Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 30   Yuni 2002
MALAM ZURKE


BABBAN SHAFI
RA'AYI
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) 
Rayuwarmu
Duk Sun Yi Aure
Malam Zurke
Ra'ayin Mujallar Fim
Bukukuwa
Sauran Labarai
Ra'ayi Ba Gaba ne
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


YADDA 'YAR WASA TA SA AKA KULLE FURODUSA

IDAN har dai mutum bai rike girmansa ba, to yana tare da jin kunya. Shi ya sa Hausawa kan ce wanda bai ji bari ba, ya ji hoho.

Kwanan baya ne wani abin kunya ya faru a Zariya cikin Jihar Kaduna, a yayin daukar wani fim mai suna Nasir wanda wani furodusa mai suna Hamza Ahmed ya shirya, kuma kamfanin shirya finafinai na 'Ya-Kareem Ventures' ya shirya. Kamfanin, wanda yake a Tudun Wadar birnin na Shehu Idrisa, yana da daraktoci guda shida. Shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kaduna, Adamu Bello (Ability) ne yake shugabantarsa. Su ne suka jagoranci wannan shirin fim din.

To, a ranar Asabar, 13 ga Afrilu, 2002 'yan wasa suka taru a harabar ofishin, suna jiran a fara yin fim din wanda Adamu Ability yake a matsayin mai ba da umarni. A wurin akwai wata yarinya mai suna Hadiza Usman wadda aka fi sani da suna Hadiza Kisisina. Kada ka dauka sunanta halinta ne; ta samo sunan ne a wani fim din Zazzagawa mai suna Kisisina; hasali ma ita ce jarumar fim din.

Hadiza tana hira da wata kawarta, tana cewa ita tana mamakin wadansu 'yan fim, musamman mata, da ke ba da kansu ga wadansu furodusoshi har ya kai ga an yi zina da su, ta ce bai dace a ce mai mutumci ta yi haka ba. Ta ce irin wadannan matan suna aikin assha ne don a saka su a fim. Hadiza tana magana ne kan wata mishkila da ke neman ta zama ruwan-dare a harkar fim.

Ashe duk hirar da suke yi suna yi ne a kan kunnen daya daga cikin daraktocin kamfanin wanda kuma shi ne Odita na Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kaduna mai suna Nasiru Danmaliki. Sai kwatsam ya tsulma masu baki ya ce ita Hadiza karya take yi, wai ya taba ganinta a wani wuri da wani saurayi inda ake tafka barna (watau zinace-zinace). To fa, ashe ya tsokano tsuliyar dodo! A nan ne sai Hadiza ta bukaci Nasiru ya gaya mata inda ya taba ganinta din. Sai ya ce shi ba zai fada ba. Ai fa sai jarumar ta fusata, ta tsare shi tana cewa idan bai gaya mata ba to ita ko za ta dau mataki domin, a cewarta, har in dai aka tashi bai fadi inda ya gan ta din ba, to jama'a da ke wurin za su dauka ita gantalalliya ce. Ta yi ta yi da shi ya fada, ya ki. Sai ta fara kwara masa ashar. Nan da nan shi kuma bai yi wata-wata ba sai ya kashe ta da mari. Ho da! Ka ji namiji!

Wannan abu ya faru ne da misalin karfe 11 na safe, kuma a gaban dimbin 'yan fim da suka zo daga garuruwa daban-daban, ciki kuwa har da wakilin Malam Zurke.

Ashe Nasiru bai san abin da ke gabansa ba. Da tashin Hadiza ba ta zarce ko'ina ba sai hedikwatar 'yan sanda wadda ke unguwar G.R.A., ta shigar da kara ga sajen da ke kanta. Nan da nan sajen ya umurci da a zo da Nasiru Danmaliki. Aka kuma zo nan 'Ya-Kareem Ventures' aka tasa keyarsa, sai caji ofis. Da aka isa, sajen ya gaya wa Nasiru cewa Hadiza ta yi kararsa a kan ya mare ta kuma ya yi mata kazafi. Sai Nasiru ya amsa cewa shi ya san ya mare ta amma shi ba wani kazafi da ya yi mata. In dai takaice maku labari, a nan aka sakaya Nasiru, ita ko Hadiza ta dawo masauki (location).

To, a yayin da ake wannan hatsaniya duka daraktocin kamfanin ba su a wurin; hatta shi shugaban kamfanin ya je ganin wani wurin daukar shirin fim din (location) tare da furodusan fim din, wanda ya je ya nuna masa. Can sai Ability ya shigo. Aka gaya masa abin da ake ciki. Nan da nan sai ya garzaya gun 'yan sanda don neman belin Nasiru. Sai sajen ya ce ba zai ba da beli ba sai in har yarinyar da ta kawo karar ta zo da kanta.

Buzum-buzum Adamu Ability ya dawo masaukin 'yan wasa domin ya ga Hadiza su tafi ofishin 'yan sanda. Bai yi dace ba, domin kuwa a lokacin da ya tafi wurin 'yan sandan ita sai ta bar wajen ta tafi cikin birni. Aka yi nemanta ruwa a jallo ba a gan ta ba sai bayan misalin karfe 6 na yamma. Daga nan aka garzaya tare da ita ofishin 'yan sanda. Da isarsu sai suka hadu da wadansu furodusoshi wadanda da suka ji labarin abin da ya faru, sai dukkansu suka shiga cikin ofishin. Da shugaban furodusoshi Adamu Bello ya gabatar da kansa ga sajen mai binciken rigimar kuma ya shaida masa cewa sun zo karbar beli ne, sai sajen ya ce ya kamata su je ne su sasanta da ita Hadiza, idan ta yafe to ana iya rufe karar. A nan ne fa furososhi suka yi mata magana kuma ta amince. Sai dai ta ce a yayin rigimarsu ta yi asarar kudi kimanin N1,000. Sai shugaban furodusoshin ya ce za a biya ta. Nan take kuwa ya biya ta. Aka je aka fito da Nasiru Danmaliki, duk jibi ya rufe shi. Kun ji inda tasa ta kwashe.

Shi ya sa nake rokon furodusoshi don Allah su rinka rike girmansu, don su kare mutuncin sana'arsu. Abin da ya faru a Zariya abin kunya ne kwarai da gaske. In muka duba, Nasiru babba ne a wannan harka; ita ko yarinya ko banza ya isa ya haife ta kuma ga shi ya sha wakiltar Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kaduna a wadansu jihohin. Ba ajinsa ba ne husuma da 'yar wasa har a karshe ma ta sa ya shafe awoyi a sel din 'yan sanda.

Wanda ke son ya ga hoton Hadiza, to ya duba filin 'Mu San 'Yan Wasa' (a shafi na 42).

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin