Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 29   Mayu 2002
MALAM ZURKE


BABBAN SHAFI
Mu Leka Mu Gani
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 1
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 2
Rayuwarmu
Mu Leka Hollywood
Malam Zurke
Mutanen Boye
Bukukuwa
Sauran Labarai
Ra'ayi Ba Gaba ne
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Akwai:
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


Watakila ni zan sayi gemun Maishunku!

NA san ba kowa ne ya gaskata labarin wani ladani da ya sayar da gemunsa a cikin Magana Jari Ce ba. Ba don komai ba sai don gani mutum zai yi tamkar abin almara ce. To irin wannan ya faru kwanan nan a cikin 'yan fim (koda yake abin bai wuce ba).

Tun da na rika ganin jarumi Ibrahim Maishunku da gashi a habarsa na san akwai dalili. Ba wai ba shi ajiye wa ba, a'a yanzu dai gashin ya fi tsawo.

Da na kasa daurewa sai na yi tambaya. A nan ne wani furodusa ya ce min ai Maishunku wani fim zai yi mai suna Laulayi, shi ya sa yake barin gemunsa ya yi toho domin yana so ya fito da dogon gemu a cikin fim din. Wato dai kamar yadda aka sa jarumin nan na Amerika,Tom Hanks, ya aje kasumba har tsawon shekara daya saboda yin fitaccen fim din nan da ya fito a bara, wato Cast Away. A halin da ake ciki yanu dai, Maishunku ya bar gemun sai toho yake yi. Ko zai yi harkiya kamar na Tom Hanks, oho!

Su kuma furodusoshi, ganin kyawon gemun tuni har sun fara cinikin gemun. Don Allah, Maishinku kada ka aske shi, har sai ka yi masu fim da shi.

Na ji a wata majiya mai inganci cewa tuni har wani matashi furodusa mai suna Abdulhadi (furodusan Kauna da kuma Inganci) ya tuntubi Maishunku, sun tattauna kan hadahadar yi masa tsimin gemun har lokacin da zai fara wani sabon fim. Ni kuma na zuba ido daga nan har lokacin da za a fara Laulayi in ga ko gemun Maishunku zai iya kai zira'i hudu. Wa ya sani? Kila ma da ni za a yi cinikin.

Sam, ba Superstar Hadiza Kabara ba ce!

KAI, lallai mutane akwai su da neman makala wa mutum kayan kwalba - wato sharri! Wai dan labarin nan da na ba ku na wata barauniya mai suna Hadiza wadda ta bulla a gidan su marigayiya Balaraba a Fim ta watan jiya, shi ne wasu suka yi zaton ko jaruma Hadiza Kabara ce. Wai!

Rannan Hadiza Moh'd Sani (Kabara) din da kanta ta zo har zaurena ta gaya mani abin da wasu ke cewa. Na ce ni ma na ji rade-radin. Nan take na ba ta hakuri. Daga baya ma na ji an ce su kansu iyayenta abin ya dame su. Ban ga laifinsu ba.

Ni ma abin ya dame ni, domin a gaskiya ba Hadiza Kabara ba ce ta yi satar kudin marigayiyar. Ita barauniyar, na bayyana kamannunta, na ce fara ce, tana sa hakorin Makka. Idan ka ga Kabara, ka ce mata ta bude hakorinta ka gani ko tana da hakorin Makka; kai, ko ma tana da shi, ba ita ce ba!

Ita waccan, sabuwar 'yar wasa ce wadda har yanzu ban taba ganinta a fuskar talbijin ba. Ina dai ganinta tana ragaita a ofishin darakta Tijjani Ibraheem tare da fatan ko zai saka ta a fim. Saboda rashin ficenta, na kasa samun hotonta, da na lika shi a wannan zauren kun gan ta.

Bari in gaya maku wani abu game da Hadiza Kabara. A'a, ba cewa zan yi budurwar darakta Mohammed Garba Kabara ba ce (saboda shi ne ake ce mata Kabara). Cewa zan yi yarinya ce ta kirki, wadda ba ta sa komai a gabanta ba sai yadda za ta kara inganta aikinta na fim. Wannan ya ba ta dama har ta zama Superstar. E, na san an taba yin barauniyar Superstar, to amma Hadiza Kabara ba ta cikin wannan da'irar ta 'ya'yan kusu.

Can ga su gada!

Zurke ka jahilci aikin banki

Assalamu Alaikum,

BAYAN gaisuwa mai yawa da fatan kana lafiya. Dalilin rubuto wannan takarda tawa shi ne domin na yi maka gyara a bisa wani kuskure. Na karanta sharhinka mai taken "Ayyuriri! 'Yan fim sun yi selula!" a cikin mujalla ta watan Maris. A ciki ka yi maganar wata da ta ce maka ta yi amfani da layin GSM ta kira bankinta su kuma sun aiko mata da bayani a kan account dinta. Ni a matsayina na ma'aikaciyar banki, na san wannan magana da ta yi akwai gaskiya a cikinta. Akwai wani abin da muke kira electronic banking. A karkashinsa akwai telephone banking, internet banking, da mobile banking, kuma duk wannan ana iya amfani da su domin samun labarin account a kowane lokaci kuma a kowace rana.

Saboda haka, Malam Zurke, idan nan gaba za ka sake sa labari a shafinka ka tabbatar ka yi bincike. Don idan ba ka yi hankali ba, za ka tozarta kanka tare da nuna jahilcinka a fili. Allah ya ba ka ikon sayen taka GSM din! Ka huta lafiya

Lantana Musa,

Hajiya, na yi murna da jin wadannan kalaman naki. Batun electronic banking, idan kin lura har yanzu bai kankama ba a nan kasar, don haka mutum ya buga wa bankinsa waya ya ce a ba shi kididdigar kudin da ke cikin asusunsa, bai taso ba. Hasali ma, ni bankin da nake zuwa, sai sun gan ni ido-da-ido, kuma sun ga katin I.D. wanda hotona ke jikinsa, kafin su gaya mani yawan kudina da suka rage. Kila dai a nan gaba kadan ku gyara aikinku na banki don tafiya da zamani; ya zuwa lokacin ni ma kila na yi GSM, sai in bugo ku ba ni balance dina.

Wassalam.

M. Zurke

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin