Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 39   Maris 2003
Malam Zurke
MALAM ZURKE


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
FADI SONKA
Wasiku
NEMAN MAFITA
DUNIYAR FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
FADI SONKAr sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da tunanin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: Wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, ta da jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Wai ladi mutu-ka-raba 'yar bori ce?

"WAI iskokai gare su ko kuwa 'yan iska ne kawai." Abin da ya bai wa mai daukar hoto Nasiru Dorayi (DOP) mamaki har ya fadi wannan kalma shi ne yadda wasu mata 'yan fm suka rika hawan bori da nufin bugun aljanu a garin Dawakin Tofa cikin talatainin dare lokacin da aka je daukar shirin wani fim mai suna Ga Koshi a can. Irin wannan abu yanzu ya zama ruwan dare a cikin industiri a Kano.

Sau da yawa a wuraren daukar fim za ka ji kuma ka ga budurwa ko mace da yawa cikin dare suna bori suna fizge-fizge da kakabi, suna kiranye irin na surkulle. Wani mai daukar hoto da ya ce ya sha ganin irin wannan abin mamaki ya bayyana mani cewa shi a 'NNDC Quarters' ya fara ganin wannan al'amarin; lokacin an je daukar wani shiri ne mai mai suna Jalala, cikin Disamba 2002. A wurin, cikin dare sai 'yanmata hudu suka hau bori. Hankalin darakta Murtala Madaki da sauran ma'aikatansa ya tashi sosai. Daga bisani an yi sa'a wani dan wasa da ake ce wa Soja ya rika yi masu karatu da adduo'i . 'Soja' ya shaida wa jama'a cewa daga cikin 'yanmatan hudu daya ce kawai ke da aljanin gaskiya. Sauran, a cewarsa, karya suke yi. Lokacin da yake yin addu'o'i da karatu, an ce aljanar da ta hau kan 'yar wasan ta roki a daina karatun. Da aka tambaye ta dalilin hawa kan 'yar wasan sai ta ce bata mata rai aka yi, kuma ita ba Musulma ba ce. Wannan kalamin dai duk ita yarinyar da ta hau borin ake jin tana fadarsa.

A garin Makarfi kuwa, can ma 'yan wasa sun je don yin shirin fim mai suna Kash Kaico. Da safe har kowa ya yi wanka za a fara daukar fim din wai sai wata 'yar wasa mai suna Jummai da kuma fitacciyar jaruma Ladi Mohammed (Mutu-Ka-Raba) suka hau nasu borin. Wani wanda aka yi abin a gabansa ya gaya mani cewa dalilin hawansu shi ne wai wani ne ya shiga wurin sanye da turare mai karfi.

Ko lokacin da ake daukar shrin fim din Qauli na kamfanin 'Fatima Production', wanda darakta Tijjani Ibraheem ya bada umurni, irin haka ta faru. A unguwar Kwanar-Ungogo a Kano abin ya faru. Wadanda abin ya faru a kan idonsu sun tabbatar da cewa wani al'amari ya faru da Ladi Mutu-Ka-Raba. A can ba bori ta hau ba. Ana cikin daukar wani sin ne inda darakta Tijjani ya ce ta fadi "Police da Judiciary" amma wai an kusan kwashe awa daya cur Ladi na kokarin fadin wadannan kalmomin, amma ta kasa. An ce duk lokacin da ta buda baki za ta fada, sai abin ya gagara har dai abin ya kai ta ga hada gumi sharkaf.

An yi kokarin a sauya Ladi daga rol din na matsayinta na babbar alkali (chief judge), amma furodusan fim din, Baba Shariff, ya ce ba zai sauya ta da kowa ba.

Shin da gaske Mutu-Ka-Raba 'yar bori ce? Ko kafin mu tafi nemanta an gaya mana cewa ko an je ma ba za ta ce e, ita din ba ce. Don haka ba mu yi mamakin jin amsarta ba; amma kila kuma ba ta da ljannun. Ladi dai ta ce karya da sharri ne kawai ake yi mata.

TAMBAYA: Ana surutu cewa wasu 'yan fim na da iska har sukan hau bori a lokeshin. An ce kina daga cikinsu. Shin ya gaskiyar abin take?

LADI: Ba na cikinsu. Sharrin mutane ne.

TAMBAYA: Da ake cewa kin hau bira'izai a garin Makarfi fa?

LADI: Can ma mun yi fim mun gama lafiya.

TAMBAYA: An kuma ce a wurin daukar fim din Qauli a Kwanar Ungogo wai 'mutanen' naki sun hana ki cewa "police da Judiciary". Ya abin yake?

LADI: Ni ban sani ba. In ma sun hana ni to ai za a kalli fim din. Karya ne.

TAMBAYA: To me za ki ce kan masu yi maki surutun cewa kina da iska?

LADI: Abin da zan ce shi ne mutane su tuna fa aljani ba abin wasan mutane ba ne. Kuma in ina da su, ina roko Allah ya yaye min tunda ba saya na yi da kudina ba. Kuma duk mai su Allah ya yaye masa. Kuma ba sa cutar da ni in ma ina da su. Kuma duk dan' adam yana neman hirji gare su.

TAMBAYA: Da ma idan kina da su ana so a ji ya aka yi kika sami abin. Shin Musulmi ne ko arna? Kuma an taba kokarin cire maki su ta hanyar rukiyya ko girka? Sai kuma ana so a ji sharaddUn da suka gindaya maki.

LADI: (Bayan ta yi dariya kan irin mamakin da ta yi da tambayoyin): Wai shi (wanda) da ya rubuto maka wadannan tambayoyi, ina ya kwakulo labarin da tambayoyin? To ni ban tabbatar ina da su ba ko ba ni da su ballantana in ce an taba yi min wasu abubuwa a kai. Amma ina so ka fada masa idan zai iya bugawa to ga sharuddun da suka kafa min... Sharadin da suka kafa min in ka ji shi… shi ne wai sai na aure ka. Kuma daga yanzu ka rika sayo min man shafawa, sabulu da turmin atamfa duk wata.

TAMABAY: Madalla, mun gode.

LADI: Ni ma na gode.

Ina masu karatun da suke cewa suna son su ga hoton Malam Zurke? Ga ni can a saman shafi. To yaya, na yi kyau?

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin