Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 33   Satumba 2002
MALAM ZURKE


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
HIRAR MUSAMMAN
Wasiku
KU TAMBAYE SU
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
RA'AYIN MUJALLAR FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon Fim ta 31
Bangon Fim ta 30
Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Riba biyu bikin Abida: Ga amarya ga kudin kalanda!

MASU cewa an wulakanta su a wurin bikin auren jaruma Abida Mohammed, ba su san me ake kira wulakanci ba ma. Su je su tambayi Alh. Auwalu Mutunchi Mai Kalanda su sha labari. Idan ba su gan shi a rumfarsa da ke kasuwar Sabon Garin Kano ba, to su garzaya babbar kasuwar Kaduna, gefen titin 'Ahmadu Bello Way,' su tambayi Alhaji Musa Yaro Mai Kalanda, shi ma su ji yadda ya dandana kudarsa a hannun Hamza Mohammed Danzaki, wato angon Abida, da abokansa.

Su dai su Auwalu da Musa, suna cin abincinsu ne ta hanyar buga kalanda irin wadda talakawa ke saye suna likawa a bangon dakinsu. Babu irin kalandun da ba su buga ba a rayuwarsu - tun daga na shugabannin kasa da na 'yan dambe har zuwa na jaruman finafinan Indiya. Shi Auwalu ma, ya kwashe shekara 15 yana wannan sana'ar. A cewarsa, bai taba samun matsala da wani ba sai da ya shiga buga kalandar 'yan fim. To fa! Wa ya gaya masa lahira ana danwake? Matsalar farko da ya samu ita ce lokacin da ya buga kalandar auren Fati Mohammed, ya cika kasa da ita. A sakamakon haka ne angon Fati din, wato Sani Musa Mai Iska, ya sa aka sakaya shi a caji ofis har tsawon kwana biyu, sa'annan kuma aka tilasta masa ya biya wasu kudi. Ga mari ga tsinka jaka kenan.

To, ashe da sauki aka yi masa a bara. A bana, kalandar bikin Abida na fitowa sai zaratan katti abokan Hamza suka dira shagon Auwalu, suna ta kumfar baki kan dalilin da ya sa ya buga kalandar ba tare da izini ba. "Su anguna sun zo sun tambaye ni wanda ya ba ni hotuna, kuma suka ce za su dawo gobe," inji shi lokacin da yake yi wa wani wakilina bayanin al'amarin maras dadin ji. "Da suka dawo washegari sai na ce masu me suke ganin za a yi?"

Auwalu ya dauka karamar magana ce. Angunan suka karbe kalanda da kuma kwanonin dab'i da aka buga ta da su, suka tafi. Ashe barikin sojoji suka zarce. Kun san shi Hamza ai yana da sojoji da suke yi masa aiki; kun tuna da kashin da 'yan biki suka sha a otal din Ni'ima lokacin walima? Ai fa Auwalu yana zaune sai ya ga askarawan Nijeriya sun dira a shagonsa kai ka ce yaki ne ya barke a kasuwar. Tare da su akwai anguna. "Sun zo a kan cewar ya aka yi muka buga wannan kalandar?" inji Auwalu a labarinsa. "Sojojin sun zo a mota. Suka tafi da ni wajen kwamanda muka yi bayani." A nan ne ya ce suka bukaci ya biya su kudi. "Na biya su naira dubu hamsin. Ka ga kowa kenan da irin nasa wulakancin."

Dubu hamsin? Malamai, kada ku yi mamakin yawan wannan tarar wadda ba a kotu aka yi ta ba. Ai sa'a ma ya yi da ba a taba lafiyar jikinsa ba, aka tsaya ga lafiyar aljihunsa kawai.

Auwalu ya yi mamakin wannan danyen hukuncin da aka yanke a kansa. Ya ce ai ko Ibro, da kansa yake zuwa a dauke shi hoto, kuma bai taba cewa a biya shi ko kwabo ba. Ya ce haka su ma irin su Mandawari, Tahir Fagge, da Iyan-Tama. "Amma ban taba ganin wulakanci ba sai a bikin Abida da Fati," inji shi.

Duk da wannan abu da ya faru gare shi, Auwalu bai ci riba ba. Ya ce kalandar bikin Abida din ma ba ta yi farin jini ba. Kuma abin mamaki, ya ce duk da abin da aka yi masa babu komai tunda a ganinsa shi da 'yan fim sun zama daya. Sai dai kuma ya nuna cewa ture ne aka yi masa kuma munafinci ne. "Ai da, wasu mutane uku ne suka fara zuwa, daga baya kuma aka dawo da Hamza mijin Abida."

Auwalu dai ya koyi wani darasi daya daga wannan badakalar: daga yau idan wani abu na dan wasa ya tashi zai same shi ya ce zai buga kalandarsa. "Idan ya yarda shikenan, idan bai yarda ba kuma in watsar da shi."

A nasa bangaren, shi ma Musa Mai Kalanda sai da ya amayar da kudin kalandar bikin su Hamza da ya buga. Amma ga alama shi tsorata kurum ya yi. Domin kuwa lokacin da ya ji wai an sa sojoji sun cafke Auwalu a Kano, sai ya rarumi kudi ya garzaya Kano da kansa, ya kai wa Hamza N50,000. Dalili shi ne shi ma Musa, wanda kwanan nan ya gama daukar fim dinsa na Ibro Soja, ya buga kalandar bikin na Abida. Ko ya ci riba? Oho!

Wanda dai muke da tabbacin ya ci riba daga wannan bahallatsa shi ne Hamza Mohammed Danzaki, sai kuma kila abin da ya tsintsinka wa abokan ango. Domin in ka tara N50,000 da N50,000, ka ga ya samu N100,000 kenan. In ni ne ai ina jin ko a nan na maida kudin lefena, ko?

Tunda ko abin ya zama haka, ni ma Malam Zurke ina nan ina nazarin yiwuwar aurenmu da wata fitacciyar jarumar fim. Kuma idan an tashi bikin, ba zan ce wa 'yan kalanda komai ba. Zan bude masu kofar zauren walimar auren namu, su shigo su daddauki dukkan hotunan da suke so. Zan bari in ga wanda zai yi gigin bugo kalandar bikin. Da ta fito zan ruga Barikin Bukavu na Kano, in kwaso sojoji mu yi awon gaba da shi, mu kai shi gadirun mu jefar da shi. Bayan ya kwana biyu ya nuna, sai a zauna a yi magana. Ba zan kyale shi ba sai ya amayo akalla N150,000. A ciki, na san zan sallami su Oga, da kuma abokaina. Ka ga abin da ya rage ai ya ishe ni in kara jari in buga kwalin fim din da muka yi da jarumar kafin mu yi aure, in fito da shi kasuwa. Kai, ko ban yi haka ba dai na san zan maida kudin da na kashe na yi mata lefe. Kuma ba 'yan kalanda ba ma, hatta 'yan mujalla sai na latsa su. Riba biyu kenan: ga shahararriyar amarya na aure, ga kuma kudin hotuna! Ka ga ai auren ya zama gobarar Titi kenan. Shin in ko haka ne me zai hana mutum ya rika auren 'yan fim mata? Shi ma ai wata hanya ce ta cin riba. Gane mani hanya Malam, wai makaho ya so tsegumi!

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin