|
Ci-gaba ya zo: Su Biba, Ishaq da Saratu a 'Nigerian film' a karo na farko
Daga MUHAMMED NASIR
a Kano
Saratu Gidado
|
NAN ba da dadewa ba za a fara shirin wani fim mai suna Unchained wanda ke kunshe da 'yan wasan Kudu da kuma na Hausa. Fim din, wata fitacciyar 'yar wasa ce 'yar Kudu mai suna Hilda Dokubo za ta shirya shi.
Daga cikin wadanda aka gayyata a 'yan wasan Hausa akwai Ibrahim Mandawari, Ali Nuhu, Ishaq Sidi Ishaq, Saratu Gidado, Hauwa Ali Dodo (Biba) da Hajara Usman.
Fim din Unchained labari ne wanda zai bayyana yadda ake mayar da matan kasar nan koma-baya ta fannin siyasa. A fim din akwai zaratan da za su taka rawa sosai don wayar wa matan cikin gida kai kan su fito a dama da su aikin harkar siyasa.
Furodusar fim din ce da kanta ta zo Kano ta tattauna da'yan wasan da ta dauka. Kuma tuni har ta raba masu kundin da ke dauke da labarin fim din.
Za a yi fim din ne da Turanci.
Ya zuwa yanzu dai 'yan wasan Hausa da suka taba fitowa a fim din Kudu kalilan ne. Sun hada da Kasimu Yero, Ali Nuhu, Ibrahim Mandawari, Hindatu Bashir, Ladi Jamila Salisu, da Waziri Zayyanu.
Wanda bai san Hilda ba, to ya kalli A Woman's Mind, Gone Forever, My Love, Black Maria, Deatly Fashion ko Remember Your Mother.
Da labarin ya fara watsuwa a fagen shirin fim na Kano, an ji wani dan wasa yana cewa, "Mun zuba ido mu ga Turanci daga bakin matan fim din da za su fito a Turawa da Taturatu uwar Turai."
Mata Musulmi sun soki lamirin finafinan Hausa
Daga ASHAFA MURNAI BARKIYA a Kano
A WANI taro da ta gudanar musamman kan finafinan Hausa, wata kungiyar mata Musulmi ta yi korafin cewa wasu finafinan Hausa suna bata tarbiyyar 'ya'ya, musamman mata. Taron, wanda aka gudanar a ran 8 ga Satumba, 2002 daidai lokacin da ake aiwatar da zaben kungiyar masu sayar da kaset na Jihar Kano, bai samu halartar 'yan fim da yawa ba duk kuwa da cewa wadanda suka shirya shi sun raba wa wasu 'yan fim takardar gayyata.
Mahalarta taron sun fito fili sun nuna bacin ransu kan dagula tarbiyya da suka ce wasu finafinai na haifarwa. A cikin jawabinta, shugabar taron, Hajiya A'ishat Usman, ta yi korafin cewa, "'Yayanmu mata ba su san da zuwa wurin boka ba sai ta dalilin ganin haka a cikin finafinan Hausa". Ta kuma yi nuni da cewa saboda su 'yan fim din sun san abin da suke yi babu gaskiya, shi ya sa da aka gayyato su ba su je ba.
Daga cikin kalilan da suka je wurin kuwa, yawancinsu masu wakiltar wasu mujallu ne na finafinan Hausa. Ishaq Sidi Ishaq da Alhaji Jamilu, furodusan Muqabala, sun je wurin a makare ana daf da fara shirin yin addu'ar rufe taro.
An yi taron ne a dakin taro na 'Sani Abacha Sports Complex' da ke Kofar Mata a Kano. Ya samu halartar wasu malamai, cikinsu har da Sheik Umar Kabo Idris.
Finafinan yanzu shirme ne - Jibrin
Daga SHAFI'U MAGAJI USMAN
a Kaduna
Jibrin Yahuza
|
A YAYIN da wasu suke ganin cewa harkar shirya finafinan Hausa ta sama ci-gaba ta wajen sanya samari da 'yanmata suna rike bindigogi wajen aikata ta'addanci a fim, wani tsohon dan wasa da ya ba da muhimmiyar gudunmuwarsa a harkar cikin shekarun 1980, kuma ya koma ruwa a yanzu mai suna Malam Jibrin Yahuza, ya yi kakkausar suka tare da ambaton cewa wannan wani babban bala'i ne da ya gangaro zuwa ga al'ummar Hausawa ta hanyar wasannin kwaikwayo.
Malam Jibrin ma'aikaci ne a 'Kaduna Polytechnic' kuma dan wasan da ya fito a matsayin Waziri a cikin fim din Ruwan Bagaja. Ya bayyana bacin ransa kan haka ne ckin wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu a Kaduna a kwanakin baya. Ya kara da cewa, "Yawancin finafinan Hausa da ake shiryawa yanzu shirme ne kawai ake tafkawa, ba alkibla bare fadakarwar da ta kamata. Ba su san komai ba sai baragada wajen kwaikwayon rawa da wake-wakken finafinan Indiya; ko ka ga wai budurwa Bahaushiya a fim ta zanzare rike da bindiga wai ita ga 'yar ta'adda tana gogayya da maza.
"Don Allah ina alherin wannan? Ko shi ne ci-gaban wajen lalata tarbiyyar 'ya'yanmu da suke kallon wadannan finfinan?"
Dan wasan, wanda yawancin wasanninsa ya yi su ne cikin shekarun 1980 zuwa 1990 a hukumomin rediyo da talbijin na Kaduna, ya kara da cewa a halin yanzu da harkar wasannin kwaikwayo ta fadada sai kuma ta tabarbare ta hanyar raya al'adu da kyawawan dabi'o'inmu na Hausawa. Don haka bai ga laifin jama'ar da suke daukar 'yan fim musamman mata a matsayin 'yan iska ba. Domin shi kansa yana kyamar 'yan mata fim na yanzu da batun aure.
Da wakilinmu ya tambaye shi hanyoyin gyara al'amarin in akwai, sai Malam Jibrin Yahuza ya ce akwai hanyoyi masu yawa; wadanda suka fi muhimmanci su ne, a sanya tsofaffin 'yan wasanmu irin su Kasimu Yero, Malam Mamman, Samanja, Dan Wanzan, Karkuzu da sauransu damu-dumu cikin harkar. Domin in suka ga za a yi ba daidai ba suka tsawata za a saurare su ko don shekarunsu da kuma dadewarsu a harkar.
Hanya ta biyu kuma ita ce hukumomin gwamnati da kungiyayin al'umma su sa ido kan finafinan da za a rika bari su shiga kasuwa, ya kasance fim ne na fadakarwa ne ba sharholiya ba.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|
|