzu ka je kan titin IBB lamba 12 za ka ga ofishinmu da alamar kaset na bidiyo da CD an zana a jiki. Ko shugaban kasa idan ya zo zai gani."

A karshe an tambaye shi ba ya ganin kamar zaman banza suke yi a cikin ofishin tunda wancan bangaren kungiyar har ya kai kansa gidan gwamnati? B.K. cewa ya yi, "Maganar sun je gidan gwamnati ai wannan shirme ne. Wannan ai kamar siyasa ne kawai suke yi." Sai ya kara da cewa don sun je gidan gwamnati ziyara ai ba shi ne sun hambare mu ba."

Furodusoshin jihar Kaduna sun tsige shugabanninsu tare da yin 'Allah ya isa!'
Daga ALIYU A. GORA II a Kaduna da Zariya

KAMAR yadda mujallar Fim ta ruwaito a watan jiya cewa akwai alamun za a rushe shugabannin Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kaduna, to hakan ta tabbata domin kuwa yanzu an yi waje-rod da shugabannin wadanda ke karkashin jagorancin Malam Adamu Bello 'Ability.' Hakan ya biyo bayan zargin da wasu 'ya'yan kungiyar suka yi wa Ability da aikata laifuffuka guda tara, wadanda a cewarsu sun taimaka wajen tabarbarewar shugabanci da kuma ci-gaban kungiyar.

A ranaR 23 ga Yuni ne 'ya'yan kungiyar suka yi taro na farko a kan maganar, wanda aka yi a ofishin Alh. Tukur Aliyu, shugaban 'Capital Films Production' a Zariya. Akalla furodusoshi 14 suka halarci taron, aka kuma gabatar da laifuffukan da ake zargin shugaban da aikatawa.

Sakataren kungiyar na lokacin, Abubakar Isah Abdullahi, shi ya karanto laifuffukan kamar haka:

1. kungiyar tana zargin Ability da rike kayan kungiya da ba su shafi ofishinsa ba;

2. ya hana zababbun shuwagabanni gudanar da aikin da ya rataya a wuyansu;

3. rike kudin kungiyar ba ta tare da mika su ga ma'aji ba;

4. mallakar takardun kungiyar ba tare da mika su ga sakataren kungiyar ba;

5. kin halartar taron kungiyar da gangan ta tare da wani kwakkwaran dalili ba;

6. zagin uwar a kungiyar a wani taro da aka taba yi a ofishin Ashiru Sani Bazanga;

7. hana 'ya'yan kungiyar gudanar da kowane irin aiki;

8. kulla makarkashiya da mutum biyu a matsayin furodusoshi a karkashin kamfani daya don su zabe shi a matsayin shugaban kungiyar a ranar da aka yi zabe, da

9. rashin sanin halin da kudin kungiya ke ciki.

Ability bai zo taron ba, don haka 'ya'yan kungiyar sun amince da a rubuta takarda dauke da zarge-zargen a aika masa, a kuma ba shi kwana bakwai don ya samu damar zama a gaban kungiyar ya kare kansa.

A taron da aka yi a ranar 30 ga Yuni Ability ya samu halarta. A kan hukuncin da aka yanke a taron da ya gabata ya ce ba a ba shi takardar ba, kuma ko wannan zuwan ma da ya yi Alh. Tukur ne ya gayyato shi da baki ba uwar kungiyar ba.

Ability ya ce a shirye yake da ya amsa duk wata tuhuma da ake yi masa. Shugaban taron, Abdullahi Maikano Usman, tare da amincewar 'ya'yan kungiyar, sun umurci Ability da ya je ya kammala duk wasu shirye-shirye da yake bukata cikin kwanan bakwai, sannan ya dawo ya kare kansa.

Ranar Asabar, 8 ga Yuli aka sake taruwa a ofishin Alh. Tukur don sauraren jawabin da Ability zai gabatar na kare kansa. Furodusoshin da suka halarci taron sun hada da Abdullahi Maikano Usman, wanda ya shugabanci taron; Alh. Tukur Aliyu, Abukakar Isah Abdullahi, Nasiru Danmaliki, Aminu Shehu, Galin Money, Dan'azumi Usman, Magaji Sulaiman, Muhammad Murtala Aminu, Abdullahi Yahaya Maizare, Nuhu B. Imrana, Jibril Dayyabu, da sauransu.

Ability ya yi kokarin ya kare kansa, amma abin ya ci tura, domin sai da aka zo maganar kudi kura ta tashi. Ability ya bayyana cewa kungiyar tana da kudi da suka kama N212,080 amma ya ce an kashe N127,140 a kan ayyukan kungiyar, sauran sun rage N84,940. Nan take wasu daga cikin 'yan kungiyar suka nuna rashin gamsuwarsu da bayanin Ability.

Al'amari ya kara dagulewa da Ability ya sake yin bayani game da sauran kudin da suka rage. A cewarsa, daga cikin N 84,940 da ya kamata a ce suna cikin asusun kungiyar, akwai N50,000 da Sardaunan Furodusoshin Arewa, Alh. Abdu Haro Mashi, ya yi wa kungiyar alkawari amma har yanzu bai ba da ba. Sai kuma N5,000 da Shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Arewa, Alhaji Hamisu Lamido Iyan-Tama, ya yi alkawarin ba kungiya, shi ma bai bayar ba. Ya ce akwai kuma N1,000 da tsohon shugaban kungiyar, Aliyu Abdullahi, ya ranta har yanzu bai biya ba. Akwai kuma wasu N2,800 wadanda ya ce bai san yadda aka yi suka salwanta ba. Daga karshe dai abin da kungiya ta samu a hannu bai wuce N14,940 daga cikin N212,080 ba.

Wannan jawabi ya bata wa kusan kowane dan kungiya rai. Daga nan aka nemi Ability da ya zauna a ci gaba da tuhumar wasu 'yan kungiyar da ake zargi da aikata wasu laifuffuka. Abubakar Isah Abdullahi, wanda shi ne sakataren kungiyar, an zarge shi da yi wa kungiya zagon kasa ta hanyar wai ya yi taro da 'yan bidiyo kulob tare da bayyana masu sirrin kungiyar. Sai kuma Nasiru Danmaliki da ake zarki da laifin wai ya yi murdiyar kujerar mataimakin sakataren kungiyar. Shi ko Muhammad Murtala Aminu, tuhumarsa aka yi da laifin yi wa kungiya zagon kasa ta hanyar wai ya gaya wa Yakubu Lere asirin kungiya.

Daga karshe dukkan wadanda ake tuhumar an umurce su da su fita waje don a tattauna irin hukuncin da ya dace da su. Bayan fitarsu, an kashe tsawon lokaci ana muhawara. Daga karshe aka amince da a rushe shuwagabannin kungiyar gaba daya a sake sabon zabe. Da aka juyo kan maganar Ability, wasu furodusoshi suka kawo shawara cewa maganar kudi dai ko an neme su ba samuwa za su yi ba, saboda haka suna ba da shawarar cewa abin da kawai ya dace, kowa ya yi "Allah ya isa". Haka kuwa aka yi, sannan aka kira masu laifin a kansu.

Ba tare da wani bata lokaci ba, nan take aka zabi Alh. Magaji Sulaiman a matsayin shugaban rikon kwarya, sai kuma Abdullahi Maikano Usman a matsayin sakatare. Shi kuwa Abdullahi Yahaya Maizare shi aka zaba ma'ajin kungiyar na wucin-gadi. Mutanen uku sun dauki alkawarin shirya zaben shugabancin kungiyar cikin wata biyu. Nan take aka fara mika masu wasu daga cikin kayan kungiyar don su fara aiki.

Taron, wanda aka fara da misalin karfe 1 na rana, ba a kammala shi ba sai karfe 10:30 na dare. Wakilinmu ya ji wasu furodusoshi na cewa su tun farko da sun san zaben tumun dare suka yi, da ba a kawo yanzu ba. Daya kuma daga cikin 'yan kwamitin rikon kwaryar cewa ya yi shi yanzu tunaninsa shi ne wanene ya dace daga cikin 'yan kungiyar da zai iya rike mukamin shugaban kungiyar. Wannan tambaya ita ce a ran kusan kowane dan kungiyar. Daga cikin wadanda ake rade-radin za su so zama shugaba har da Dan'azumi Usman (Dafe-Dafe), wanda shi ne shugaban gidan shakatawa na Marhaba.

Dillalan kaset sun kai wa Gwamnan jihar Kano caffa

MAI girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso, ya jaddada aniyar gwamnatinsa wajen kara goya wa harkar finafinan Hausa baya a jiharsa. Gwamnan ya yi wannan bayani ne lokacin da 'ya'yan kungiyar masu sayar da kaset na bidiyo da rediyo ta Jihar Kano suka kai masa ziyara a fadarsa.

Kwankwaso ya nuna jin dadinsa kan yadda finafinan Hausa ke wayar da kan al'umma. Ya kara da cewa, "Finafinan Hausa sun shiga gidaje sun kori finafinan waje masu dauke da mummunar al'adu."

Gwamnan Kano
'Yan kungiyar ta Dillalan kaset na bidiyo da rediyo na jihar Kano sun dauki wannan hoton tare da Gwamna Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso lokacin da suka kai masa ziyara a gidan gwamnati. Ga Gwamna nan a tsakiya

Da ya karkato wajen nasiha kuwa, gwamnan ya hori duk wani mai sana'ar fim da sayar da kaset da ya kara daukarta da muhimmanci. A ta bakinsa, "sana'a ce wadda al'umma ke dogaro da ita, mai muhimmanci. Ku ci gaba da inganta ta, a daina dogaro da aikin gwamnati." Sai kuma ya hore su da su guji yi ko sayar finafinai wadanda suka saba wa shari'ar Musulunci. A karshe ya yi masu alkawarin duba kukansu na neman kyautar fili wanda za su gina ofishin kungiya na dindindin.

Tun farko a jawabinsa, sakataren kungiyar, Alhaji Ahmed Mohammed Amge, ya labarta wa gwamnan cewaan kafa kungiyar ne kimanin shekaru 13 da suka gabata, inda ta fara da mutum 15. "A yanzu akwai mutane sama da 6,000 masu amfana da wannan sana'a," inji shi. Ya kuma shaida wa gwamnan cewa babban makasudin ziyarar tasu shi ne don su yi wa gwamna ta'aziyyar al'ummar da aka rasa sanadiyyar hadarin jirgin sama da ya auku a Kano watannin uku da suka wace.

Alh. Ahmed
Alh. Ahmed Muhammad Amge

Alhaji Amge ya kuma yi wa gwamna murnar cika shekaru uku kan gadon mulki a madadin sauran 'yan kungiya. A karshe kuma ya nemi alfarmar fili domin gina ofishin kungiyar.

Bayan Amge ya kammala jawabi ne sai jagoran tafiya, Alhaji Musa Na Malam Kato ya bai wa gwamna kyautar Alkur'ani mai tsarki kammalalle a cikin kaset na rikoda. Ya kuma ba shi wata kyautar ta kaset na finafinan Hausa iri daban-daban har guda 50.

Ita wannan kungiyar dai a rarrabe take a daidai wannan lokaci. Bangaren da ya je gidan gwamna yana karkashin shugabancin Alhaji Musa Na Sale wanda bai sami halartar ziyarar ba saboda wata tafiya da ya yi. Kan haka ne matamakinsa Musa Na Malam Kato ya shugabanci ziyarar.

Sai dai kuma wani wanda ke ikirarin jagoran a wani bangare na kungiyar ya yi tir da wannan ziyara da aka kai. Mai ikirarin, Alhaji Rabi'u B.K., ya nuna cewa shi bai ga dalilin da zai sa a rika kiran tawagar maziyartan da suna shugabanni ba "domin ai sun rubuta takardar sauka har an yi zabe, an zabe mu. To me zai kai su gidan gwamna?" inji Rabi'u B.K. Sai dai kuma daidai lokacin da B.K. yake wannan magana, tuni har su Amge sun ci gaba da ziyartar manyan mutanen jihar don neman gindin zaman shugabancinsu. A ranar da suka je wurin gwamna kuma sun kai ziyara wurin Wamban Kano.

Budurwar wacece?
Maje El-Hajeej ya mai da wa S. Nuhu martani:

"Ni ban ce ina son Maryam Mushaqqa ba"

FITACCEN marubuci kuma furodusan fim din Juyayi, Maje El-Hajeej Hotoro, ya musanta wasu kalamai da jarumi Ahmed S. Nuhu ya yi a cikin hirar da Fim ta yi da Ahmed din a watan jiya, yana mai cewa sam, babu kanshin gaskiya da Ahmed ya ce Maje ya nuna yana son 'yar wasan nan Maryam Aliyu (Mushaqqa).

A fusace, Maje ya kuma kalubalanci mujallar saboda rashin zuwa ta tambayi Maryam ko da gaskiya ne idan ya taba zuwa ya ce yana son ta. Ya bayyana cewa shi akwai yarinyar da yake soyayya da ita kuma za su yi aure, amma da ta karanta inda Ahmed ya ce Maje ya nuna yana son Maryam sai da budurwar ta marubucin na littafin Sirrinsu ta canza masa fuska. Sai dai kuma ya nuna cewa ba mamaki shi Ahmed ya yi haka ne domin ya rama wani abu da shi Maje din ya ce ya yi masa. Haka kuwa aka yi, domin bayan an yi hirar, tun kafin a buga ta, Ahmed ya shaida wa Maje cikin raha cewa ya yi masa wani abu don ya rama wani abu da ya yi masa.

Maje dai ya yi addu'ar Allah ya tabbatar da auren Ahmed da Maryam ya kuma sa auren ya yi danko. "Idan za ku tambayi Ahmed, zai fada muku cewa ai ni mai ba shi shawara ne kan ya auri Maryam," inji shi. Ya kara da cewa, "To me ya sa kuma zan dawo in ce ina son ta?"

Marubucin na Shakka Babu ya kuma ce 'yanmata sun sha zuwa su neme shi kan wannan magana da Ahmed ya ce Maje ya nemi yin soyayya da jarumar ta shirin Sharadi da Yanayi, har suka rika zolayarsa.

Da ma tun ranar da wannan mujalla ta je Kano a watan jiya, Maje ne wanda ya fara karanta ta, saboda yana zaune a ofishinmu aka kawo ta. Kamar ya sani, labarin Ahmed ya fara karantawa. Bayan an dauki lokaci mai tsawo sai ya kada baki ya ce, "Fim magazine ta fito da labarai, amma ni wannan ne bai yi min ba," wato yana nufin hirar Ahmed S. Nuhu, wanda shi ne yaron bangon mujallar a watan jiya.

A karshe Maje ya yi bayanin cewa dalilin haduwarsa da Maryam shi ne wata rana a ofishin mujallar Fim lokacin da Halima Adamu Yahaya ta kai ta aka fara yin hirar farko da ita. A lokacin ma yarinyar ba ta shiga ko da a fim guda daya ba. Maje ya tuno cewa bayan ya furta cewa, "Ni ma zan yi fim", sai Halima Adamu Yahaya ta yi masa tallar yarinyar, ta ce masa, "Ga wata 'yar wasa sai ka saka ta; ga ta fara, kuma ba sai ta yi karin gashi ba."

Maje El-Hajeej Hotoro ya sa kyakkyawar yarinyar a matsayin jarumar fim dinsa Juyayi, wanda bai fito ba tukuna, kuma Ahmed S. Nuhu ne yaron fim din.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin