Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 33   Satumba 2002
LABARAI


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
HIRAR MUSAMMAN
Wasiku
KU TAMBAYE SU
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
RA'AYIN MUJALLAR FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon Fim ta 31
Bangon Fim ta 30
Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

An sadaukar da finafinai ga marigayi Jarma

Daga SANI MOH'D MAIKATANGA a Kano

WASU mutum biyu daga garin Kabo na Jihar Kano sun yi kundumbala sun shirya finafinai biyu wadanda suka sadaukar ga marigayi Jarman Kano Hakimin Kabo, Alhaji Muhammadu Adamu Dankabo.

An yi taron kaddamar da finafinan biyu, wato Noor da Tawili, kwanan nan a Kano. Cikin mahalarta bikin har da Mai Girma Hakimin Dala kuma Sarkin Dawakin Tsakar Gida, Alhaji Aminu Ado Bayero, da babban mai kaddamarwa, Kaftin Sa'idu Mohammed (Dan Amanar Jarma).

Da karfe 11:40 na safe aka fara taron tare da yi wa Jarma addu'ar musamman.

Alh. Bello Hayatu Gwarzo ne ya yi babban jawabi inda ya ja hankalin mutane kan kokarin da 'yan fim suke yi wajen fadakar da jama'a kan wasu abubuwa munana da suke yi. Ya ce a ganinsa, 'yan fim suna taimakawa sosai wajen nuna wa mutane illar munanan ayyuka musamman a cikin zaman aure. Ya yi kira ga masu shirya fim da su rika tabbatar da cewa duk fim din da za su shirya bai kauce wa shari'a ba kafin ma su fara shirya shi. A nasa jawabin, Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana cewa shi kansa ya karanci wani bangare na shirin fim lokacin da yake karatunsa. Ya bukaci masu kudinmu da su rika koyi da abin da marigayi Dankabo ya yi na taimaka wa bayin Allah a kowane hali da ya ga zai iya.

Da ya koma kan 'yan fim, Hakimin ya ce harkar fim aba ce mai wahala da sadaukar da kai. "Ya kamata mutum ya yi abin da gaske idan har zai yi," inji shi.

Furodusan Noor, Safiyanu El-Zakh, wanda shi ne jarumin shirin, ya ce ya shirya fim din ne sakamakon yadda ya ga 'yan Kudu suna dagewa su yi fim mai kyau. Kuma furodusan Tawili, Abdullahi Usman Kabo, ya ce sun shirya fim dinsu ne dalilin sha'awar yadda 'yan fim suke zuwa Kabo suna shirya finafinai - kamar su Samodara, Amalala, Alfijir, da sauransu. Ya ce an shafe akalla shekara daya ana shirya fim din, a yi a tsaya, har Allah ya sa aka kammala. "Mun yi niyyar kaddamarwar tun kafin rasuwar marigayi domin ya kaddamar mana, amma Allah bai yi ba."

Furodusoshin sun yi godiya ga mutanen da suka halarci taron.

'Yan koroso sun cashe a wurin, sa'annan jama'a sun yi ta yin addu'a ga marigayi Jarma Dankabo. 'Yan fim da dama sun halarta, ciki har da Sakataren Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kano, Baba Sheriff, da Tijjani Ibraheem, Mohammed Garba Kabara, A.G.M. Bashir, Tijjani Asase, Musbahu M. Ahmad, Rukayya Umar Santa, Rahama Isa, da kuma mai gabatarwa Ibrahim Mu'azzam.

Ya zuwa lokacin da aka tashi daga taron da karfe 1:22 na rana, an tara kudi kimanin N200,000 - tsaba da cek da kuma na alkawurra.

Furodusoshi za su yi shari'a da matan aure masu hayar kaset a gida
Sun fara yin gagarumin samame a Kano

Lilisco
Shu'aibu Lilisco

Daga SANI MOH'D MAIKATANGA a Kano

KUNGIYAR Furodusoshi ta Jihar Kano ta sha alwashin sa kafar wando daya da duk wani mai ba da hayar finafinan Hausa ba bisa ka'ida ba, ciki kuwa har da matan aure da suke tafiyar da harkar bidiyo kulob daga cikin gidajensu.

Daya daga cikin 'ya'yan wasu kwamitocin da kungiyar ta kafa domin yin kamen masu ba da hayar, Malam Shu'aibu Idris (Lilisco), ne ya bayyana haka a cikin wata hira da mujallar Fim kwanan nan.

Shu'aibu yana maganar ne bayan wani gagarumin samame da kungiyar ta fara gudanarwa kwanan nan a Kano. A samamen, kwamitoci da aka ba sunayen A, B, C, da D sun yi kamen 'yan bidiyo kulob a unguwanni daban-daban na birnin na Dabo. Shi Shu'aibu shi ne shugaban kashi na 'A' wadanda suka yi samame a Dakata, Hadeja Road, Court Road, Tarauni, Brigade, da Gwammaja.

Da yake bayyana dalilin kamen, Lilisco ya ce, "Mun duba mun ga kasuwar finafinan ta mutu, kuma su masu yin hayar kaset su ne suka kawo hakan. Ana yin renting (sana'ar ba da hayar kaset a ko'ina a duniya), ba ba a yi ba, to amma wannan (na Hausa) babu doka a cikinsa. Yanzu za ka ga furodusa ya yi fim, maimakon ka ga ya samu riba sai ka ga ya fadi. Ka buga kwalin kaset misali dubu goma amma kuma ko dubu bakwai ba ka sayar ba, bacin kuma da ba haka ba ne.

"Kuma duk wannan renting din shi ya kawo haka. Misali, a wani bangare za a samu mutum dubu biyar suna sayen kaset da kudinsu, amma sai ga shi an bude wajen renting. Ka ga ka'ida ne sai an janye sama da mutum dubu biyu sun koma renting, tunda za su ce, 'Af, ga inda zan biya N20 in kalla me zai sa in saya?', bacin da kuma sayen yake. To ka ga ai wannan ya kashe mana kasuwa ba kadan ba."

Shu'aibu ya ce har a gidan matan aure ana ba da hayar kaset, wanda hakan ci-baya ne. Ya bayyana cewa kungiyar furodusoshin ta wakilta mata da za su bi gidajen da matan aure ke ba da haya su ja kunnensu. "Kuma in aka kama matar aure sai mun gurfanar da ita a gaban kuliya," inji shi.

Shugaban kwamitin ya kara da cewa ba wai za a hana ba da hayar kaset ba ne kwata-kwata, to amma tilas ne a yi abin bisa tsari ta yadda su ma furodusoshi za su amfana. Ya ce kungiyar furodusoshin tana nan tana tsara yadda za ta yi hulda da masu bidiyo kulob. Kafin nan kuwa za a bar su su ci gaba da hayarsu. Ya ce wadanda aka kama kwanan nan ba kowa da kowa ba ne, sai wanda aka gani a fili, to amma za a ci gaba da yin samamen da aka tsara.

Fim ta fahimci cewa a lokacin wannan samame sun kewaya wasu unguwanni ne tare da 'yansanda inda suka kakkama mutanen da suka kira "barayin zaune masu ci da gumin furodusoshi."

Samamen dai ya tayar da kura, domin su masu bidiyo kulob din da aka kama sun yi kukan cewa ba a yi masu adalci ba saboda yadda aka aiwatar da kamen. Daya daga cikinsu, wani mai suna Rabi'u Shu'aibu, mai kantin 'Danny Indian Music Studio' da ke kasuwar Tarauni, ya ce bai ji dadin yadda aka kama yaransu aka hada su da masu aikata muggan laifuka ba a ofishin 'yansanda. Ya ce, "Bayan mun je can mun yi kokarin a sako mana yaranmu suka ki. Kuma sun hada mana yaranmu da masu munanan laifuka sun kulle, suka hana mu belinsu. Shi ne abin da ya fi ba mu haushi da bakin ciki."

Wani abu da ya bata wa 'yan bidiyo kulob din rai kuma shi ne da 'yan kungiyar suka ce su tafi sai bayan mako biyu za a zo a shirya yadda za a rika tafiyar da huldar ba da aron kaset. "Bayan an cuce mu kuma aka zo ana ba mu hakuri," inji Rabi'u.

Ya ce ai da can sun taba zama da furodusoshin kan yadda za a tsara yadda masu kulob za su rika biyan masu finafinan wani dan hasabi ga furodusoshin, to amma "sai su furodusoshi suka ki."

Ya bayyana cewa masu ba da aro mutum 18 aka kama, kuma kungiyarsu ce ta yi belinsu a kan N3,500 kowane mutum. "Amma akwai masu karamin karfi wadanda ba za su iya biya ba, su ma dai aka ce to za a san yadda za a yi da su. Wasu har talbijin dinsu da kaset-kaset da bidiyo aka kwace masu."

Rabi'u ya ga laifin furodusoshi da suke barin finafinai suna fitowa da yawa a mako, maimakon daya ko biyu. Ya ce idan kaset biyar sun fito a mako, yaya za a yi mutum ya iya sayensu duka? Ai tilas sauran sai dai ya ara.

Ya ce idan furodusa ya samu su masu bidiyo kulob da fim dinsa, za su iya saye a kan yarjejeniya. Ya ce haka suka yi da mai fim din Romon Rogo inda suka rika sayen kaset din a kan N300 kowane. "In ba shi ba ma ba wanda ya zo ya same mu ya ce ya ba mu izinin mu bayar da kaset dinsa haya. Har taro aka shirya a Daula Hotel amma furodusoshin suka ki zuwa."

Rabi'u ya ce idan furodusoshi ba su son a ci gaba da ba da hayar kaset dinsu, to su fada domin a daina din. "Sai mu koma ga inda muka fi wayo - wato na Indiya da Amerika."

Ya ce, "Ni da ma 'yan unguwarmu ne suka dame ni da kuma su 'yan kasuwan, suna cewa me ya sa ba ma sayen na Hausa. Amma in ba haka ba fim na Hausa da ya yi sati shikenan an daina yayinshi. Amma kuwa na Indiya da Amerika ko yaushe ana tambayarsa."

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin