SHIN da me zan ji? Da mutuwar Balaraba ko da satar da aka yi mata a ranar da ta koma ga Mahaliccinta?
Na san za ka yi mamakin jin cewa an yi satar a daidai wannan lokacin da muke cikin garari. To, karkade kunnuwanka ka sha labari.
Wata 'yar wasa ce mai suna Hadiza, wadda ta zo bikin daga Kano, ta dibga halin beran a gidan su Marigayiya. A kan idon Mukhtar M.D., furodusan fim din Tafiya da fim din Dan Gajarma, aka yi komai. Mukhtar yana gidan lokacin da aka kai gawar amaryar ta Kumurci da ta sauran wadanda suka mutu. Kuma da shi aka je makabarta.Ya shaida mani abin bakin cikin da aka tafka:
"Ni dai a gabana Amarya ta tashi zuwa Kano da misalin karfe 3:30 na rana. Bayan wani lokaci sai aka fara kawo gawar yarta, jami'an 'Road Safety' suka yi mana karya cewa yar Balaraba ce kadai ta rasu. Da ni aka kai wanta asibiti bayan ya samu raunuka a kansa."
Mukhtar ya kara da cewa bayan an dawo daga rufe su Balaraba ne abin kunyar ya faru. An nemi kudin da za a gyara wa wan amarya targadensa, sai wasu kawaye suka ce ai akwai kudi a cikin jakar Balaraba, a tambayi Hadiza, wata mai hakorin Makka, domin ita ce ta dawo da jakar. Da aka tambaye ta sai ta ce ita ba ta ga kudi ba a jakar. Abinka da mata, sai aka ce a caje ta. Ballagazar ta ki. Haba, ai sai kawaye, ciki har da 'yar wasa Maijidda Abbas, suka kayar da ita suka danne ta suka kwance maza zane. Sai ga tudun kudin a cikin pant dinta. Suka zura hannu suka jawo damin kudin, N20,000 kuma duk 'yan Murtala ne sababbi kar. Daga cikinsu aka biya kudin targaden da Abdullahi ya yi a hannunsa. "A gabana aka biya kudin," inji Mukhtar.
Tsinuwar da Hadiza ta sha a lokacin, na bar maku sani. Ita ko ta sha toka kawai, ta bar gidan. Ka ji karfin hali! Malamai, wannan rashin imanin har ina! A ce an yi mace-mace irin wadannan, maimakon ka kawo sadaka ka bayar, amma ka dibga sata a dakin uwar Amarya lokacin ita ma an kai ta asibiti saboda zautuwa!
Haba!
... Assha, wasu jarumai sun sha mangara!
A BIKIN Balaraba, wasu jarumai ba su sha da dadi ba. Ga shi dai taron taya murna suka zo, amma da yake zamanin dukan masoyi ne yanzu, sai suka gamu da fushin nigogin Kaduna.
Bari ka ji yadda abin ya faru. Maganar yawan jama'a dai a kofar gidan su Amarya, abin ba a cewa komai. Taro ya yi taro. Su kuma 'yan fim, sai wandaka suke yi, domin suna zaton sun shigo cikin masoyansu. To, an kuwa nuna masu kaunar - amma fa ta wata hanya. Da yawansu da suka zo daga Kano, duk wanda ya sauka a mota ko ya karaso a kasa daga tasha, sai 'masoyansa' su yi masa caa. Mutane ba abin da suke so illa dan wasa ya yi masu magana, wasu kuma kokari suke yi su ga cewa ko rigarsa ce sun taba domin samun tubarraki.
To, wasu daga cikinsu tsallake rijiya da baya suka yi. Misali shi ne wani shahararren jarumi da ya rikide furodusa. Dirarsa wurin ke da wuya sai jama'a suka ce da wa aka hada mu ba da kai ba. Da yawa suna so su gaisa da shi. Tun yana amsawa har ta kai ga shi ma ta kansa yake yi don ya samu sararin da zai sha iska.
Abinka da taro irin wannan, dole ne mutum ya samu makiya. Ga alama, fitaccen jarumin ya dauka kowa sonsa yake a wurin, don haka yana ta haba-haba da su. Can sai ya fara jin saukar duka; makiya sun iso kenan! Kai, sai da ta kai an yaga masa riga. Bai samu sa'ida ba sai da ya shige wata mota bas, kirar C20, sannan jama'a suka kyale shi. Illa dai aka kewaye shi, kamar an je gidan zoo ana kallon wata irin halitta ta daban.
Shi ko wani jarumin, wanda shi ma ya auri wata shararriyar jaruma, wani shirgegen kato ne, madakin kare, ya same shi a tsaye. Bai tsaya wata-wata ba kawai sai ya ce masa, "Ina amaryarka?" "Tana gida," inji shi. Ya dauka abin arziki ne.
Ai kawai ba zato ba tsammani sai katon mai kama da dan kokawar nan Hulk Hogan ya dake shi a kirji, bakinsa na kumfa ya ce, "Kai, mu masoyan Wance ne! Mun ji ka saki wance! To wallahi idan ka saki Wance, kashinka ya bushe!"
Da abokinmu jarumi ya ga abin ba na arziki ba ne, nan da nan sai ya rikide, ya koma Mike Tyson. Ya tube don a kwafsa din; saboda shi ma ba kashin yadawa ba ne, domin ya taba yin zaman tasha, lokacin da ya yi sana'ar yi wa tireloli iska (har ya samu wani shahararren lakabi). Kwatsam, sai ga bos din nan na fim, wato Sinana. Shi kuma da zuwansa sai shi ma ya tube zai agaji jarumin da ake badakalar da shi. Ganin abin zai kazance, sai aka raba su.
Shi ko wancan dan sholishon, ya kama gabansa. Ba a jima ba kuma sai ga Damisa ya iso wurin. Da ya ji abin da ya wakana, shi ma sai ya tube, ya doshi inda dansholishon ya bi, amma aka tarbi gabansa aka ce don Allah ya yi hakuri. Ni ko ina ta kallonsu, duk dariya ta kama ni. A raina na ce, "Lallai su Wane sun gamu da masu son su. To amma su sani akwai makiya a bayansu, kuma su rika yin taka-tsantsan."
Su waye Balaraba ke bi bashi?
SAKAMAKON wani dan bincike da na gudanar, na gano cewa marigayiya Balaraba Mohammed tana bin wadansu furodusoshi kudin da ta yi masu fim amma ba su kai ga biyanta kudin ba. Wasu sun ba ta wani abu cikin kudin, da nufin cika mata kudinta kafin ta yi aure, kobayan ta yi.
"Ya kamata su dubi Allah su gaggauta biyan wadannan kudade ga magadanta," inji wani dan wasa da muka yi maganar da shi.
Shin furodusoshi ne za su taru su tattauna wannan magana ko kuwa? Zai kyautu a kafa wani kwamiti don gano wadanda take bi bashi. Idan kuma tana bin ka amma ba a dago ka ba, to ka je ka biya kudin. Ya fi a ce ka dake sai an je Can inda ta je, inda kuma kila ba ka maganin ko kwandala.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin