Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 34   Oktoba 2002
Malam Zurke
MALAM ZURKE


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
HIRAR MUSAMMAN
Wasiku
KU TAMBAYE SU
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
RA'AYIN MUJALLAR FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka
Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Mandawari da Biba: An shirya kenan?

A YAU na yi wawan kamu. A da, kukan ji labaran 'yan ku-ci-ku-ba-mun 'yan fim ne a wannan fili nawa, wato irin su O'o. To, yau komar tawa wasu tika-tikan kifaye ta kamo. Ta taba kama su a can baya, amma na san yanzu kun manta da zakin romon farfesunsu da kuka sha. Su waye wadannan? MAN-dawarii da BI-baa!!

Ba sai na nanata ba, duk wani dan fim da ya kwana kuma ya tashi a Kano ya san cewa babu kyakkyawar fahimta tsakanin Bibalo - Hauwa Ali Dodo da babab soyayya na Hajiya Hadiza ba-mamaki, wato Ibrahim Mohammed Mandawari.

Idan kai ba ka sani ba don kana nesa, bari ka ji. An ce dadadden sabanin nasu ya faro ne lokacin da shugaban kamfanin talbijin din bidiyo na 'Mu Shakata,' Alhaji Mandawari, ya raba takardar gayyata ga wasu taurarin Kano su 13 da suka hada da biba. An gayyace su ne don yin wata waka da ta fito cikin shirin Mu Shakata na 3 mai shigen wakar "We Are the World" ta shahaharrun mawakan Amerika. Duk sauran suka halarta, in ban da Biba. Ina jin a lokacin ita biba ba ta san cewa a al'adar industri idan mandawari ya gitta kara ba a ketarawa ba; ita ko sai ga shi ta tsallaka. Ko me ta taka? Oho!

Tun daga lokacin sai jaruman biyu kowa ya kama gabansa. Ko a fim aka hada su, to dayan ba zai yi ba, sai fa idan an tsara fim din yadda har a gama su biyu din ba za su hadu ba. Hakan ya faru a wurare da dama, har ma a garuruwa irin Zariya inda suka fito (ko a shirin Asali ne?) da kuma Kaduna inda suka fito a Adali. An shafe shekara ana wannan zaman doya da manjan.

To, da yake in dai kere na yawo zabo na yawo wata rana sai an gamu, kwanan nan sai kamfanin Oga, wato 'Mandawari Enterprises,' ya samu kwangilar shirya wani fim mai suna Hannun Dama daga hannun Hajiya Laila Dogonyaro, tsohuwar 'yar siyasar nan mai zama a Kaduna. ban tsammanin ita Hajiya ta san siyasar industiri inda idan ba ka shiri da wane to ba za ka sa shi a fim dinka ba ko ka bar shi ya fito a wani fim da kake da hannu a cikinsa. Don haka sai ta rubuto jerin sunayen 'yan wasan da take so su fito a fim din, ta bai wa Mandawari. Cikinsu kuwa akwai Biba. To fa! Tunda babu halin yi wa 'yar wasan murdiya, sai Mandawari ya hakura a yi fim din da ita; da ma Hausawa sun ce a cikin ido ake tsawurya. Babbar asarkalar da ke cikin al'amarin kuwa ita ce shi Mandawari din ne zai fito a matsayin mijinta. Wai!

Fim din na siyasa ne, ana so a nuno musamman yadda mata ke taka rawa a cikin harkokin siyasar kasar nan. Akwai fitattun 'yan fim har 27 a cikinsa (ban da mazan da ke ciki).

Shirin fim din ya tafi lafiya ba tangarda. Ashe rincimi yana gaba.

To rannan a karshen watan Agusta sai aka kwashi 'yan wasa. Aka kwaso mata daga Hukumar Al'adu da Tarihi wadanda Biba, a matsayin 'yar takara a fim din, za ta hure wa kunne su zabe ta. Aka taru a Dandalin Matasa na Fagge (Fagge Youth Centre). Taro ya yi taro amma wani dalili ya hana a fara daukar fim. Ke Biba sai kai-da-kawo kike kina zanzana don ki hau duro ki yi kamfen ki watsa wa talakawan da za ki ja hankalinsu da kudi. Ga alama tana son role din.

Da jarumar ta ga rana ta kusan komawa ga Ubangijinta, sai ta fara yi wa Mandawari, wanda shi ne darakta, korafin cewa ita fa tana da baki, don Allah a sallame ta da wuri ta kama gabanta. Hakan bai sa an bi uzurinta ba. Ita wacece da za ta ba Oga sukutum oda? Ko don ana kiranta Superstar?

Can da Biba ta yi fushi sai ta dan bar wurin, kuma ta turo wata yarinya don ta daukar mata jakarta, ita kuma ta matsa can gefe tana jira.

Da fitaccen jarumi Kabiru Nakwango ya fahimci lallai akwai bacin rai a tare da Biba, sai ya rike jakar ya nemi ya maida abin wasa don kada shi ma Mandawari ya yi fushi abin ya dagule. Ita ko Biba da ta ga 'yar aike ba ta dawo ba, sai ta je wurin ta rika zunduma mata zagi, ta fizgi jakarta ta fice.

A lokacin Mandawari ya shirya. Da ma a ranar ita Biba ce za ta yi kamfen, to kuma ga shi ta fice. Aka yi cirko-cirko. Wannan fa shi ake cewa mutum dubu jiran mutum daya. Mandawari ya kule. Shi ko an ce in ya yi fushi bai da kyau!

Mai karatu, kada ka dauka ba mutane sosai a wurin. Wannan badakalar a bainar jama'a aka yi ta, ba mutane biyu ko uku ba, ai sun kai dari daya, in ma ba su fi ba, ciki kuwa har da wani almajirina mai dauko mani labari.

Can bayan kamar minti 20 ko 30 kuma sai ga Biba ta dawo, wai ita ta je ta gama wata harka ta ne. Da ma harzuka wurin Mandawari ba a cewa komai, ta kai masa iya wuya. Sai kawai aka ga ya tattakura, ya hakikice, ya daga yatsa ya nuna Biba, ya yi kwance-kwance ya yi ta antaya mata zagi iri daban-daban - da mai dadin ji da wanda idan mutum ya ji zai toshe kunne don kada ya kara jin irinsa.

Jama'a suka taru suna ba shi hakuri, wani na cewa, "Kada a yi abin kunya dai. Ga shi ana kallonmu!" Ita kuwa Superstar ta yi tsaye sototo. Can sai kuma aka ga ya yi kukan kura ya nufo ta don ya yi mata kwaf-daya. Cacirindon jama'a kuwa suka rike shi, suna ba shi hakuri: "Oga, ai ba girmanka ba ne." Wasu kuwa sai suka bai wa Biba shawara cewa ta bar wurin har sai kura ta lafa, suka tare mata dan acaba, ta hau babur za a gudu da ita.

Kafin mutane su ankara kuwa har zuciya ta kara dibar gogan naka. Ya auka motarsa ya sa dan makulli ya bude ta, motar ta yi wani irin ruri. Da ya kwarari motar, 'yan wasa da yake ba mai son ya ga badi da kafar katako, sai kowa ya yi ta kansa, ya kauce.

To da Mandawari ya bi su Biba da dan acabar ai sai sararaf suka auka kan 'Kano-ba-doka' (wato tsakiyar titi). Nan fa aka taru aka rika hada shi da Allah da Allaro - inji Fulani. Da kyar ya hakura ya fasa kashe ta.

Washegari kuma da ma Abuja za a tafi don a gama da daukar fim din. A cewar wata kwakkwarar majiya ta kusa da Biba, ke Biba da kika tsira, sai kika buga wa Hajiya Laila waya don ta san abin da Kano fa ke ciki. An ce Hajiya ta ba ta shawara cewa ta riga kowa isa Abuja don a ba ta masauki daban. A babban birnin tarayyar, haka aka fara wannan fim kowa na kule da juna, duk da yake wai ita Garkuwa ta zaunar da su ta yi masu huduba. Su dai sauran 'yan wasa ba su san dalili ba, wane tudu wane gangare, sai suka ji ana cewa ai Biba da Mandawari sun shirya, wai har ma... Da wasu mata ma suke kara yi wa Biba barka da arziki, sai ta ce ai abin ya wuce, wai ya kira ta ne ya ba ta hakuri.

Wata ''yar wasa da aka yi abin kan idonta ta ce mani, "Ni dai shawarata ga 'yan fim a nan ita ce, duk wadanda kuka ga suna gaba, ku daina goyon bayan wani bangaren ko da kuwa naka ne. Ku tuna duk da an ce naka shi ne naka, to wata rana nakan shi zai bada kai."

Wani dan wasan kuma cewa ya yi, "Ni Mandawari ya burge ni. Hauwa tana da wata dabi'a: sau da yawa da an je ziyara wurinta lokeshin sai ta rika azazzalar darakta wai ya yi sauri ya sallame ta. Ka tambayi kowa a industiri, zai gaya maka haka ne. Kuma ai wannan ba daidai ba ne."

Kwarai, ba daidai ba ne. Amma ba Biba kadai ke da wannan halayyar ba, kusan duk ''yar wasan da ta kai matsayin superstar, wato fitacciya, haka za ka ga tana yi wa mutane - ba kuma matan ba har mazan. Na tuna a 'yan shekarun baya sai da furodusa B.K. Dandago ya damka Maijidda Abdulkadir ga hannun 'yansanda saboda sakaci da yarjejeniyar da suka kulla lokacin da za ta yi masa fim. Shi ma darakta Bala Ahmed ya taba cinna wa Fati Mohammed dan sanda saboda irin wannan sakacin. Don kuwa su Abida, ba a cewa komai.

Shi kuma mandawari, na ji 'yan fim da dama suna bayyana nadama a kan halayyar da ya nuna wa Biba, suna cewa a matsayinsa na Shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kano, bai dace ya nuna aniyar kashe wani dan wasa ba saboda zuciya a kan kowane dalili ne. Ai akwai hanyoyi da dama da mutum zai iya bayyana bacin rai, ba sai ya bi ta hanyar 'yan daba ba. Wani matashin dan wasa cewa ya yi, "In da mu ne muka yi abin da ya yi sai ka ji an kira mu mitin ana wani menene... Ga shi kuwa su shugabanni suna girma suna cin kasa."

A yanzu dai ba a san makomar "shiryawar" Biba da Mandawarin ba. Abin zai dore kuwa? Ko kuwa tunda kwangilar Hannun Dama ta kare za su koma hannun hagu ne su ci gaba da zaman doya da manja? Mu dai ba haka muke so ba. Bari in samu wani fim in kira su in ga idan za su yarda su fito tare a matsayin jaruman shirin.

Arangamar Ciroki da 'yan damfara

ASHE ba banza ba Hausawa ke yin karin maganar nan, gaba da gabanta, wai aljani ya taka wuta; haka kuma maso abinka ya fi ka dabara. In da za a ce za a iya yi wa wayayye kuma fitaccen dan wasa kamar Bashir Bala (Ciroki) dabara ta hanya mafi sauki har a damfare shi, wasu za su yi mamaki ko ma su musanta hakan zai iya faruwa. To an yi. Domin shi Ciroki yana ji yana gani kiri-kiri 'yan damfara ko fowannayin (419) suka raba shi da babur dinsa kirar Vespa cikin 'yan mintoci kalilan a birnin Kano. Na san mai karatu zai kagara ya ji yadda aka yi wannan al'amari mai ban takaici da mamaki ya faru. To gyara zama ka sha labari.

Makonni kalilan gabanin ranar Babbar Sallah ta bara ne wasu dillalan motoci suka kawo wa Ciroki tallar wata kankareriyar motar shiga, wadda aka fi sani da 'yar Kwatano, suka tambaye shi ko yana da sha'awar zai saya? Suka ce motar ta wata mace ce da take son saidawa, kuma ta yi sallaminta kan kudi N160,000 kacal. Shi kuma gogan naka sai wannan mota ta ba shi sha'awa, ga shi kuma yana ganin farashinta a bagas ne. Don haka sai ya ce zai biya motar in dai ba a samu wani da ya riga shi ba cikin kwanaki kalilan masu zawa. Aka rabu a kan haka.

Abin da ya sa Ciroki ya yanke wannan hukuncin shi ne a lokacin yana da N100,000 da ya tara. Saboda haka maimakon ya je neman bashi sai ya sanya babur Besfarsa a kasuwa; saboda giredi ce kuma ta mori bodi ya yi mata kudi N70,000. Saboda ba kwashi-kwaraf ba ce sai ya ki ya bai wa dillalai; tana hannunsa, duk mai so ya same shi a gida ko kuma a duk inda suka hadu domin a yi ciniki a biya. Bisa wannan sharadin da ya gindaya wasu sun sha taya Besfar tun daga kan N45,000 zuwa N55,000 amma ya ki sallamawa, ya ce sai N70,000. Ashe asara ce ke tafe!

A ranar Jajibirin ranar Sallah, sai ga wani matashi tare da wani karamin yaro sun sallama masa a gida. Ya fito.

Da fitowarsa sai shi babban ya dubi karamin ya yi masa tsawa ya ce, "Me ya sa ba ka da kunya? A zo wajen manya ba za ka gaishe su ba!"

Bayan Malam Ciroki da mutumin sun yi musabaha, sai yaro ya tsuguna ya gaida shi cikin girmamawa.

Daga nan sai shi babban ya dubi Ciroki ya ce, "Babana ne ya aiko ni wajenka saboda an ce za ka sayar da Besfarka; shi ne ake son a saya wa kanena domin ya rika zuwa makaranta."

"Kwarai, zan sayar," inji Ciroki. Duk dadi ya kama shi. Ya shiga cikin ya fito da ita domin a yi ciniki.

Yaro dai ya yi kasake yana kallonsu. Cikin kama-kama daga N55,000 har aka kai ga N70,000, sannan Ciroki ya sallamar. Abu kamar a mafarki, sai matashin ya ce, "To tunda an daidaidata bari in dana ta in tabbatar da lafiyarta."

Kamar asiri, ba tare da wani bata lokaci ba, Ciroki ya kawo dan ki ya ba shi. Shi kuma ya hau ya tafi ya bar Ciroki a kofar gida tsaye tare da yaron nan.

Tun Ciroki yana duba hanyar dawowar wannan mutum, har ya soma duban agogon da ke hannunsa. Abu kamar a fim, ya ga an tasar wa minti 10 ba amo ba labari. Sai ya fara tambayar kansa cikin zuciyarsa, "Wai ya aka yi ne ma na ba da danin Besfar nan wacce tun bara da na saye ta babu wanda ya taba hawanta sai in na je Wudil?"

Da aka samu kimanin minti 15 ba a ko keyar mutumin ba, sai Ciroki ya dubi yaro ya ce, "Kai wai ina yayan naka ya tafi ne?"

Da bude bakin yaro sai ya ce, "Ni fa ba yayana ba ne."

Ciroki ya hassala, ya harare shi ya ce, "Karya kake yi!"

A takaice dai bayan jama'a ta taru Ciroki ya tasa yaro har gidan Malamin nasa inda suka tabbatar da cewa shakka babu almajirin wannan gidan ne. Ciroki ya shaida wa Malam cewar shi fa ba zai bar yaron ba don an hada baki da shi an damfare shi.

Suna barin gidan Malam, Ciroki bai zame ko'ina da yaron ba sai ofishin 'yansanda. Su kuma folis suka yi ta tursasa yaro ko za a samu wani bayani daga gare shi. Duk azabtarwar da suka yi masa, a banza. Ya kafe a kan cewa sun hadu ne kawai a titi ya kawo N20 ya ba shi tare da wasu 'yan kwarannin ayaba da lemu a cikin leda. Ya nuna wadannan kudin da ayabar da lemun aka tabbatar. Amma duk da haka 'yansanda suka ci gaba da tsare shi wai sai an kara bincike.

Bayan kwana uku yaron yana tsare kuma ba a samu wani labari na Besfa ba, sai iyayen yaron tare da malaminsa suka je har gida suka samu Ciroki suka ba shi hakuri tare da tabbatar masa da cewar su ba su da kudin da za su iya biyansa mashin din nasa. Don haka shi kuma da yake zuciyar Musulunci gare shi sai ya tausaya masu ya ce ya bar maganar - ya nemi sakayyar Allah.

Aka je aka sako yaro.

Da yake bayyana mani labarin kwanan nan, Ciroki ya ce ba abin da ya fi ba shi haushi da takaici kamar bayan mai kasancewa ta kasance har ya bar wa Allah sai kuma ga wasu malamai 'yan tsibbu suna biyo shi har gida suna neman wasu kudi a hannunsa da nufin wai cikin mako guda za a dawo masa da Besfarsa har gida. Su kuma 'yansanda suka rika samunsa suna neman izininsa da nufin ya fada masu sunayen dukkan dillalan da suka tallata masa mota da kuma wadanda ya tallata masu mashin dinsa, wai za su san yadda za a yi a sama masa kudinsa. Ka ji 'yan duniya!

Shi kuwa Na-A'isha-ba-mamaki tunda ya bar wa Mai kowa Mai komai al'amarin, kuma ya fahimci akwai wani nau'i na wata sabuwar damfarar da ake son a yi masa ta wata hanyar sai duk ya share su.

Mota dai har yanzu ba ta samu ga Ciroki ba. Amma bayan wani lokacin sai ya sake sayen wata Besfar "'yar ubansu" wacce yake amfani da ita har yanzu. Addu'ata ga Ciroki ita ce kada Allah ya maimaita abin da ya faru ga ita waccan Besfar tasa. ----------------------------------

Ina masu karatun da suke cewa suna son su ga hoton Malam Zurke? Ga ni can a saman shafi na 46 daga dama. To yaya, na yi kyau?

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin