Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 35   Nuwamba 2002
LABARAI


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
TALLA
Wasiku
KU TAMBAYE SU
Duniyar Finafinai
Rahoto
Malam Zurke
Rayuwarmu
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka
Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Ligidi na so a sake tsari don gyara lafawar kasuwa

Daga SANI MOH'D MAIKATANGA a Kano

A CI-GABA da 'yan fim suke yi na gano dalilan da suka jawo faduwar kasuwar finafinan Hausa da hanyar da za a bi a yi gyara, shahararren dan wasan nan Abdullahi Zakari (Ligidi), ya ce babu shakka harkar fim na Hausa za ta ci gaba, amma fa sai an yi gyaran da ya dace.

Lokacin da yake tattaunawa da Fim a Kano, Ligidi ya ce, "Akwai hangen ci-gaba amma kuma akwai bukatar gyara, saboda duk abin da kake yi da ma sai ka samu matsala. Daga baya kuma za ka ga alfanunsa in ka gano matsalar.

"Na tabbatar in har mun gyara kura-kuranmu samun ci-gaba ba sai an fada ba, domin da ma kasuwanci yana da wannan."

Malam Abdullahi ya lura da cewa a wannan harka akwai kurakuran da ake tafkawa, kuma ba za su kau ba har sai ana "samun hadin kai." Ya ce: "Ita wannan matsalar ba ta mutum daya ba ne - daga kan masu gabatar da finafinai, 'yan kasuwa, sai 'yan wasan da kuma su masu gabatar da wasannin wajen daukar wasan."

Ya yi nuni da yadda wasu mutanen ke ta antayowa cikin harkar fim barkatai babu tsari. "Ga shi muna samun wasu suna ta shigowa harkar, dole ne da ma duk abin da kake yi in dai har na jama'a ne, sai an samu wasu sun shigo, to amma shigowar tasu ba tsari, duk wanda zai shigo kamata ya yi ya biyo ta kafa mai kyau. Saboda da zarar wani abu na gyara ya taso sai a sanar da shi. Amma kawai kuma ga cunkushewar kasuwar finafinai a yanzu. Amma abin ba na mutum daya ba ne; kowa yana da laifi."

Ya kara da cewa in dai har ana so a ci gaba a harkar, "kamata ya yi mu san inda matsalar take, mu zauna kowa ya kaskantar da kanshi domin a yi wannan gyara. To amma ga shi an bar finafinai suna ta fitowa ba tsari barkatai, sannan da kuma ma rashin tsarin fim mai kyau.

"Kamata ya yi duk fim din da zaa yi a san yana da labari mai kyau, sannan kuma 'yan wasa sun san abin da suke yi. To in dai za mu yi haka to lallai insha Allahu kasuwa za ta gyaru."

Kuma a duk harkar da mutum ya sani, inji Ligidi, ana neman sani kuma ana neman hadin kai da tsari mai kyau. "Ya kamata duk wani mai wannan harkar ya zo domin a zauna a sami tsari mai kyau wanda duk wanda ya karya doka a hukunta shi. Kuma duk bin da mutane ba sa so mu guje shi ba mu yi ta yin abu daya ba - soyayya kawai. Dole mutane su ce ta gundire su.

"Tunda haka ne mu koma irin matsalolin da suke addabarmu mana, kamar makirce-makirce, cin amana da zamba. To ko soyayya ka sa kuma rawa da wakar ma a yi masu tsari da ma'ana."

Yakubu Lere ya yi amarya

Daga Wakilinmu a Zariya

Lere
Yakubu Lere

FITACCEN furodusan shirin Wasila, Yakubu Lere, ya kara mata, inda ya auri wata budurwa mai zama a Kaduna mai suna Habiba Mohammed Rilwanu. An daura aurensu a ran Asabar, 5 ga Oktoba, 2002, da misalin karfe 3:30 a gida mai lamba 58 da ke 'Aminu Road,' Tudun Wada, Zariya, a kan sadakin N10,000, kuma ango ya biya lakadan. 'Yan fim da dama sun halarci daurin auren, yawancinsu daga Kano, amma kuma angon ya ki gayyatar wasu manyan 'yan fim wai saboda bai shiri da su, ciki kuwa har da Sakatare-Janar na Kungiyar Furodusoshi ta Arewa, Malam Abdullahi Maikano Usman.

A ranar Lahadi ne kowa ya kama gabansa tare da yi wa ango da amarya fatan alheri da zaman lafiya. Muna taya su murna.

A gafarce mu

A Fim ta watan jiya, a filin "Mu Leka Mu Gani," Ibrahim Sheme ya ambaci cewa marigayi Alhaji Adamu Halilu dan Jihar Adamawa ne saboda dan asalin Garkida ne. To, an jawo hankalinmu ga cewa Garkida cikin Jihar Borno take kamar yadda muka rubuta a labaran da suka shafi marigayin a baya. Muna fatan za a gafarce mu kan wannan tuntuben alkalamin. Edita

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin