Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 42   Agusta 2003
LABARAI


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
FADI SONKA
Wasiku
NEMAN MAFITA
DUNIYAR FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
FADI SONKAr sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da tunanin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: Wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, ta da jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Furodusoshi sun rungumi sabon tsarin sayar da jaket

Daga SANI MAIKATANGA a Kano

FURODUSOSHIN finafinan Hausa sun ce tsarin nan na ba ni manda in ba ka mandako, inda mai fim zai kai wa dan kasuwa jaket dinsa a biya shi nan take, shi ya fi dacewa da yanayin kasuwancin kaset da ake ciki yanzu.

Furodusoshi da dama sun shaida wa Fim cewa tunda dai dillalan kaset ba a shirye suke ba su rika biyansu kudin kwalayen finafinansu a kan kari, to sabon tsarin shi ya fi dacewa.

Wannan tsari, Alhaji Rabi'u Ibrahim, mai kamfanin HRB, shi ne ya fara aiwatar da shi, lokacin da ya baza kwalayen wani sabon fim dinsa, ya ce duk dan kasuwar da ke bukata ya zo ya zuba kudinsa ya sayi na daidai karfin aljihunsa, amma babu bashi.

Wannan ya biyo bayan faruwar kazaman matsaloli da rigingimu a tsakanin furodusoshi da dillalan kaset a Kano, inda furodusoshin kan ji hausi idan suka ga jaket dinsu ya kare amma dillali ya hana kudin. Wajen kokarin karbar kudin ko kuma bin bahasin yadda dilali ya yi ya samu wani jaket wanda aka ce ya kare, akan kare da wata masifa, domin furodusoshi sukan yi zargin an bi ta bayan fage ne aka sake bugo jaket din. Wannan abu ya faru ga shahararrun 'yan fim irin su Zulkifilu Muhammad, wanda ta hado su da dan kasuwa Alh. Isma'ila T.M., sannan kuma furodusa/darakta Rabi'u Ibrahim ya kwafsa da masu saida kaset na waka a Kasuwar Kofar Wambai.

Sakamakon wadannan matsaloli ne wasu manya furodusoshi suka fara yin amfani da sabon tsarin na 'juye-ban-kwarya' ko 'ban-kudi-in-ba-ka-fim-ko-da-kuwa-guda-goma-kake-so', wanda ake masa taken 'Cash-and-Carry'. Daga cikin furudososhin da suka fara amfani da tsarin akwai Rabiu Ibrahim, da Hamisu Lamido Iyan-Tama, da Sani Musa Danja.

Shin ko wannan sabon tsarin zai iya fitar da jaki daga duma, wato ya warkar da ko ya rage wa furodusoshi taskun da suke sha a wurin dillalan kaset? Wakilinmu ya tuntubi wasu daga cikinsu, kuma ya samo ra'ayoyinsu.

A nasa ganin, Shugaban Kungiyar Furodusohi ta Arewa, Alhaji Hamisu Lamido Iyan-Tama, wannan ba batun 'Cash-and-Carry' ba ne, batu ne na gaskiya domin ka tsirar da mutuncinka. Ya ce, "Yadda su dillalan nan wasunsu ke yi, ka sha wahalar yin fim ka kai kasuwa amma kafin kudinka su fito sai ka dandana ko wajen zirga-zirga a kan mashin. Kuma wai sai ka ga fim din naka ya kare amma kuma ba maganar kudin, ko kuma a rika biyanka da kadan-kadan. To idan har mutum ya san ya shirya fim dinsa kuma har ya yi tallarsa a duniya har mutane suna nemansa a kasuwa, ka ga dole su 'yan kasuwar za su nemi wannan fim din in har suna son kasuwar ta yi da su, sai ka kai wa mutum ya ba ka kudinka. Ko da goma ya ce yana so ya fi ka dankara masa kwalinka a nan. In ya kare ya kara nemanka, ba kai ka ba da kwalinka ba kana tutiyar zuwa karbar kudi sai ka ji an ce ai fim din bai sayu ba, su dawo ma da kwalin da kudin 'yan wadanda aka sayar. In kuwa kudI aka ba ka ka bayar da kwalinka, ko da nawa ne ya fi ma kwanciyar hankali.

"Kuma wannan tsarin akwai dillalan da ba za a yi musu ba domin in suka ba ka lokacin karbar kudi insha Allahu in ka zo sai sun ba ka kudin ba tantama. Duk mai ganin wannan tsarin shi ne ya fi, to sai ya gyara fim dinsa."

Shi ma fitaccen jarumi kuma darakta Alhaji Sani Musa Danja, wanda yake shugabancin kamfanin 'Two Effects Empire', ya ce wannan tsari. Ya ce: "Tsari ne mai kyau wanda zai sa furodusoshi su dage wajen yin aiki da kayan aiki masu kyau da inganci da samar da labari mai kyau ga al'ummar da suke kallonmu da kuma ilmantar da su ta hanyar wannan fim din."

'Yan Sabon Titi ba su fahimce ni ba'
- Ahlan

Daga ABBAS SAID KIRU, a Kano

WANI takun-saka da ke yi tsakanin 'yan fim da ke zaune a Sabon Titi, Kano, da takwarorinsu na 'Zoo Road' yana neman ya baci, yayin da ya hado da fitaccen jarumi Shariff Aminu Ahlan sakamakon wani furuci da aka ce ya yi cewa 'yan Sabon Titin ba su iya shirya fim ba, wai sai 'yan Zoo Road ne kwararru.

Shi dai wannan al'amari, ya yi kamari ne a 'yan watannin baya, inda ake yi wa juna gani-gani. 'Yan Sabon Titi sun hada da kamfanoni kamar Iyan-Tama, Dukku, Ibrahimawa, Gidan Dabino, Sarauniyar Sabon Titi, RK Studio, Yoko, Two Effects, Mazari Filmirage, ISI, Zik Entertainment, Home Alone, Hajin Fafa, Usmaniyya, da sauransu. Saboda karfin da wadannan kamfanonin suka yi a shirin fim tun farkonsa ya sa ake kiran Sabon Titi da lakanin 'Kannywood'.

Su kuma 'yan Zoo Road, wasunsu ma ba a Zoo Road din suke ba. Fitattun cikinsu su ne FKD, HB, Fasaha, HRB, Sulpha, yanzu kuma da Afandaj.

Da alamun dai abin ya fi gaban wasa domin kalamin da aka ce wai Ahlan ya yi ya bata ran mutane da dama da abin ya shafa, inda har wasu ke daukar matakan ladabtarwa daban-daban. Wakilinmu ya fahimci akwai kallon hadarin kaji tsakanin dan wasan da wadanda maganar ta bata wa rai a lokacin daurin auren wani dan wasa da aka yi a ranar Lahadi, 6 ga Yulin bana.

Wannan abin da ya faru ya zama barazana ga dan wasan, wanda ya garyazo ofishinmu don ya kare kansa daga abin da ya kira "yarfen 'yan adawa" da masu yi masa hassada.

Ahlan ya ce abin da ake yadawa ko kusa bai yi daidai da abin da shi ya fada ba, domin shi ya yi furucinsa ne a lokacin taron Kungiyar 'Yan Wasa da aka yi a gidan wasa na Lahai da ke Zoo Road inda ya ce bai kamata a ce sai dan asalin Kano ne kawai zai shiga takara ba, ya kuma nemi a rage kudin fom don shiga takarar.

Ya ci gaba da cewa, "Wasu suna ta yada ji-ta-ji-ta cewa na ce wai bakin da suka shigo harkar su ne suke kawo mata ci-gaba, ba 'yan Sabon Titi ba. To ni wannan magana ba haka take ba domin babu abin da zan ce da furodusoshin Sabon Titi wadanda su suka fito da ni a fim din Laila, kuma a halin yanzu na yi finafinai sababbi har bakwai a Sabon Titi wadanda ba su fito ba".

A karshe Ahlan ya bukaci manyan shuwagabannin fim da su yi masa adalci su yi nazarin abin da ya ce, sabanin masu yada wadannan magangamu na karya.

Taron dai da aka ce ya yi furucin an yi shi ne a ranar Lahadi, 15 ga Yuni, 2003 a gidan sinima na Lahai.

A'isha Ibrahim (Saliha) ta haifi Hadiza

Daga ALIYU A. GORA II a Kaduna

FITACCIYAR jarumar shirin Saliha? da A'isha 1&2, Hajiya A'isha Ibrahim, ta samu karuwa da 'ya mace watanni 12 bayan aurenta a garin Kaduna. A'isha, wadda aka daura wa aure a ranar 17 ga Agusta, 2002 da wani malami dan kasar Nijar da ke zaune a Amerika mai suna Malam Oumaten Atta, ta haihu ne a ranar Lahadi, 29 ga Yuni, 2003 a gidan iyayenta da ke Kaduna.

Ranar Lahadi, 6 ga Yuli, 2003 aka yi rugundumin suna, inda baki har daga kasashen waje suka cashe. An rada wa jaririyar suna Khadija. Sai dai wani abin takaici shi ne duk da dimbin kawayen da maijegon take da su a cikin 'yan fim, Hauwa Ali Dodo ce kadai ta halarci bikin sunan daga Kano.

Mijin A'isha ma ya zo suna daga kasarsu Nijar. Mujallar Fim ta fahimci cewa zuwan nasa ya dan dakushe gulmace-gulmacen da aka rika yadawa game da auren nasu, inda wasu suka rika cewa wai akwai matsala a auren, wanda wai hakan ya sa A'isha ba ta tare a can Amerika inda mijinta yake kasuwanci ba ko kuma Nijar inda sauran iyalinsa suke.

Jim kadan da daura auren na A'isha da Malam Atta, masoyan amaryar sun zaci cewa kasar waje kawai za a nufa da ita, amma dadewar lokaci sai suka ji shiru. A'isha ta tare a wani gida cikin Kaduna wanda mijinta ya kama mata haya.

A tattaunawar da maijegon ta yi da Fim kwanan nan, ta ce maganar fita kasar waje a gunta ba ta taso ba, domin har yanzu ba ta kammala karatunta na digiri a Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya, ba. Ta nuna rashin jin dadi kan yadda aka rika yin gulmar cewa wai mijinta ya yi watsi da ita har ta shiga saida kayan dakinta, ganin cewa ta koma gidan iyayenta da zama.

A'isha ta bayyana cewa ta koma gidan iyayenta ne domin gidan da mijinta ya kama mata ya yi mata girma, kuma tana jin tsoron zama ita kadai saboda ba ya kasar, kuma ga ta da ciki. Don haka ta koma gidansu har sai ya dawo. To, Allah ya raya Hadiza, kuma muna yi musu fatan alheri.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin