Ku zo mu kafa Kungiyar 'Ya'yan Mohammed
SUNAN Mohammed, babban suna ne. Shi ya sa muke addu'ar Allah ya sa mu ga mai wannan sunan idan mun cika (ba a Sabon Titi ko Zoo Road ba). Bari ku ji inda na dosa. Tun daga lokacin da aka fara harkar finafinan bidiyo na Hausa, ko tantama babu 'Muhammadu' ne ya fi kowa kafa tarihi da kuma cin moriyar harkar. Ba wani dalili ya sa na fadi haka ba illa kawai yadda na duba na ga cewa duk wani da na Mohammed da ya tashi sai kawai ya shiga fim, namiji ne ko mace, yaro ko babba. A maza ga Ibrahim Moh'd Mandawari; Tahir; Danhaki, da Saminu. A mata kuma ga su Fati (har su biyu) da Halisa da Abida tuni sun ci kasuwar fim sun nade kaya sun kwashe ribarsu. A kan layin aure kuma ga su Asiya da Hadiza.
Baba Mohammed ya yi rashi kwanan baya, inda 'yarsa Balaraba Mohammed ta rasu a hadari bayan ta yi aure da kwana daya. Allah ya jikanta, amin!
Wani abin sha'awa shi ne da wuya ka ga 'ya'yan Mohammed suna raba-darni a shirin fim. Duk wanda ya shigo daga cikinsu, namiji ne ko mace, sai ya yi fice. Akwai furodusoshi, 'yan wasa da daraktoci duk cikin 'ya'yansa. Wannan ya sa wanda ma ba dansa ba ne, wata sa'a in ya shigo Industry sai ya yi wa kansa inkiya da sunan.
Yadda Mohammed ke jan akalar rayuwar 'ya'yansa mata a cikin harkar fim abin sha'awa ne matuka; duk wadda ya fahimci ta yi tashe, sai tashi daya ya kai ta gidan miji. Ban da Balaraba da ya aurar, kuma ya aurar da wasu 'ya'yan nasa, zafiya mai kaifin murya Maryam Mohammed (wadda Momo ya aura), da kuma Abida. Na tabbatar 'ya'yan suna da dimbin yawa a fim. A Jos da Kaduna da Sokoto duk akwai 'ya'yansa da ke fim wadanda duk na cikinsa ne ba 'yan riko ba. Kai, ba da dadewa ba wata sabuwar 'yar wasa ta fara fitowa. Kun san sunanta? Wai Fati Mohammed! Sai dai ita wannan Fatin ba Bafillatana ba ce. 'Yar cikin Kano ce, a unguwar Gabari.
A yau dai ga wata dabara da zan ba su. Ya dace su kafa Kungiyar 'Ya'yan Mohammed A Shirin Fim. Kuma na tabbatar za ta iya zama wata mafita. Za ta iya zama Mafia, ta juya harkar yadda ta ga dama!
Ina Sarkin Mu Shakata? Me ya sa ba za ka yi Mu Shakata na 6 da 'yan fim zunzurutun kannenka da yayyenka da kuke uba daya ba ('yan uba!)? Ai kuwa da ka aje tarihi, a ce furodusa dan Mohammed, darakta dan Mohammed, mai daukar hoto dan Mohammed, a yi shirin fim din a gidan Mohammed, dan Mohammed ya yi editin, dan Mohammed ya tace, dan Mohammed ya sayar, duk su kasance kannenka maza da mata 'ya'yan Mohammed! Sai dai kash! akwai wasu sababbin 'yan wasa daga cikinsu har akwai mata masu sunan uba Mohammed. Suna yawo suna tsilla-tsilla daga wuri zuwa wuri wai su ma 'yan fim ne. To ka ja masu kunne, ba fim suke ba, yawon-ta-zubar kawai suke yi. Idan da hali a kore su su koma gida. Kuma akwai wasu mutum biyu, maza, wato "O'o Mohammed O'o," wadanda dabi'arsu ta saba wa ka'idojin wannan kungiyar ta mutanen da suka san abin da suke yi. Kada a bar su su shiga su ma, kada su bata yara a banza!
A nan kasa, ga jerin sunayen 'yan fim da za su iya zama membobin farko na sabuwar kungiyar da nake ba da shawarar a kafa. Ga su: Abdulkarim Mohammed; Ibrahim Mohammed Mandawari; Zulkifilu Mohammed; Sani Mohammed Sani; Fati Mohammed; Abida Mohammed; Hamza Mohammed Danzaki; Hadiza Mohammed Sani Kabara; Mohammed Garba Kabara; Ibrahim Mohammed Sheme; Maryam Mohammed (Mashahama); Maryam Mohammed (amaryar Momo); Yakubu Mohammed; Sa'adiyya Mohammed; Ladi Mohammed; Mustapha Mohammed (Danhaki); Abdurrasheed Mohammed (Abab); Ado Ahmed ko Mohammed Gidan Dabino; Hafizu (Mohammed) Bello; Saima Mohammed Raga; Saminu Mohammed Mahmud; Amina Mohammed Lamido; Mohammed Munzali Moh'd (Yoko); Abba (Mohammed) Lawan Daneji ('Yallabai); Adamu Mohammed Bello (Ability); Shu'aibu Mohammed Lawan (Kumurci); Bala Mohammed Bachirawa; Musa Moh'd Abdullahi; Akilu Moh'd (Baban Mulika); Adamu Moh'd (Kwabon Masoyi); da Rabi'u Moh'd Rikadawa.
Malam ko malama, idan ba ku ga sunanku ba, ku aiko da shi a sa ku a rijista. Amma ban da su "O'o Mohammed O'o" masu bata samari!
Na ku, Malam Zurke 'Mohammed', Sakataren Riko na kungiya
In da a ce nine Lere…!
WAI wai wai wai!!! Shin wai Mai Martaba Dan Iyan Zazzau Alhaji Yusufu Ladan bai san ko wanene Yakubu Lere ba, da har zai tsaya a gaban jama'a yana sukar fim dinsa? A ran 1 ga watan jiya ne aka je taron kaddamar da fim din Kaddara, wanda Lere ya shirya. Sai aka kawo dattijon nan Alhaji Yusufu a matsayin babban bako mai sharhi. Mu mun dauka idan ya zo zai yi yadda ake so ya yi ne kurum ya tafi gida, wato ya yi ta koda fim din. Mun manta cewa zai yi yadda ya yi a wurin kaddamar da shirin Taskira can a cikin 1999. To, sai kawai na ji wannan tsohon marubucin diramar yana sukar fim din, har da cewa wai akwai wurare da ya saba wa al'adar Hausa da kuma Musulunci. Ha! Ai sai gabana ya fadi. Sai na shiga tunani: shin 'Yallabai bai san cewa ba a sukar Lere ba ne ko wani abu da ya aikata? Bai san cewa Lere na iya maka shi a kotu ba, a bi masa hakkinsa? Ko kuwa yana ganin don kurum yana da masaniya kan harkar dirama sai ya zo yana sukar aikin babban furodusa, wanda ya yi suna wajen ja da ko waye a kasar nan? Ko kuwa yana ganin don yana Hakimin Kabala shikenan sai ya zo ya zuba kasa a cikin garin muhimmin mutum irin wannan wanda ba ya laifi? LERE fa aka ce, ba wani dan ku-ci-ku-ba-mun furodusa ba irin su Wane. Mutumin da yake da adireshin e-mail, da First Lady, da gida, da ofis hadadde, da selula, dukkansu sabbi ful, kuma ga shi zai auri yarinya wadda ta fi kowace yarinya kyau a duk fadin Kaduna (in ka debe Kabala!)!! Lere fa aka ce, malam, wanda ya buga da gwamnati, ya buga da Maikano, ya buga da Ability, ya buga da Mandawari, kai har malaman jami'a da 'yan jarida fa ya buga da su, duk sun bar shi! Malam, Lere fa aka ce! Mu fa yanzu a fagen shirin fim ba a sukarsa. Ina dai jin Dan Iya bai san haka ba. To, gaskiya da ni ne sai in nemi Kungiyar Arewa ta kira taron sasantawa da hakimin, in ba haka ba kuwa ... to, zan iya ganin lauyana ba wani bata lokaci. Lere fa aka ce Malam!
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin