Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 46   Junairu 2004
LABARAI


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
HIRA DA DARAKTOCI
Wasiku
NEMAN MAFITA
SHARHI KAN FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
ADABI
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon FIM TA 45. Danna nan ka gani!
Bangon FIM TA 44. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 43. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 42. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 41. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 40. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 39. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM YA FITO!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

KASH! Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

'Yan wasa: Farida Jalal, A.A. Shariff (Momo), Kasimu Yero, Bashir Nayaya, Abubakar Yusuf Ladan, Hajara Usman, Sani Idris Moda, Sani Garba S.K, da Rashida Bello.

Darakta: Aminu A. Shariff

BABU IRINSA!

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Rikici a Sakkwato: An dakatar da 'Twins' daga SOFMA

Daga BASHIR ABU SABE, a Sakkwato

GA dukkan alamu, turka-turkar da ke tsakanin manyan jami'an Kungiyar Shirya Finafinai ta Jihar Sakkwato (SOFMA) da kuma matashiyar kungiyar shirya finafinai ta 'Twins' ta dauki sabon salo, domin kuwa ya zuwa yanzu an dakatar da ita kungiyar 'Twins' din daga duk wani aiki da ya shafi harkar fim a jihar.

Ita dai wannan dakatarwar ta biyo bayan taron da shugabannin SOFMA din suka kira a ranar Lahadi, 5 ga Oktoba, 2003 inda suka fayyace wa sauran membobin kungiyar irin halin da take ciki da 'Twins', da kuma irin matakan da take son dauka. A nan ne ta nemi shawarar sauran 'ya'yanta. Zarge-zargen dai da suka fi shafar shugaban kungiyar da jami'in yada labarai na SOFMA, Malam Sadiq Bello Jariri, ya karanto sun hada da:

"(i) Sun je Kano sun dauko 'yan wasa a kan N7,000 domin su zo Sakkwato su yi gala, an sallami wasu, wasu kuma ba su sami kudinsu ba, sai ma N10,000 da suka karba a wurin Gidigo da sunan ranar Litinin za a ba shi kudin, ranar babu kudin Gala kuma ba kudin da aka karba a wurinsa, muka ga nan gaba in furodusa ya je Kano dauko 'yan wasa ba za su zo ba.

"(ii) An samar ma kungiyar ofis, amma sai suka ce ba su yarda ba har suka yi sa-in-sa da M.Z. faru, sai muka fahimci ba da'a tsakaninsu da shugaban kungiya na jiha. Mun ja kunnensu, duk a banza.

"(iii) Mun soke gala a Sakkwato saboda ire-iren matsalolin da ake fuskanta a wurin, suka ki. Idan muka bari haka ta ci gaba da aukuwa, harkar fim za ta iya samun matsala a Sakkwato, sai ga shi sun je suka kara yaudarar 'yan wasa suka taho da su, suka bar su cikin wahala suna watangaririya, sai da M.Z. ya dauki nauyin binciko masu bikin, su kuma suka ce ba su saba yi ba, kuma ba su san an dauko su ba.

"iv) Sun kuma haddasa rikici tsakanin 'yan wasa da shugabannin shirin fim na jiha."

Sadiq Bello Jariri ya ci gaba da zayyana wa sauran membobi wadannan matsaloli da 'Twins' ke kawo wa SOFMA, inda ya kara da cewa, "Yanzu haka a Kano ana shakkar 'yan fim din Sakkwato." Sai dai ya ce har yanzu akwai wadanda suka tsare mutuncinsu kuma ake ganin mutuncin nasu a Kano. "Kuma a Kanon an san wanda ya yi wannan, hasali ma, dan Kanon ne ba dan Sakkwato ba," inji shi.

Haka zalika, Sadiq ya ce sun kira Hussaini domin ya zo ya kare kansa har sau uku amma ya ki zuwa, amma ya ce wadannan abubuwan duk a fili suke mutune sun gani, kuma wasu daga cikin 'yan wasan da abin ya faru a kansu sun tabbatar da haka, wato irin su Fati Baffa Fagge. Daga karshe Sadiq, wanda shi ne shugaban 'Algerian Films,' ya yi kira ga 'yan wasan Kano da su sani duk wani da ya je daukarsu su yi biki ko gala a Sakkwato to su yi yarjejeniya ya biya su daga can, kar su zo suna sukar 'yan fim na Sakkwato. Kuma ya yi kira ga Fati Baffa da Rukayya Dawayya musamman da ya ce su suka fi sanin wannan, don kada gaba a zo ana neman M.Z.

Da dama daga cikin furodusoshi na Sakkwato sun nuna bacin ransu game da wannan abu da 'yan 'Twins' suka yi, har wasu suka nemi a kori kungiyar gaba daya, amma wasu sun nemar mata sassauci. Daga karshe dai shuwagabannin sun dauki shawarwarin da aka ba su da cewar za su je su duba su.

A wani zama da shugabannin suka yi a ranar Lahadi, 12/10/2003, sun yanke hukunci kamar haka:

"1) Dole ne ku zama masu ladabi da biyayya ga shugabanin kungiya. 2) Dole ne ku bi tsarin mulki. 3) Dole ne ku cire Hussaini a matsayin shugabanku. 4) Dole ne ku rubuto takardar neman afuwa. 5) Dole ne ku daina gayyato 'yan wasa daga wasu jihohi don su yi gala. 6) Daga karshe, an sa maku takunkumi na tsawon wata uku ba tare da kun yi harkar fim ba a Jihar Sakkwato."

Wadannan dokoki dai da aka sa wa kungiyar 'Twins' sun fito ne daga hannun Sadiq Bello Jariri kuma takardar na dauke ne da sa hannun mataimakin sakataren kungiyar, Salis Yusuf Salihi.

To sai dai kamfanin 'Twins Productions' din da ma Hussainin da aka fi zargi duk sun musanta wadannan zarge-zarge da ake yi musu. Shi dai Hussaini ya musanta cewar ya san an hana gala a Sakkwato, kuma ya ce duk dan wasan da ya dauko daga Kano sai da ya ba shi rabin kudinsa. Hakazalika ya ce bai karbi kudin Gidigo ba. kuma bai yi suman karya ba, don kada ya biya 'ya wasan kudinsu. Sannan kuwa ya ce shi ba jayayya ya yi a kan ofis din da aka sa SOFMA ba, ya dai nemi karin bayani kuma an wayar masa da kai.

Game da bai iya zuwa Kano in dai yana da kunya kuwa, Hussaini ya ce gobe ma Kano zai je. Kuma sabanin abin da wasu ke cewa, Hussaini ya ce duk Kano ba wani dan wasan da ke binsa bashi. Daga karshe Hussaini ya yi jirwaye mai kamar wanka inda ya yi kira ga kungiyar SOFMA da ta dauki kuma ta ci gaba da daukar mataki kan duk kungiyar da ta saba ko ta taka dokokin tsarin mulki na kungiyar. Ya zuwa yanzu dai 'Twins' din ta tsige Hussaini a matsayin shugabanta, saboda ire-iren matsalolin da ya jajibo mata, inda ta nada dan'uwan tagwaicinsa, wato Hassan, a matsayin shugabanta.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin