Anya su Bush din Kano za su kyale 'yan Alka'idan Industry su kai labari?
DUK wanda bai san Usama bin Ladin ba, to bai san abin da duniya take ciki a yau ba. Mu dauka ba ka san shi ba; to, shi ne shugaban rundunar mayakan kasar Afghanistan din nan, wato Alka'ida, wadanda suke yaki da Amerika da Turai bayan Turawan sun rushe gwamnatin kasar ta 'yan Taliban. To ya aka yi aka samu 'yan Alka'ida a fagen shirin fim? Bari ka ji.
Sanin kowa ne duk inda ake shugabanci ko jagorantar al'umma, akan sami masu yin kuka da irin jagorantar da ake yi masu. Wannan ne idan ya yi kamari yakan haifar da 'yan adawa. Idan ya kazamce kuwa, akan kai ga samun wasu tsiraru ko jama'a masu yawa su ware su koma 'yan tawaye.
To ko a cikin harkar fim din Hausa, abin haka yake domin duk inda wasu suka hau jagorancin wata kungiya, za ka ga an samu masu adawa da su. Tun can baya an sha kokarin kafa kungiyoyin da za su yi adawa da shugabancin kungiyar furodusoshi ko kuma ta 'yan wasa a Kano. Yin hakan kan hadu da cikas sakamakon rashin maida hankalin wasu, ko kuma a sami wasu sun shigo ciki don su bata al'amarin.
Amma kwanan baya a Kano sai wata kungiyar matasa ta bullo da nufin "kwatar 'yancinsu" daga zaluncin da suka ce manya na yi masu. Mafi yawa sun gudo ne daga wasu kamfanonin shirya fim inda suke ganin an mayar da su gugar yasa, wasu kuwa ba su yarda su zama bayin wasu ba. Dadin dadawa kuma akwai abubuwan da suke ganin ya dace a ce suna gudana amma ake samun akasin haka.
Burbushin wannan yunkuri na 'yan a-ware ya samo tushe ne daga lokacin da wasu matasa shida, wadanda suka hada da fitaccen mawaki Mudassir Kasim, suka balle daga wani shagon shirya fim da ke Gwammaja. Kwatsam, cikin azumin da ya wuce an rika ganinsu a wani wurin da ba a zata ba, kofar ofishin 'Usmaniyya Production' na Musbahu M. Ahmad, suna yin buda-baki. Shi ma Musbahu 'gudajjen bawa ne' (kamar yadda yake kiran kansa). Sai majalisar tasa ta zama matattarar matasan 'yan wasa masu yin tantado don kaiwa inda na gaba da su ya kai. Da ma wasunsu suna korafi da cewa su kansu wasu daga cikin "manyan" tsawonsu bai kai ba, su ake takawa kurum.
Su kuma wasu 'yan fim da suka fara yi wa majalisar Musbahu kallon fandararru, sai suka rika kiran wurin da sunan "Tora Bora." Kun san Tora Bora? Tsaunukan Afhanistan kenan inda Amerika ta yi luguden bamabamai don rarako 'yan Alka'ida take zaton sun buya a ciki, ciki har da Usama. Ma'ana, an rika yi wa majalisar wani kallo tamkar ta 'yan Alka'ida. Daga nan ne su kansu da kuma sauran wasu matasan 'yan fim suka garwaye da "'yan Tora Bora" suka sake lakaba wa kungiyar tasu suna 'Kandahar'. Kandahar dai wani babban birnin Afghanistan ne inda nan ma Turawa suka yi ruwan bom don fiddo 'yan Alka'ida.
A duk rana ta Allah 'yan wannan kungiya sai karuwa suke yi. Abin ya fito fili duk kuwa da cewa har yanzu ba su fara aiwatar da ko da daya daga cikin manufofinsu ba. Kawowa karshen watan Yuni, 'Kandahar' tana da membobi masu yawan da har wadanda ba su cikinta suna kiransu da suna 'G.50'.
Shin da gaske sun kai hamsin din? Suna da karfin shanye ruwan bamabaman da babu shakka manyan furodusoshi da daraktoci (wato su George W. Bush din Kallywood) za su yi masu ta hanyar kutungwila da furofagandar zahiri da ta badini? Su wanene shugabannin 'yan 'Kandahar' din yadda ko kazar-karfi aka sa tsakaninsu da manyan furodusoshi ba za su ji shakku ko yin tababar dauka ba? Ga shi da ma kajin wasu manyan kamfanoni sun fara karwa, an fara barinsu da 'as kaji.' Don jin amsar wasu daga cikin wadannan tambayoyi, wakilina ya karbi bakuncin fitaccen jarumi Aminu Ilu Dambazau wanda tun kafin 'Kandahar' ta yi zabe ya nada gammo an dora masa shugabancin kungiyar.
TAMBAYA: Aminu, me ya yi zafi har kuka sa wa kanku wannan suna? Wani hakki kuke son kwatowa da karfi ko da tsiya?
AMINU: E, to gaskiya mun kafa kungiya kam, amma maganar tawaye ko wani abu makamancin wannan, sam babu wannan tsari a cikin kungiyar.
TAMBAYA: Idan haka ne, menene dalilin kafa kungiya taku ta matasan 'yan fim zunzurutu?
AMINU: Babban dalilin kafa kungiyar shi ne domin nema wa kanmu wani matsuguni da kuma 'yanci daga irin kalubatantar da muka fuskanta daga wasu daga cikin masu yin wannan harka sabanin irin abubuwan da sukan taso a yanzu. Shi ne muka ga me ya kamata mu yi? Muka ga a matsayinmu na samari matasa mu kafa wata kungiya don kanmu da kuma ci-gaban kanmu da kammu.
TAMBAYA: An ce kungiyar ta kunshi 'yan wasa, furodusoshi, masu rike kyamara, mawaka da sauransu.
AMINU: E haka ne. Ina so ka fuskanci wani abu daya. Mun riga mun san a Jihar Kano akwai kungiyoyi da muke da su kamar Filmmakers Association da Council of Artists. Wadannan kungiyoyi ba su da wani abu da suke yi domin ci-gabanmu ko kwatar mana hakki. Don haka muka ga me zai hana mu ma mu yi kokari mu fito da wani reshe a cikin kungiyar don samar wa kanmu wasu abubuwan da nake gaya maka a yanzu?
TAMBAYA: Wane abu ne kungiyoyin suka yi wa kansu wanda ba su yi maku ba?
AMINU: Akwai. Idan wani abu ya sami 'yar wasa ko dan wasa, babu wani abu da Council of Artists ke yi. Idan wani abu ya sami dan wasa babu inda zai kai kukansa a share masa ido. Don haka muka ga ta yaya za mu iya kasancewa cikin zama irin haka?
TAMBAYA: Can baya an sha yin yunkurin kafa kungiyoyi amma sai a samu wasu sun shige su don su bata al'amarin. To ku yanzu ba ku guji haka ba?
AMINU: Can baya an taba yunkurin kafa wata mai suna KASAKA wadda ni memba ne ma a cikinta. Daga baya muka samu 'yan matsaloli wadanda suka sa kungiyar ba ta yi wani tasiri ba, saboda wata fassara da aka yi mata.
TAMBAYA: Kuna da niyyar canza sunan kungiyar maganin yi maku wani kallo na 'yan neman tayar da zaune tsaye?
AMINU: Ba mu da wata manufa ta ci wa wani mutunci ko suka ga wata kungiya, a'a. Mu dai 'Kandahar' kungiya ce mai neman zaman lafiya da ci-gabanmu.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin