Daga SANI MAIKATANGA
a Kano
A HARKAR fim, akwai fasihai iri-iri wadanda sam ba ka ji duriyarsu. A yayin da wasu ke cika gari da babatun cewa su ne kaza su ne kaza, wadansu ba ruwansu da wannan, illa kurum a ga aikinsu a gari. Daya daga cikin irin wadannan mutanen shi ne matashin darakta Yasin Auwal Musa, wato daraktan finafinai kamar Tashin Hankali, Cuta, Salo, Tiriri, da sauransu. Yasin yana daga cikin matasan daraktocin finafinan Hausa da suke ba da himma wajen gwada bajintarsu. Can kwanan baya mun hadu da shi a Kano, inda muka tattauna kan tarihinsa da kuma ra'ayoyinsa kan harkar fim.
Da farko dai, ya shaida wa mujallar Fim cewa an haife shi a unguwar Sarari cikin birnin Kano a cikin 1980. Ya yi makarantar firamare da sakandare. Yanzu yana karatu a Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya (F.C.E.) da ke Kano.
Yasin ya shiga harkar fim ne a wajen 1995, lokacin 'Sarauniya Production' suna farkonsu. "Su suka fara sa ni a cikin fim dinsu," inji shi. Ya kara da cewa, "Na yi sha'awar shiga harkar ne ganin yadda take tare da fadakarwa da nishadantarwa."
Da ya shiga harkar, a matsayin dan wasa ya shiga. Ya fara da fim din Gagare, sannan Tantiri, "daga nan sai harka ta dan yi sanyi."
To, yanzu dai Yasin ya rikide zuwa mai ba da umurni. Shin yaya aka yi ya kai wannan matsayin? Yasin ya amsa: "Bayan harkar ta dan dawo ne sai ni da wasu abokaina muka shirya wani fim mai suna Zanen Dutse, wanda Ishaq Sidi Ishaq ya yi daraktin. Bayan mun koma za mu sake yin wani ne sai muka samu Ishaq yana yin wani aiki. Sai na ce, "Me ya sa ni ma ba zan gwada ba in gani ko Allah zai sa in dace? Sai kawai na yi wannan fim mai suna Tashin Hankali. Kuma daga nan sai masu fim din Cuta suka ba ni fim dinsu na yi daraktin."
Ba da umurni a Tashin Hankali da Cuta ya sa aka fara yi wa Yasin wani kallo. Bai samu kwanciyar hankali ba duk da yake ba a kalle shi a matsayin mai cuta ba. Surutu aka fara yi wai yana yaro ya fara aikin ba da umurni. Wayyo, ashe mai rabon ganin badi sai ya gani, kuma hassada ga mai rabo taki ce. Domin kuwa manyan daraktoci sun hango cewa yaron yana da basira da fasaha. "Sai Hafizu Bello ya ji, sai ya kira ni na yi msa Assistant Director a wasu finafinansa, kuma marigayi Tijjani Ibraheem shi ma ya dada ba ni karfin gwiwa a kan abin. Daga lokacin da na fara zuwa yanzu na yi finafinan kamar bakwai; su ne Tashin Hankali, Cuta, Tsantsar So, Salo, Tiriri, Murmushi da sauransu."
Matashin daraktan ya yi tsokaci kan batun tabarbanewar harkar fim a yanzu. Ya ce, "Gaskiya wannan wani abu ne wanda kusan mu ne muka haddasa shi."
A yanzu Yasin shi ne darakta a kamfanin nan da ke shirya fim tare da editin da buga waka mai suna Afandaj, wanda ke Zoo Road, Kano. Lokacin da muka yi wannan hirar da shi, ana cikin shirin zuwa gasar nunin finafinai ta kasa wanda aka yi a watan Oktoba da ya gabata. Mun tambaye shi irin rawa da yake ganin finafinan Hausa za su taka a gasar. Yasin Auwal ya ce, "Komai ai na Allah ne, amma za mu shiga da finafinanmu kuma za mu nuna irin bajintarmu kuma za a yi mamakin ci-gaban da muka samu."
A kan fadar da wasu ke yi cewa 'yan fim din Hausa ba su da wani fim da zai taka wata rawa a gasar, daraktan ya ce, "Su waye suka fada? Ai duk wanda ya fada ma to shi ne ba shi da fim din da zai shiga wannan gasar da shi... Kuma ni ma ina da fim din da zan shiga gasar da shi."
A kan yin adawa ko gasa a industiri, musamman tsakaninsa da sauran daraktoci, Yasin ya ce: "Ni ba na fada da kowa. Amma wai akwai wadanda su suke cewa wai suna adawa da ni, amma ni ban dauke su a bakin komai ba domin ni ba wanda ya tare min gaba, harkokina kawai nake yi, ni ban san ma suna yi ba."
Kai da jin wannan kalamin ka san na mutum ne wanda ya san abin da ya taka. To a karshe wace shawara zai bayar ga sauran 'yan'uwansa 'yan fim? Yasin Auwal: "Don Allah kananan daraktoci su daina surutun manya suna musu bakin ciki - wai suna samun aiki. Kuma don Allah ku manyan ku yi hakuri da duk wani abu da muka fada, duk komai mai wucewa ne."
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin