BAYAN haka, ina sanar da kai cewa Rukayya Umar Santa tana daga cikin 'yan wasa mata wadanda suka kwanta mani a rai. A yadda nake son wasannin wannan lafiyayyar yarinyar, in ba domin na fara tsufa ba (ka san an ce yarinya sai yaro!), kuma in ba domin Misbahu M. Ahmad ya riga ni ba, to da sai in ce ni ma wannan yayin aure-auren da ake yi na gabatowar watan azumi da bayan Sallah ba za a bar ni a baya ba wajen yin amarya mai fasali. Shi ya sa idan na ji an ce abu kaza mara dadi ya faru ga Rukayya, nakan ji zafi; haka kuma idan abin farin ciki ya same ta, nakan taya ta murna.
To, kwanan nan Rukayya tare da wasu 'yan wasan Kano sun je Yola cikin Jihar Adamawa domin yin wasan kalankuwa na 'yan fim, wanda suke kira 'gala.' Ni dai ba mai son gala ba ne, domin a ganina gala na zubar wa dan wasa da mutunci. Dalilina na fadar haka shi ne yawan ganin 'yan fim da 'yan kallon finafinan bidiyo ke yi yana rage wa su jaruman kwarjini. Tun ana yin gala mai armashi inda ake marmarin ganin 'yan wasa, yanzu kowane birni da kauye ma sai ka ji wai an shirya bikin gala. A cikin wata daya kacal da ya gabata, an yi gala a Abuja, Yola, Misau, Maiduguri, Legas, Zariya da sauransu. Kai, ni ina ma ganin cewa yawan yin gala ya taimaka wajen lafawar kasuwar finafinai, domin kuwa duk mai sayen fim idan yana ganin 'yan wasan a kullum sai ka ga ya raina su. Ka san an ce ido wa ka raina? ya ce wanda nake gani kullum. Babu ma kamar da yake akan tafka abin kunya a wurin gala.
To, kila Rukayyarmu ba ta fahimci haka ba, shi ya sa da aka gayyace ta Adamawa, suka rankaya tare da sauran abokan sana'arta, cikinsu har da Malam Misbahu wanda kwanan nan zai zama angonta.
Idan ka tuna, ana cikin yin gala sai aka kira Rukayya don ta hau dandamali ta taka rawa da waka. Ta nemi wanda za ta ba ajiyar jakarta, ta rasa. To, sai ta ga ai su Zahara'u Shata ma duk sun ajiye jakunkunansu. Don haka ta aje tata inda suka aje, ta hau ta cashe.
To, abinka da ku Da'u fataken dare (koda yake yanzu har da rana ma fataucin kuke yi) sai ka lababo babu wanda ya lura, ka zage zif din jakar Rukayya, ka dauke mata tarho na GSM. Da ta dawo daga kan dandamalin, ba a jima ba ta ga babu handset ko sama ko kasa. Ka dauke shi!
Ban sani ba ko Rukayya ta yi kuka ko da a boye ne, amma na san ta yi babban bakin ciki. Ita ba tsadar kurtun tarhon (handset) ke damunta ba kamar dan faifan maganidisun da ke cikinsa wanda ke kunshe da lambobin tarhon abokan arziki da takan yi wa waya (mai suna SIM card); kai, hatta lambar mahaifiyarta da ke Saudiyya tana ciki. Kai, har ma lambar Misbahu na ciki!
To, babu yadda za ta yi. Haka nan ta hakura suka dawo Kano ana ta jajanta mata. Mu kuma a nan Kano mun yi ta buga mata waya ba mu samunta (ka san a Adamawa babu GSM tukuna!). Wayyo, ashe ka sace wayar, kuma da yake wayar ba ta aiki a can, shi ya sa ba mu ji ta kada ba ballantana wani ya dauka. Sai da jarumar ta dawo ne sa'annan muka ji labarin abin da ya faru.
To, da ta dawo sai ta samu waya ta buga lambar tata da ke cikin wayar da ka dauke. Lambar ita ce: 08037042510. Abin mamaki, sai ta ji an dauka an ce, "Hello!" Idan ka tuna, ga yadda kuka tattauna da ita Rukayya Dawayya:
Rukayya: Hello, don Allah ina so in yi magana da mai wannan wayar.
Barawo: Kina nufin Rukayya Dawayya? Ai ba ta nan.
Rukayya: Malam, gaskiya ni ce ke da wannan wayar da ke wurinka. Ni ce Rukayya.
Barawo: Af, Rukayya ce? Wallahi ai ban gane ki ba. To, yaya garin? Kina lafiya?
Rukayya: Lafiya kalau. Ina so don Allah don Annabi ka taimake ni ka dawo mani da wayata.
Barawo: Haba Rukayya! Ni ma fa saye na yi. Ya zan yi asara?
Rukayya: To, idan ba za ka dawo mani da ita ba, ka taimake ni ka aiko mani da SIM card din. Ka dai san cewa bai ma kai kudin handset dina ba. Wallahi ni lambobin da ke cikin wayar nake so.
Barawo: To ya za ai in dawo maki da shi?
Rukayya: Bari in yi maka kwatance layinmu. Ka zo unguwar..., ko da dan acaba ka samu ka zo, idan ka zo layin..., ka cire SIM card din kawai ka saka a cikin wani abu ka ba duk yaron da ka gani ka ce ya kai gidan su Rukayya Dawayya. Za a kawo min har gida.
Barawo (ya yi dariya): Haba, ke ma ba'a kike. Gaskiya ba zan iya yin haka ba. Ni yanzu ma daga Abuja nake, gobe zan iso Kano.
Rukayya: Amma malam, ka tuna fa akwai lahira akwai hisabi.
Barawo: Ahaf! Ni ina ruwana?
Rukayya: To shikenan. Wallahi zan sa MTN su toshe layin wayar.
Barawo: To sai me? Ni kaina cire SIM card din zan yi in jefar, tunda bai da wani amfani a gare ni, kuma ga shi mutane sun dame ni da bugo waya da aiko da text message wai suna son su yi magana da ke.
Rukayya: To, shikenan. Ni dai kawai Allah-ya-isa zan yi maka; sai Allah ya saka mani!
Barawo (ya fashe da dariya, ya kashe wayar ba tare da ba ta amsa ba).
Kai barawo, na ji Rukayya tana ta ce maka 'Malam.' To a gaskiya kai ba malami ba ne, domin duk malami wanda ya san addini, to ya kuwa san hukuncin sata. Kuma ka daina burgar Rukayya da wani abu wai kana Abuja. Mu muna jin ba shakka a Kano kake. Kuma muna jin ka san Rukayya kwarai da gaske, kila ma ita ma ta san ka. Kuma muna jin kai ma ka je galar nan ta Adamawa. Wa ma ya sani ko kana cikin 'yan wasa ko kuma dan wasan ne ya saci wayar ya sayar maka? Shin wace karuwa kake jin za ka samu da ka sayi kayan sata? Wallahi ka gaggauta tuba, musamman tunda ga watan azumi (watan tuba!) ya zo. Ka mayar da kaya ga mai su!
Ke ko Dawayya, kar ki damu. In dai GSM ne ai za ki yi wani ba tare da dadewa ba. Kada ki manta, lokacin da yayinsa ya shigo kina daga cikin 'yan fim da suka fara sayensa. Ko kin manta da tsokacin da na yi mai taken "Ayyuririi 'yan fim sun yi selula"?
A karshe, na ji an ce kun bata da wani mai kaunarki, wato Aminu Mai Dawayya wanda tun da ya shigo harkar fim da sunanki ake masa lakabi. Don Allah ku shirya, domin za mu so a ce ya yi waka a bikinki kamar yadda yakan yi a bukukuwan wasu 'yan fim din. Kul kika bari Sadi Sidi Sharifai ya kwace shi; don ga shi har an nada shi Garkuwan Sadi Sidi Sharifai kwanan nan a ran bikin Sadi din.
Sauran ke da Misbahu ku nada shi Wazirin Rukayya Dawayya.
Ina masu karatun da suke cewa suna son su ga hoton Malam Zurke? Ga ni can a saman shafi na 46 daga dama. To yaya, na yi kyau?