Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 39   Maris 2003
LABARAI


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
FADI SONKA
Wasiku
NEMAN MAFITA
DUNIYAR FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
FADI SONKAr sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da tunanin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: Wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, ta da jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Hedimasta, fitaccen dan wasa, ya rasu

Daga BASHIR ABUSABE a Sakkwato

INNA lillahi wa inna ilaihi raji'un! Allah ya yi wa tsohon shahararren dan wasan nan kuma dan siyasa da ke Sakkwato, Alhaji Haruna Abubakar Dogondaji, wanda aka fi sani da suna Hedimasta. Ya rasu a ranar Jumma'a, 3 ga Janairu, 2003, bayan ya yi fama da dogon rashin lafiya. Ya rasu yana da shekaru 57 da haihuwa, ya bar mata uku da 'ya'ya wajen 12.

Idan za a iya tunawa, marigayin ya yi doguwar hira da mujallar Fim, ta fito a Disamba 2001. A cikin hirar ya bayyana tarihin rayuwarsa da ra'ayoyinsa kan harkar wasan kwaikwayo.

An haife shi a garin Dogondaji a cikin 1945. Ya yi aikin koyarwa a makarantu daga 1962 zuwa 1977. Ya yi aiki a kamfanin buga littattafai na Arewa (NNPC), Zariya, kuma ya yi aikin rediyo a 'Rima Radio,' Sokoto, na tsawon shekaru takwas.

A cikin 1978 ne ya fara wasan kwaikwayo a rediyo a matsayin marubuci kuma dan wasa. A cikin 1980 kuma ya soma wasan a talbijin, inda ya kara yin fice musamman a wasanninsu da su Danwanzan, Bahausa, Hakimi, Mai Gero, 'Yar Mai Albasa, da sauransu. Ya samu sunan Hedimasta daga wani wasa inda ya fito a matsayin shugaban makarantar firamare. Daga baya ya shiga siyasa, inda ya kai matsayin an zabe shi a matsayin Wakilin mazabar Dogondaji (bangaren 'yan adawa) a Majalisar Dokoki ta Jihar Sakkwato, mukamin da yake rike da shi har zuwa lokacin da Allah ya karbi ransa.

A hirarsa da wannan mujallar ta watan Disamba 2001, Hedimasta ya shaida mana cewa mai yiwuwa bayan siyasa su fantsama cikin shirin fim, to sai dai ya yi nuni da cewa kasancewar wasu daga cikin guruf dinsu sun rasu saboda haka idan suka yi babu su fim din ba zai yi dadi ba. Kuma ya ce ya rubuta wasannin kwaikwayo na rediyo da na talabijin sama da dari biyu.

Ya zuwa yanzu a rundunar tsofaffin 'yan wasan kwaikwayo da ke Sakkwato wadanda suka rasu sun hada da Hakimi, Maigero, Liman, Bahausa, Maitarugu, da Kafigwanja; na baya-bayan nan shi ne Hedimasta wanda yake rubuta da tsara wasan kwaikwayo.

Allah ya jikansa ya gafarta masa, ya kyautata tamu in ta zo, amin.

An rushe shugabannin kungiyar 'yan wasa ta Kaduna
Ana zargin su da cin kudin kungiya

Daga ALIYU A. GORA II a Kaduna

SAKAMAKON zargin da ake yi wa shugabannin kungiyar 'yan wasan kwaikwayo ta Jihar Kaduna na rashin iya gudanar da mulki da kuma yin facaka da kudin kungiyar ba bisa ka'ida ba, wanda ya sa 'ya'yanta suka dakatar da shugabannin suka kuma nada kwamitin bincike mai dauke da mutane goma kimanin watanni uku da saka wuce, yanzu kwamitin ya mika sakamakon binciken da ya yi ga uwar kungiyar. Hakan ya faru ne a wani babban taro da kungiyar ta yi a ranar Lahadi, 2 ga Fabrairu, 2003 a harabar Hukumar Fasaha da Raya Al'adun Gargajiya ta Kaduna.

An yi taron a karkashin shugabancin Alh. Umar Maikudi (Cashman) wanda kuma shi ne shugaban kwamitin binciken.

Da ya yake karanto sakamakon, Mahmud Marwan ya ce a binciken da suka gudanar, sun kama tsohon shugabansu Yahuza A. Ilu da laifin kaka-gida da kayan kungiya da kuma hana wasu shugabannin gudanar da aikinsu yadda ya kamata. Haka kuma an zargi tsohon shugaban da laifin kin bude wa kungiya asusu a banki. Sa'annan ana zargin Yahuzan a tare da mukarrabansa da laifin cinye kudin kungiya kimanin N109,800.00.

Bayan sauraron sakamakon zaben sai 'ya'yan kungiyar suka zabi shugabannin rikon kwarya su bakwai wadanda za su shugabanci kungiyar na tsawon wata shida kafin a yi zabe. Sani Idris Kauru (Moda) aka zaba a matsayin shugaba.

Nan take, bayan an kaddamar da su, sai Sani Moda ya mike ya yi jawabin godiya da kuma fatan Allah ya ba su ikon sauke amanar da aka dora masu lafiya. Moda ya ce daga wannan rana, ya dakatar da yi wa sababbin membobi rijista a kungiyar har sai sun gama sabunta fom din da ake cikawa don zama dan kungiya, da kuma wasu muhimman takardu don magance sharrin 'yan damfara da ake sa ran za su iya ci gaba da yin amfani da tsofaffin takardun suna damfarar mutane da sunan kungiyar.

Shugaban har ila yau ya bayyana cewa daga wannan rana, ya rushe kwamitin binciken tare da yi masu godiya game da yadda suka gudanar da bincikensu bisa adalci. Daga karshe, ya yi rantsuwa tare da daukar alkawarin karbo dukkan kudaden da ke hannun rasassun shugabannin da kuma kayan aiki. Ya ce babu wata dangantaka a tsakaninsa da wani wadda za ta hana shi karbar hakkin jama'ar da suka damka masa amana.

Amma har wasu sun fara korafi kan binciken da aka yi inda aka nuna cewa sun handame kudin kungiyar. Wani daga cikin wadanda ake zargin, Malam Isah A. Isah (Danlami) ya ce, "Ni kam kwamitinbincike bai yi mani adalci ba, domin babu wanda ya taba samuna a kan maganar sai ga shi an karanto wai ana neman kudin kungiya a wajena har N10,000." Da wakilinmu ya nemi cikakken bayani daga gare shi, sai ya nuna ba ya son yin wata magana yanzu, sai idan nan gaba an kara kiransa game da maganar kudin.

Haka kuma wakilinmu ya ji wasu a bayan fage suna cewa an koma gidan jiya domin Moda dai ba zai iya rike kungiyar ba. Wani kuma cewa ya yi shi kam, a nasa hangen yanzu ne za a yi kungiya, domin tun farko da ma irin su Moda ne ya kamata a ce suna shugabantar kungiyar, ba zaben tumun dare dare ba.

An tashi taron lafiya da misalin karfe 4:11 na yamma. Manyan baki sun hada da shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kaduna, Alh. Ashiru Sani Bazanga.

Furodusoshin Sakkwato sun samu rijista ta Arewa
Saura ta gwamnatin jiha kuma

Daga BASHIR ABUSABE a Sokoto

P>FADI-TASHIN da shugabannin riko na Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Sokoto (SOFMA) ke yi na ganin sun samu rijista ya kusa cimma nasara. Wannan ya biyo bayan samun rijista da ta yi daga Kungiyar Furodusoshi ta Arewa ('Arewa Film Producers Association of Nigeria') domin kasancewa daya daga cikin 'ya'yanta na kasa.

jaimi'in yada labarai kuma ma'ajin SOFMA din, Sadiq Bello Jariri, wanda ya dade yana babatu kan al'amarin, shi ne ya tabbatar da haka, kuma ya nuna wa wakilinmu kwafen takardar rijistar. Ya bayyana farin cikinsa kan yadda Allah cikin ikonsa ya biya masu bukatarsu ta samun rijista da Arewa a karkashin jagorancin M.Z. Faru, ya ce "kuma Allah ya sa kunjiyarmu ta zama halattaciyar kungiya kamar kowace kungiya a Nijeriya."

Duk da haka ya ce samun wannan rijistar ba zai sa su yi watsi da neman ta jiha ba. Ya ce sun yi taro na shugabanni da na membobi inda aka kawo shawarwari na yadda za a samu rijista da jiha, kuma har an nada wakilai wadanda za su je su samo rijistar. Ita dai kungiyar, ta kasa samun rijista ne daga gwamnatin jihar, wadda ke yin amfani da batun Shari'ar Musulunci da aka kaddamar a jihar ta hana su rijista.

Da wakilinmu ya tuno wa Sadiq wani furuci da wani babban jami'in gwamnatin jihar ya taba yi cewa ba za a ba su ta jiha ba, sai ya amsa, "Idan za ku tuna, na shaida maku wannan ba zai sa mu karaya ba, da yardar Allah za mu bi shi mu lallabe shi har mu cimma gaci."

Sadiq ya ce ba neman rijista kadai aka zabi shugabannin kungiyar su yi ba, "amma dai tana daga cikin abubuwan da aka dora mana alhakin nemowa, kuma yanzun ko mun samu ta jiha ko ba mu samu ba za mu sauka, wadanda aka zaba kuma su ci gaba daga inda muka tsaya. Sannan matakin da za a dauka kan productions din Sokoto, tunda an samu rijista ya rataya ne kan sabbin shugabannin da za a zaba."

A ranar Asabar, 18 ga janairu da ya gabata ne aka tsara cewa shugabannin kungiyar za su sauka don a yi zaben wasu shugabannin da za su ci gaba da gudanar da kungiyar.

Da yake zayyana nasarorin da kungiyar ta samu a lokacin mulkinsu, Malam Sadiq Bello Jariri ya ce, "Alhamdullilahi, ina bugun kirjin mu muka tattaro kan 'yan fim na Sokoto muka ga an kafa kungiyar masu yin fim a jihar. Koda yake akwai kungiyar a da, amma ta fadi warwas. Sannan mun tabbatar da ganin cewa ana yin mitin a kowane wata; hakazalika, mun yi kokari mun tantance yawan production din da muke da su a Sokoto. Haka ma mun yi kokari mun ga kan furodusoshin Sokoto ya hadu ta yadda kowane production yana taimakon dan'uwanshi. Sannan mu muka tabbatar da cewa SOFMA tana da tsarin mulki. Sannan mun kafa hukumar zabe mai zaman kanta wadda za ta gudanar da zabe. Sannan uwa-uba mun samo rijista da Arewa, wato 'Arewa Film Producer Association of Nigeria.' Wadannan su ne kadan daga cikin nasarorin da muka samu.

Heyman na so 'yan fim su dauki sana'arsu da gaske

Daga ALIYU A. GORA II, a Kaduna

WANI sabon furodusa a Kaduna, Alhaji Abdullahi Heyman, ya bayyana cewa ya shiga harkar fim ne ba domin ya samu kudi ba, sai don kawai ya ba da tasa gudummuwar wajen habaka darajar harshen Hausa, al'adunta da kuma samar wa matasa aikin yi.

Heyman tsohon dan kwallo ne da ya taba buga wa Nijeriya kwallo, sannan ya samu damar wucewa kasar Siwizalan ya buga wa wani kulob mai zaman kansa kwallo kafin ya zama dillalin Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA). Ya yi wannan bayani ne a wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu a ofishinsa da ke unguwar Kurmin Mashi a Kaduna kwanan baya.

Furodusan, wanda har ila yau shi ne shugaban kamfanin 'Absad Universal Limited,' ya ci gaba da cewa fim dinsa na farko mai suna Musa'ada somin-tabi ne kawai.

Ya ce ya yi mamakin ganin yadda 'yan fim na Hausa da yawa ba su damu da sana'ar ba, suna yi mata rikon sakainar kashi, bayan jama'a suna yi masu kallon wasu mutane masu daraja, musamman na a kasar da ya zauna, inda ya ce abokansa Turawa sun sha'awar kallon finafinan Hausa, kuma shi ke fassara masu abin da finafinan ke nufi idan suna kallo.

Alh. Abdullahi Heyman ya ci gaba da jawo hankalin 'yan fim a kan su dauki wannan sana'a da muhimmancci, domin sana'a ce ta mutanen kirki wadanda jama'a suka yarda da su, kuma suke yin koyi da abin da suke karantarwa a finafinai.

Ya kara da cewa fim din nasa zai fito nan ba da dadewa ba, kuma za a ga bambancin labari da nagartar aiki. Ya kara da cewa zai yi iyakar kokarinsa ya ga ya jawo hankalin takwarorinsa 'yan kwallo su ma su shigo cikin harkar fim su ba da tasu gudunmuwar ta hanyar zuba jari, don finafinan Hausa su kara samun daukaka da daraja a duniya.

Daga karshe ya yi kira ga furodusoshi da su inganta finafinansu ta hanyar amfani da na'urori masu kyau, su kuma daina gaugawa wajen daukar shirin finafinan.

Wayyo, ba ni da sauran mai gaya min gaskiya!
Inji Hajara Usman bayan rasuwar mahaifinta

Daga ALIYU A. GORA II, a Kaduna

INNA lillahi wa inna ilaihi raji'un! Allah ya yi wa mahaifin fitacciyar 'yar wasa Hajara Usman rasuwa. Mahaifin nata, Alhaji Usman, ya rasu ne a Kano kwanan nan bayan ya sha fama da rashin lafiyar da ya yi jinyar mako uku a asibiti. Ya rasu yana da shekara 87 a duniya.

A da, marigayi Alhaji Usman yana zaune ne a garinsu Dukku cikin Jihar Gombe. Diyarsa Hajara (wadda 'yan wasa ke kira Mama Hajjo saboda girmamawa) ta shaida wa wakilinmu cewa rashin lafiyarsa ya faru ne tun a Dukku din. "Da na ga haka sai na je na dauko shi na kawo shi asibiti a Kano, kuma a asibitin ya rasu," inji ta.

Lokacin da take zayyana irin kyawawan halayensa, Hajiya Hajjo, wadda ita ce ta ci lambar mace mafi iya wasa a matsayin uwa a fim, ta ce mutum ne mai hakuri da kadan, mai dadi ko maras dadi. Ta ce ya hore ta da ko yaushe ta zama mai neman zaman lafiya, kuma yana sonta fiye da yadda ake zato.

Hajara ita ce ta 13 cikin 'ya'yan marigayin. Ta ce, "Yayyena sha biyu, amma yanzu mu takwas muka rage a duniya."

Ana cikin wannan hirar sai kawai ta barke da kuka. Wannan ya faru ne lokacin da wakilinmu ya yi mata tambaya kan irin abin da za ta yi kewa daga mahaifinta da ta rasa. Bayan ya jira ta gama kuka, sai hajiyar ta ce, "Ina tunanin ba ni da uwa, ba ni da uba, ba ni kuma da mai fada min gaskiya tsakani da Allah. Ba ni kuma da masoyi da ya wuce iyayena."

Daga karshe ta nuna matukar bakin cikin rabuwa da iyayen nata. Tana magana tana kuka ta ce, "Saboda duk abin da zan yi sai wanda na yi tunani na kaina yanzu, sai kuma masoya da za su gaya min wani abu-amma ba kamar iyayena ba." Shi ne kawai, inji ta, in ta tuna sai abin ya bata mata rai, ta ji ba dadi sosai.

Kwanan baya, wajajen karshen shekarar 2002 Hajiya Hajara Usman ta yi rashin babbar 'yarta, wadda ta rasu a Kano ba zato ba tsammani bayan ata gajeruwar rashin lafiya.

To, Allah ya jikansu baki daya, amin summa amin.

Kamfanin shirya fim ya karrama 'yan fim

Daga SANI MOH'D MAIKATANGA a Kano

WANI kamfanin shirya finafinai mai suna 'Sky Galaxy Production', mallakar gidan daukar hoto na 'Double Five' da ke Kano, ya shirya wani kwarya-kwaryan biki inda ya karrama wasu daga cikin fitattun 'yan fim na Hausa, ciki har da marigayi darakta Tijjani Ibraheem Bala. An yi bikin kwanan nan a gidan wasa na Lahai da ke daura da kamfanin editin na 'Kwality Audio-Visual' da ke kan titin gidan zu a Kano.

A cewar wadanda suka ba da kyaututtukan, sun karrama ''yan fim din ne saboda gudunmawa da kwazonsu a harkar fim na Hausa. An bada kyaututuuka ga ''yan wasa da daraktoci da kamfanonin shirya finafinai.

Dan marigayi Tijjani, Mohammed (wanda ake yi wa lakabi da Momo), shi ne ya karba a madadin mahaifinsa wanda Allah ya yi wa cikawa a ran 25 ga Disamba, 2002.

Wasu wadanda aka karrama sun hada da Ishaq Sidi Ishaq, Hafizu Bello, Isa Bello Ja, A.G.M. Bashir, Zulkifilu Muhammad, Shehu S. Bello, Maryam Aliyu, Husaina Gombe (Tsigai) da Dokta Umar Faruk Jibril. Haka kuma su ma kamfanoni irin su HRB, Iyan-Tama, Fasaha, Ibrahimawa, Mandawari, Afandaj, Fatima Production da sauransu an karrama su.

Dan wasa Kabiru Maikaba ne ya rika mika kyaututtukan.

Daga nan ne sai 'yan wasan nan masu fitowa a matsayin basawa, Ibrahim Sinana da Jazuli Kazaza, suka hau kan dandamalin karbar kyaututtukan domin taya ''yan kallo shakatawa. Bayan saukowarsu sai aka fara hayaniya da zage-zage a kan dalilin da ya sa ba a taba ba basawa wata kyautar karramawa ba, sai dai a ce su zo su da yi wani abu na shakatawar mahalarta irin wadannan tarurrukan. A nan dai aka ba Sinana da magoya bayansa hakuri.

'Yan rawar kungiyar matasa ta Wudil sun cashe da rawar fim din Salsala tun daga farkon bikin har karshensa. Da yake an tanaji jami'an tsaro (sojoji daga Barikin Bukavu) babu dan kallon da ya yi tsaurin ido, kuma an biya naira hamsin kudin shiga. An tashi daga taron da misalin karfe 6:30 na yammacin wannan rana ta Jumma'a.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin