Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 46   Junairu 2004
Malam Zurke
MALAM ZURKE

BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
HIRA DA DARAKTOCI
Wasiku
NEMAN MAFITA
SHARHI KAN FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
ADABI
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN

Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon FIM TA 45. Danna nan ka gani!
Bangon FIM TA 44. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 43. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 42. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 41. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 40. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 39. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM YA FITO!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

KASH! Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

'Yan wasa: Farida Jalal, A.A. Shariff (Momo), Kasimu Yero, Bashir Nayaya, Abubakar Yusuf Ladan, Hajara Usman, Sani Idris Moda, Sani Garba S.K, da Rashida Bello.

Darakta: Aminu A. Shariff

BABU IRINSA!

In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Usaman Kano a Makka:
In ba ka yi ba ni wuri!

ABIN dariya ba ya karewa a fagen shirin fim na Hausa. A kusan kullum sai cikina ya kulle don dariyar wasu abubuwa da kan wakana a wannan sana'a ta kallo-kallo. Abin har ya kai ba a nan Nijeriya kadai ne 'yan fim ke yin abin ban-dariya ba, a'a har ma a kasar waje!

Wani shahararren dan fim ne ya je umrah kwanan nan a Saudi Arebiya. Da ma ya taba zuwa, kuma ko a zuwansa na baya ya yi harkalla da takari, inda suka rabu dutse a hannun riga. To, a wannan karon ba su ya takalo ba. Hasali ma dai bai takali kowa ba. Duk da haka ya ja hankalin jami'an tsaron Saudiyya. Kafin ya ja hankalinsu sai da ya ja na Hausawan da suke zaune a can da wadanda suka je sauke farali. Duk wanda ya gan shi sai ya ce, "La! Ku zo ku ga wane!" Aka fa taru ana kallonsa, shi kuma yana ta yi musu irin calikancinsa da ya saba yi a talbijin. A nan fa askar suka fara sunsunarsa, suna tunanin waye wannan?

To, rannan kuma sai aka je dawafi a masjidil haram, wato farfajiyar Masallacin Annabi. Gogan naka yana tare da masu take masa sawu, sun dafo shi sai ka ce Asshek Malam ... aham! kada dai in ba ku satar amsa ku ce kun gane ko waye. To, ana ta dawafin ma, duk wanda ya kyalla ido ya gan shi sai ya manta abin da yake yi, ya shiga binsa a baya. Kafin a jima, Hausawa da sauran kabilu masu kallon finafinan Hausa sun taru, ana binsa duuu, ana ta mamaki. A nan ma sai askar suka lura (domin fa kun san yanzu Amerika ta ba kowane jami'in tsaron karin idanu hudu don ya gano mata "'yan ta'adda. Babu ma kamar Saudiyya, garin su Osama bin Laden!). Don haka sai suka fara tunanin ya kamata su binciki wannan bakin mutum din (duk da yake ba Balarabe ba ne ai akwai Bakin Balarabe). Nan take suka kira shi zuwa gefe guda, 'yan tawagarsa suka bi su kallo. Suka ce, "Malam, kai kuwa wanene?"

A nan dai wurin amsa tambayoyin sai askar din suka fahimci cewa ai dan dirama ne daga Nijeriya. Ambasadan 'yan fim kenan! Don haka sai suka ce, "To mun ji, je ka." Amma fa suka ci gaba da sa ido a kansa.

Na ji an ce ko bayan da ya koma masauki ya samu labarin cewa an ci gaba da bincike a kansa ta bayan fage. Don haka dai sai ya ce bari mutum ya nemi hanyar gida, kada kawai kawai jami'an tsaro su kama shi su mika shi ga Amerikawa masu muklkin duniyar a yau. Don haka, majiyata ta shaida mani cewa bai ma bari ya kare ibadar yadda ya so yi ba, sai ya hawo jirgi ya tsero.

Kada ku ga wautarsa, domin da a ce an aika da kai gidan jarun a Guantanamo Bay a kasar Kyuba, ai gwamma mutum ya dawo kauyensu ya shari taushe abinsa. Ai kamar yadda marigayi Malam Kalarawi (Allah ya jikansa) ya ce ne, da a ce an kai mutum gidan yari yana cin kaza tare da shan Fanta a kullum, gwamma ya zauna a gida matarsa tana ba shi kunun kanwa da dumame yana tausawa cikin ciki.

A, to malam ko kai ne fa? Duk wanda bai yarda da cewa Asshek ya yi hikima ba, ina jiran ganin wasikarsa gare ni. Tamat.

Sata a Kaduna: 'Yan wasa sun kawo uzuri

KUN tuna da labarin satar wayar GSM da na ba ku a watan Satumba da ya gabata? Na ji an ce labarin ya bata ran mutane da dama, ciki har da wadanda ba ruwansu da labarin. Akwai ma wani furodusa dan bagu a Kaduna wanda ya ce zai tsaya wa wasu 'yan wasa wai a kai ni kara. Amma na ji shiru, kamar an aiki bawa garin Lere!

Daya dga cikin wadanda labarin bai yi wa dadi ba shi ne dattijo Malam Isa Bello (Ja), wanda na ce muku an lalubi cikin wandonsa a lokacin binciken da aka yi don gano barawon wayar. Malam Isa, wanda yana daga cikin dattawan da nake girmamawa a industiri, ya je ofishin Fim na Kano a fusace, inda ya bayyana wa ma'aikatan mujallar cewa an yi kuskure a labarin, musamman da aka ce an lalube shi. Sata kam an yi sata, kuma an yi bincike, inji shi. To amma me ya sa shi ba a tuntube shi an ji wani abu daga gare shi ba?

Da yake bayyana wa wakilina abin da ya san ya faru, malamin ya ce, "Mun je Kaduna yin fim. A lokacin ni a (unguwar) Kabala na kwana gidan su Skito. Da gari ya waye ban sami damar yin wanka ba muka wuce Unguwar Rimi inda za a yi fim din."

Ya ce da zuwansa bai shiga falo ba ya wuce kai tsaye cikin gidan, ya sa aka samo masa ruwa don yin wanka. Kafin ya fito, har an yi satar. "Ana ta dube-dube, ni ne ma garin dube-duben na gano 'sim card' din (wato kati mai dauke da layin wayar) da aka boye a karkashin kujera, na kuma ba da shawarar a bincike wanda ya zauna a wajen har aka samo barawon. Ba ma dan wasa ba ne, kawai ya zo ne don ya bayar da haske a shirin (lighting)."Har rantsuwa Malam Isa ya yi kan cewa ba a caje shi ba, ya ce hasali ma shi ne ya bukaci a duba motarsa ko wani ya sata ya jefa masa.

To, masu karatu kun ji uzurin Malam Isa a kan wannan labarin. Na karbi gyaransa, ga shi nan na buga don a fahimci cewa ba a lalubi dattijon ba. Amma a gaskiya wanda ya ba Malam Zurke labarin ne ya yi kuskuren a nan, domin shi ne ya tabbatar da hakan. Kuma tilas in yarda, domin shi ganau ne ba jiyau ba.

Da yake labarin ya tada jijiyar wuya, shi ma tauraron labarin, wato A.S. Mohammed, ya kawo wasu gyare-gyare a labarin. A cewarsa, kuskure uku ya gani a labarin. Ga su:

Ba a cikin daki suka binciki 'yanmatan nan ba; a wani kwararo ne da ya nufi cikin gida daga falon (wato corridor);

2. Sai da ya bukaci Hajiyar gidan ta binciki 'yanmatan, amma ta ki, don haka suka yi aikin da kansu;

3. Ba shi da Skito ba ne suka bukaci 'yanmatan su tube a bincike su, a'a 'yanmatan ne da kansu, musamman ta farkonsu, ta tube ba tare da an ce mata ta yi hakan ba. Ya ce tana zuwa inda shi da Skito suka tsaya, ta zo a fusace tna fadin, "Ba dai sata ake cewa an yi ba? To wallahi ko'ina ma a duba, tunda dai na san ban dauka ba!" Sai kurum suka ga ta fara kwabewa. Suna, "Tsaya! Tsaya mana!" Amma ina, har ta yi nisa. Su kuma suka zuba wa sarautar Allah ido.

Wani wakilina ya dan waiwayi yarinyar a ofis din Fim da ke Kaduna a kan hakan, sai ta ce wallahi matsa musu aka yi su tube.

To, Allah dai ya kyauta.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin