Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 42   Agusta 2003
Malam Zurke
MALAM ZURKE


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
FADI SONKA
Wasiku
NEMAN MAFITA
DUNIYAR FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
FADI SONKAr sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da tunanin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: Wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, ta da jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Su wa suke son su kashe Zulai Dahat?

A CIKIN fim din Hausa ne akan nuno 'yan daba irin su Kumurci suna tare da 'yanmata suna yi musu tsiwa, wata sa'a ma har su buge su. To, ashe mutan gari (ko in ce 'yan dabar gari, na gasken kenan fa) su ma sukan kwaikwayi abin da suke gani a wasan kwaikwayo. Dalili shi ne, irin abubuwan da ke wakanan cikin finafinai ma sukan wakana a fili. Shin 'yan fim ne ke kwaikwayon al'umma ko kuwa al'umma ce ke kwaikwayon 'yan fim? ya kamata malaman Mass Comm. su sa wani dalibi ya yi bincike kan wannan al'amari; idan ya yi aiki mai kyau, su ba shi digirinsa - ko da kuwa bai iya rike kyamara ba!

To, bari ku ji dalilin yi muku wannan matashiyar. Ya zuwa lokacin da nake rubuta wannan filin, ana nan ta dibga wa jarumar shirin Illah da kuma Salsala allurai a sibitin Jinya da ke Kaduna, sakamakon wani bugun kawo wuka da wasu zauna-gari-banza suka yi mata ba gaira ba dalili. Yadda abin ya faru shi ne, a cikin satin farko na watan jiya ne jarumar, wato Zulai Dalhat, ta dawo daga wata tafiya da ta yi zuwa Kano. Saukarta ke da wuya, ko hutawa ba ta yi ba, tana tare da wata aminiyarta mai suna Zainab, sai ta nemi izini a wajen mahifiyarta cewa tana so ta je shagon buga wayar G.S.M. na kudi don ta yi waya. Ina jin kila Shu'aibu Lilisco ta je buga wa wayar. Wayyo, ashe tsautsayi ke kiranta!

Zulai da Zainab suna cikin tafiya a kan titi, ana irin rausayar nan ta isassun mata, kamar daga sama, sai suka ga mashin ya sha gabansu kamar zai buge su, da wasu ribda-ribdan katti makasa kare guda biyu a kai. Ganin haka sai budurwa ta Lilisco ta dube su, ta ga ba ta san su ba. Sai ta ce, "Haba malam, me muka yi maka za ka buge mu?" Wanda yake tuka mashin din ya ce, "To ku yi hakuri don Allah".

Shi kuma na bayan wato wanda aka goyo, ashe ba "malam" ba ne, duk da yake yana da babban suna - Hassan. Ashe da jikakka tsakaninsu; kawai sai ya ce, "Yo hakurin me za ka ba su?" Ya harare ta ya ce, " Ke, zan ci ubanki, na ga kina wani ji ji da kai!"

Ganin haka sai Zulai ta tsorata, ta ja kawarta suka yi gaba. Af! Ashe ba a rabu da Bukar ba, an haifi Habu. Domin kuwa shi Hassan, sai ya karbi mashin din ya ce wa abokin nasa yana zuwa.

A lokacin, 'yanmatan sun shiga shagon da za su buga wayar. Kwatsam, sai ga Hassan ya diro daga mashin din nan da wasu girba- girban katti guda uku daban, duk da shi hudu kenan, kowa na huci kamar wadanda za su yi artabu da Kazaza.

Zulai da kawarta suna fitowa daga shagon buga waya sai makasa karen nan suka zagaye ta. Ba tare da bata lokacin ba, sai suka ce wa Zulai, "Ke Zulai duk da kasancewar ke Bahausa ce kuma Musulma, yau za mu ci kaza-kazanki". A'a. Abu kamar a fim, kafin yarinyar ta buda baki har sun fara dauke mata wuta. Ji kake tititif, tititif, kamar ana surfen geron kunun gandu. Suka yi mata talla talla suka suka kwamtsa ta a kan wani dutse. Nan take ta some, suka gudu suka bar ta a kwance. Ita kuma Zainab, da ma da ta ga kada a yi haihuwar guzuma - da kwance uwa kwance - makalewa ta yi a wani sako don abin ya fi karfinta. To bayan kattin nan sun bace da gani, sai ta fito ta kama Zulai tare da taimakon wasu mutane, ba su zame ko'ina ba sai ofishin 'yansanda. Zulai dai ba ta farka ba sai a nan cikin siteshon din.

To, bayan an maida jawabi, sai Zainab ta ce wa folis ita idan ta ga Hassan za ta gane shi. Aka ba da 'yansanda guda uku suka je neman wadannan 'yan ta'adda. Da aka je wata majalisar matasa ba a same su ba, amma sai wani daga cikinsu ya ce ya gane Hassan. Ya ba su adireshin gidan su Hassan din, wanda yake a 'Daura Road'.

Da zuwa gidan suka rafka sallama sai abokin tagwaicin Hassan din ya fito. Da ya ga 'yansanda tare da 'yanmatan sai ya rude. Ya nemi ba'asi, suka yi masa bayani. Sai ya ce masu ai kuwa Hassan ba ya nan. 'Yan sanda suka juya da nufin komawa ofishinsu. Husainin nan ya dan fara ba Zulai hakuri, amma ko kallon arziki ba ta yi masa ba, suka wuce.

Komawarsu ke da wuya ofishin 'yansanda, ana cikin daukar bayanin Zulai sai ga Husaini ya shigo. Wai ya zo ya ba da hakuri a madadin dan'uwansa. Da ganin haka, sai 'yansandan nan suka ga ai kamar ma ya raina masu wayo ne. Nan take suka kama shi suka kulle, suka ce in ya kawo Hassan za su sake shi.

To a wata majiyar, mun samu labarin cewa dukkan wadanda suka aikata wannan mummunan aiki sun yi tsammanin Zulai ta mutu. Saboda haka, har wasu daga cikinsu sun fara tattara 'yan komatsansu suna arcewa daga garin. Da labari ya isa wajen iyayen Hassan, cewa an kama Husaini, sai suka ce ai hakan ba ta sabuwa, wai bindiga a ruwa. Suka bazama neman Hassan har Allah ya ba su sa'a suka kamo shi suka kai wa 'yansanda, sa'annan aka sako Husaini.

To a binciken da ake yi wa shi Hassan, majiyata ta ce har yanzu ya kasa ba da takamaiman dalilin da ya sa suka nemi kashe Zulai, yana cewa wallahi sharrin shaidan ne kawai. 'Yansanda dai suna nan suna ci gaba da bincike. Na ji an ce sun ce sai ya fadi inda abokan ta'addancinsa suke tukun za a sakar masa mara. Ita kuwa Zulai ta yi ta zarya kullum zuwa asibiti tana karbar. Sai kashe kudi kawai take yi - ba ta ci ba, ba ta sha ba. Allah ya sa kada abin ya kai ta ga sayar da gwala-gwalai, ga shi kuwa aurenta da Lilisco sauran kiris. Allah ya kyauta.

A karshe, ga shawara ga Lilisco: Ka gaggauta kammala shirye-shiryen aurenka da Zulaihatu, wanda kuka ce za a yi a watan gobe, kada ka dinga dagawa, domin kila dai wasu samari da ka kasa wajen neman auren ne suke so su huce haushi, wato ko dai ba su aura ba kai ma sun bar ka da amarya gurguwa ko mai ido daya!

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin